Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: 'Yan bindiga sun tarwatsa gari 10 a Zamfara, e-Naira na fuskantar barazana
Kamar kowane mako, abubuwa da dama sun faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi. Mun duba muku muhimmai daga cikinsu.
'Yan damfara sun tilasta wa CBN sauke manhajar e-Naira
Shagunan sayar da manhajojin salula sun sauke manhajar kuɗin intanet na e-Naira daga shafukansu kwana uku bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita.
A safiyar Alhamis ne aka lura babu manhajar ta e-Naira a shagunan Play Store (masu Android) da kuma App Store (masu Apple).
Sai dai bankin ya mayar da manhajar kwana ɗaya bayan sauke ta, inda ya ce ya sauke ta ne domin ya ƙara inganta ta.
Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ankarar da 'yan kasar game da ayyukan wasu da y kira "miyagu" da ke yunkurin cutar mutane da sunan e-Naira.
Mutanen a cewar CBN, sun buɗe wasu shafukan intanet da sunan babban bankin inda suke yada cewa yana raba kudin e-Naira har biliyan 50.
A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari tare da Mataimakinsa Yemi Osinbajo suka kaddamar da kudin na e-Naira a Abuja, babban birnin kasar.
CBN ya ce ya samar da kudin ne domin bai wa kowane rukuni na 'yan Najeriya damar gudanar da harkokin kudinsu cikin sauki bayan ya haramta amfani da sauran kudaden intanet na cryptocurrency.
Buhari ya yi Umara, ya rantse da Al-Kur'ani ba zai yi tazarce ba
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi rantsuwa da girman Kur'ani cewa ba zai zarce a mulki karo na uku ba.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar ranar Juma'a.
Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ya yi a Makkah da wasu zaɓaɓɓun 'ƴan Najeriya mazauna garin bayan ya aiwatar da ibadar Umara.
"Na ranste da Al-Kur'ani mai tsarki zan yi aiki da abinn da kundin tsarin mulki ya tanada kuma zan tafi a lokacin da wa'adina ya ƙare," in ji Buhari.
"Ba na so wani ya fara magana ko yin kamfe a kan tsawaita abin da ba ya cikin kundin tsarin mulki. Ba zan lamunci haka ba."
Kazalika, Shugaba Buhari ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin inganta amfani da fasaha wajen gabatar da zaɓukan ƙasar.
"Samar da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a da rijistar masu zaɓe ta intanet addu'o'ina ne da Allah Ya amsa na cutarsa da aka yi sau uku a wasu zaɓuka a baya," a cewar sanarwar.
Yadda ƴan bindiga suka tarwatsa garuruwa 10 a Zamfara
Hare-haren 'yan fashin daji sun tarwatsa al'ummomin wasu garuruwa fiye da goma na yankin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, bayan halaka wasu mutane da sace dabbobi da kuma ƙona shaguna da dai sauransu da 'yan fashin suka yi.
Yanzu haka dai jama'ar garuruwan da abin ya shafa suna can suna zaman gudun hijira a wasu ƙananan hukumomi da ke makwaftaka da karamar hukumar ta Zurmi.
Bayanai sun ce yanzu haka jama'ar garin Ƴan Ɓuki da yankunan karamar hukumar da dama sun shiga halin ƙaƙanikayi tun bayan da 'yan bindigar suka tsaurara hare-haren da suke kai musu a ranar Lahadin da ta gabata.
Wani mazaunin garin ƴan Ɓuki da ya buƙaci mu sakaye sunansa, ya shaida wa BBC cewa garuruwan da lamarin ya shafa sun haɗar da Ƴan Ɓuki, da Ditsi, da Kada Musa, da Gidan zago, da Marmaro, da Dada, da Maduba, da Kwata, da Oho, da Fushin Buku da Gandasau.
''Dukkan wadannan garuruwa ina tabatar muku da cewa yanzu babu kowa a cikinsu, a halin da muke ciki, sun yi gudun hijira, yanzu idan ka je garin Ƙauran Namoda za ka tabbatar da su ne suka taru a can, sannan wasu suna Gusau babban birnin jiha''.
Dalibai biyar na Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano sun rasu a hatsarin mota
Wasu dalibai 'yan asalin jihar kano su biyar sun rasu a wani hadarin mota da ya same su a yankin karamar hukumar Bichi da ke jihar, a ranar Alhamis din nan 28 ga watan Oktoba.
Daliban sun gamu da hadarin ne bayan da tayar motarsu ta fashe suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina domin halartar taron rantsar da shugabannin kungiyar dalibai ta kasar, NAN, shiyya ta daya wato Zone 'A' a Katsina.
Wani tsohon shugaban kungiyar dalibai ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (Kano Polytechnic), Mukhtar Aminu Dabo Maibulo wanda shi ne ya yi wa BBC karin bayani a kan hadarin, ya ce lamarin ya faru ne bayan sun bar garin Bichi da nisan kamar kilomita goma.
Kuma ya ce a lokacin da lamarin ya faru an fara kai su asibitin Bichi ne, daga baya kuma aka debe su zuwa Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano.
Ya ce wadanda suka rasun sun kunshi maza uku, mata biyu, wadanda kuma hudu daga cikinsu daga Kwalejin Ilimi ta jihar Kanon suke, wato Sa'adu Rimi College of Education, daya daga cikinsu ya gama makarantar har ma yana aiki a kwalejin.
Ragowar dayan kuwa dalibi ne na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano, wato FCE, a karin bayanin da ya yi mana.
Kadarorin Diezani da na wasu ƴan siyasa da gwamnatin Najeriya za ta yi gwanjonsu
Gwamnatin Najeriya ta fara shirin tantance darajar ƙadarorin da ta ƙwace ciki har da na wasu 'yan siyasa da suka hada da tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke.
Kadarorin Diezani da ke Banana Island, daya daga cikin unguwanni masu tsada a Legas sun hada da gidaje 24.
Gwamnatin Najeriyar ta dauki matakin ne bayan da kotuna suka kammala tabbatar mata da ƙwace kadarorin.
A watan Mayu shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya gaya wa majalisar wakilai cewa darajar sarkoki da awarwaro da sauran kayan ƙawa da aka ƙwace daga wurin Diezani ta kai naira biliyan 14.
Wasu daga cikin fitattun kadarorin da kotu ta kwace kuma sun hada da na marigayi tsohon hafsan hafsoshin tsaro na Najeriyar, Air Chief Marshal Alex Badeh, da ke unguwannin masu hali na Wuse 2 da Maitama.
Gidajen sun hada da mai lamba 14 Adzope Crescent, daura da Kumasi Crescent, da mai lamba 19 Kumasi Crescent, Wuse 2, da kuma gida mai lamba 6 Umme Street, Wuse 2.
Karin wasu daga cikin kadarorin da aka ƙwace wadanda ake tantance darajar tasu akwai rigunan bikin aure na musamman 125 da wasu kanana rugunan suma na musamman 13.
Fitaccen marubuci kuma ɗan wasan Hausa Kasagi ya rasu
Fitaccen marubuci kuma ɗan wasan kwaikwayo na Hausa, Alhaji Umaru Ɗanjuma wanda aka fi sani da Kasagi, ya rasu.
Ya rasu ne a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya ranar Juma'a.
Marigayin ya yi fice a fannin rubutun Hausa da wasan kwaikwaiyo, kusan a iya cewa su ne na farko-farko a ƴan wasan Hausa.
Haka kuma, shi ya rubuta sanannen littafin Hausa na Kulɓa Na Ɓarna.
An haife shi ya birnin Katsina a shekarar 1950.
Ya yi karatu a Najeriya da Ingila, inda ya ware a fannin fina-finai.
Ya bar mata biyu da 'ya'ya 13.