PDP: Abubuwan da suka ja hankalin ‘yan Najeriya a taron jam’iyyar adawar

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Babban taron jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ya tashi ba tare da wata matsala ba, ko kuma aƙalla ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, wanda aka shafe baki ɗayan ranar Asabar ana gudanarwa.

Yayin taron da aka zaɓi Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugaba na ƙasa, wakilai daga jiha 36 na Najeriya sun kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen shugabannin jam'iyyar a muƙamai daban-daban, kodayake ba duka muƙaman aka jefa wa ƙuri'a ba.

An ga yadda manyan jiga-jigan jam'iyyar masu adawa da juna suka haɗu wuri guda a dandalin Eagle Square da ke Abuja biyo bayan hukuncin kotu da ya bayar da umarnin gudanar da taron a ƙarar da tsohon shugabanta na ƙasa, Uche Secondus ya shigar.

Mun duba wasu abubuwa da suka ja hankali yayin taron kamar haka.

Tawagar Kwankwaso ta bai wa mutane mamaki

Akasarin jagorori da 'yan kwamatin shirya taron sun shiga filin taron ne daban-daban kafin daga bisani su shiga wata ganawar sirri.

Wani abu da ya ja hankalin mahalarta taron shi ne yadda tawagar tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya Rabi'u Musa Kwankwaso ta mamaye filin taron da sowa da waƙe-waƙe.

Tun daga shigowarsa cikin fili dandazon magoya bayan ƙungiyar Kwankwasiyya, wadda tsohon gwamnan ke jagoranta, suka dinga yi masa waƙar maraba da bushe-bushe da kaɗe-kaɗe.

Wani bidiyo ya nuna yadda suka dinga waƙar "Ƙwankwaso a ba mu a huta". Da alama suna yi masa fatan zama shugaban ƙasa ne, domin kuwa babu sunan Rab'iu Kwankwaso a jerin sunayen 'yan takarar na kowane muƙami.

Kazalika, 'yan Kwankwasiyya sun karaɗe wurin da sowa lokacin da aka kira wakilan Kano su kaɗa ƙuri'a ƙarƙashin jagorancin shugaban nasu Kwankwaso.

Babu tabbas game da adadin magoya bayan da suka bi Kwankwaso zuwa Abuja daga Kano amma dai taro ya yi taro.

An zaɓi ɗan shekara 25 a matsayin shugaban matasa

Wani abu mai kama da na al'ajabi da ya faru a taron shi ne yadda aka zaɓi matashi ɗan shekara 25 a mastayin shugaban matasa na PDP.

Ɗan asalin Jihar Kaduna, Muhammed Kadade Suleiman ne matashi mafi ƙarancin shekaru da aka zaɓa a wannan muƙami a matakin ƙasa.

Muƙamin nasa na shugaban matasa na cikin waɗanda aka kaɗa ƙuri'a a kansu sakamakon kasa sasantawa da aka yi tsakanin 'yan takarar.

Shakka babu matasan Najeriya za su zuba ido don yin koyi da shi yayin da zai jagorance su a PDP zuwa babban zaɓe na 2023.

Babu Goodluck Jonathan babu alamunsa

Rashin ganin tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan a wurin taron ya jawo maganganu, kodayake bai bai wa wasu mamaki ba.

A matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa ƙarƙashin PDP, an sha ganin Jonathan a gaba-gaba cikin lamuran da suka shafi jam'iyyar a baya. Sai dai abubuwa sun fara ja baya a 'yan watannin da suka wuce.

Da ma dai an daɗe ana raɗe-raɗin cewa APC mai mulki na neman ba shi takarar shugaban ƙasa a 2023, kodayake babu tabbas a wannan magana.

Mataimaki na musamman ga Goodluck, Mr Ikechukwu Eze, ya faɗa ranar Juma'a cewa tsohon shugaban zai je taro Kenya wanda ƙungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta shirya.

Sai dai har aka kammala taron ba a ji wanda ya ce Goodluck Jonathan yake wakilta ba balle ma ya karanto wani jawabi a madadinsa.

Da za ku karanta martanin da mutane suka yi ƙarƙashin labarin tafiyar tasa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da kun ga mabambantan ra'ayoyi.

An zaɓi mutum 18 cikin 21 ta hanyar sasantawa

Jumillar mutum 21 ne suka bayyana a matsayin shugabannin jam'iyyar a matakin ƙasa a muƙamai daba-daban.

Sai dai gabanin fara jefa ƙuri'a, Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya shaida wa BBC cewa za a zaɓi kashi 99 cikin 100 na shugabannin ta hanyar sasantawa.

Ya ƙara da cewa muƙamai uku ne kawai ake da jayayya a kai ya zuwa lokacin kaɗa ƙuri'ar. Muƙaman su ne: mataimakin shugaba na Arewa da mataimakin shugaba na Kudu da kuma shugaban matasa.

Waɗanda suka yi nasara a muƙaman su ne: Umar Damagum (Mataimakin Shugaba na Arewa), Taofeek Arapaja (Mataimakin Shugaba na Kudu), Muhammed Suleiman (Shugaban Matasa).

Wakilai daga jihohin Anambra da Abia da Adamawa ne suka fara jefa ƙuri'a.

Taro ya tashi ƙalau duk da hasashen rikici

Duk da rikicin da ya gabaci taron na ranar Asabar, ana iya cewa an yi lafiya an ƙare lafiya, kodayake ƙila ya yi wuri a ce babu wanda zai ƙalubalanci wasu daga cikin matakan da aka ɗauka.

An fara taron ne ƙasa da kwana ɗaya bayan kotu ta ƙi amincewa da buƙtar da tsohon shugaban PDP na ƙasa Uche Secondus ya shigar gabanta na neman a dakatar da shi.

Masu sharhin siyasa a ƙasar sun yi hasashen cewa da wuya a kammala taron ba tare da wani ya yi ƙorafi ba game da mutanen da aka zaɓa ganin cewa mafi yawansu sasantawa aka yi ba zaɓe ba.

Daga cikin buƙatun da ya gabatar wa kotun, Mista Secondus na so kotun ta ayyana shi a matsayin wanda zai jagoranci taron a matsayinsa na halastaccen shugaba.

Sai dai dukkan alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani sun amince da hukuncin ba tare da jayayya ba.

Zan nemi kujerar gwamnan Kaduna a PDP - Shehu Sani

Kawai sai ga Sanata Shehu Sani a filin taron na PDP, kuma da BBC Hausa ta tambaye shi garin yaya aka yi haka sai ya ce "kujerar gwamnan Kaduna muka sa a gaba".

Tsohon sanatan mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya kwana biyu da bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PRP amma ya ƙi fayyace gidan da ya koma.

"Hakan yana nufin na koma PDP a hukumance," in ji shi a hirarsa da wakilin BBC Haruna Tangaza.

Da aka tambaye shi ko yana da niyyar takara a PDP, sai ya bayar da amsa da cewa: "Mutane na kira mu tsaya takara kuma za mu nema a wajen Allah. Takarar gwamman Kaduna zan yi."