Dalibai biyar na Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano sun rasu a hatsarin mota

Wasu dalibai 'yan asalin jihar kano su biyar sun rasu a wani hadarin mota da ya same su a yankin karamar hukumar Bichi da ke jihar, a ranar Alhamis din nan 28 ga watan Oktoba.

Daliban sun gamu da hadarin ne bayan da tayar motarsu ta fashe suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina domin halartar taron rantsar da shugabannin kungiyar dalibai ta kasar, NAN, shiyya ta daya wato Zone 'A' a Katsina.

Wani tsohon shugaban kungiyar dalibai ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (Kano Polytechnic), Mukhtar Aminu Dabo Maibulo wanda shi ne ya yi wa BBC karin bayani a kan hadarin, ya ce lamarin ya faru ne bayan sun bar garin Bichi da nisan kamar kilomita goma.

Kuma ya ce a lokacin da lamarin ya faru an fara kai su asibitin Bichi ne, daga baya kuma aka debe su zuwa Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano.

Ya ce wadanda suka rasun sun kunshi maza uku, mata biyu, wadanda kuma hudu daga cikinsu daga Kwalejin Ilimi ta jihar Kanon suke, wato Sa'adu Rimi College of Education, daya daga cikinsu ya gama makarantar har ma yana aiki a kwalejin.

Ragowar dayan kuwa dalibi ne na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano, wato FCE, a karin bayanin da ya yi mana.

Mukhtar ya yi karin bayani da cewa, bayan wadanda suka rasun akwai kuma wasu daliban kusan mutum bakwai wadanda suka samu raunuku, wadanda ake musu magani a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.

Majiyar tamu ta ce tuni 'yan uwan wadanda suka rasun suka karbi gawarwakinsu aka je aka yi musu jana'iza.

Hatsarin mota ya zama tamkar ruwan dare a Najeriya, inda yake laƙume rayukan mutane a duk rana.

Sunayen ɗaliban

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan da kuma jajanta wa waɗanda suka jikkata.

A sanarwar da gwamnan ya fitar a ranar Alhamis, ya ce: "Mun kaɗu da jin labarin wannan rasuwar ƴaƴanmu, ɗalibai biyar da suka rasu a hatsarin mota kan hanyarsu ta zuwa Katsina. Labarin akwai ɗaga hankali.Sanarwar ta lissafa sunayen ɗaliban kamar haka: Abubakar Sulaiman da Tahir A. Dalhatu da Maryam Abdullahi da A'isha Wada Abdulsalam da kuma Usman Abubakar Abubakar.