Hotunan halin da ake ciki bayan Rasha ta kai hari Ukraine

Bayan da sojojin Rasha suka tsallaka kan iyaka zuwa cikin Ukraine, mazauna manya da kananan biranen kasar sun rika neman mafaka a wasu wurare, inda wasunsu kuma ke barin biranen zuwa yankunan karkara.

Ga wasu hotunan abubuwan da ke faruwa yayin da 'yan kasar Ukraine suka farka da labarin kutsawar da Rasha ta yi cikin kasar.

Black smoke rises from a military airport in Chuguyev near Kharkiv on February 24, 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bakin hayaki ya tashi daga filin jiragen saman sojoji da ke Chuhuiv, kusa da Kharkiv.
Russian troops have also been crossing the border in Kharkiv, about 25 miles from the Russian border, Ukrainian officials say.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Rasha

Jami'an gwamnatin Ukraine na cewa dakarun kasar Rasha sun fara kutsawa cikin kasarsu ne a Kharkiv, wani gari mai nisan kilomita 36 daga kan iyakar kasashen biyu.

Cars queue to exit Kyiv in the early morning of Thursday

Asalin hoton, Reuters

Wannan hoton na nuna cunkoson motoci a Kyiv, babban birnin kasar Ukraine yayin da mazauna birnin ke ficewa bayan da aka kunna jiniyar da ke cewa Rasha ta kai wa kasar hari.

1px transparent line
Hotunan da aka dauka da kyamar tsaro, wadanda Dakarun Tsaron Iyaka na Ukraine suka fitar, sun nuna motocin sojojin Rashasuna tsallaka iyaka daga Crimea zuwa Ukraine.

Asalin hoton, State Border Guard Service of Ukraine / PA Media

Bayanan hoto, Hotunan da aka dauka da kyamar tsaro, wadanda Dakarun Tsaron Iyaka na Ukraine suka fitar, sun nuna motocin sojojin Rashasuna tsallaka iyaka daga Crimea zuwa Ukraine.

Faɗa mana labarinku: Idan ku 'yan Najeriya ne da ke zaune a Ukraine, a wane hali kuke ciki yanzu?

Ukrainian firefighters try to extinguish a fire after an airstrike hit an apartment complex in Chuhuiv, Kharkiv Oblast, Ukraine on 24 February 2022

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aikatan kashe gobara na kasar Ukraine suna kokarin kashe wuta bayan harin da aka kai ta sama ya doki wani gini da ke Chuhuiv.
Crowds at a metro station in Kyiv as air raid sirens ring out across the city. Many people are carrying bags and suitcases

Asalin hoton, Getty Images

Kimanin sa'a biyu da ta gabata ne Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya sanar da cewa sojojin kasarsa za su dauki abin da ya kira "matakan soji" kan Ukraine. Mazauna Kyiv, babban birnin kasar sun rika tururuwa zuwa tashoshin jiragen kasa na karkashin kasa domin neman mafaka. Wasunsu kuma sun shiga motoci inda suke barin birnin.

A father reassures his son as his family takes refuge in a metro station

Asalin hoton, Getty Images

Mahaifin wani yaro yana kwantar wa dansa hankali yayin da matarsa da daya dan nasa ke jira, a yayin da suka isa tashar jirgin kasa ta karkashin kasa domin neman mafaka.

Ukrainian police inspect the remains of a missile that landed in the street in Kyiv

Asalin hoton, Reuters

Wasu 'yan sandan Ukraine yayin da suke duba barnar da wani rokan da aka fada kusa da wani gida a birnin Kyiv.

People seen embracing on the streets

Asalin hoton, Getty Images

An ga mazauna birnin Kyiv na sumbatar juna, yayin da wasunsu ke yin ban kwana da juna. Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce babu kanshin gaskiya cewa dakarunsa za su kai hare-hare a wuraren da fararen hula ke zama.

Families head into the metro station on Thursday morning

Asalin hoton, Getty Images

Wasu mazauna birnin Kyiv yayin da suka isa cikin tashar jirgin kasa ta karkashin kasa da sanyin safiyar Alhamis domin neman mafaka daga hare-haren da suke fargabar Rasha za ta kai cikin birnin.

Wasu labarai masu alaka da abin da yake faruwa a Ukraine: