Iyorchia Ayu: Tarihin sabon shugaban jam'iyyar PDP

Jam'iyyar PDP ta zaɓi Sanata Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugabanta a a babban taron da ta gudanar a Abuja.

Ana kallon Ayu a matsayin ɗan takarar da taron ya amince da shi a matsayin shugaban PDP. Ya gaji Uche Secondus, wanda aka dakatar a watan Agusta a matsayin shugaban jam'iyyar.

An haifi Iyorchia Ayu ne a garin Gboko na jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya ranar 15 ga watan Nuwambar 1952.

Ya yi karatunsa na digiri a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ko da yake daga bisani ya tafi Jami'ar Jos da ke jihar Filato inda ya koyar da Ilimin Sanin halayyar dan adam wato Sociology.

Ya taɓa zama shugaban kungiyar malaman jami'a, ASUU, reshen Jami'ar Jos.

Mista Ayu ya tsunduma cikin harkokin siyasa inda a shekarar 1992 ya zama Sanata a karkashin jam'iyyar SDP kuma 'yan majalisar dattawan lokacin suka zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa tsakanin 1992-1993.

'Yan Majalisar dattawan sun tsige shi Mista Ayu daga kan kujerarsa a watan Nuwamban 1993 sakamakon adawar da ya yi ta kafa gwamnatin riƙon kwarya ta Cif Shonekan.

Ya riƙe mukamai daban-daban na ministoci. Kuma Mukaman da ya riƙe sun hada da na Ministan Ilimi daga 1993 zuwa 1998 da Ministan Masana'antu tsakanin 1999 zuwa 2001.

Kazalika ya riƙe muƙamin Ministan harkokin cikin gida daga watan Yulin 2003 zuwa watan Yunin 2005.

Sannan ya zama Ministan Muhalli daga watan Yunin 2005 zuwa Disambar 2005.