Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan halin da ake ciki bayan Rasha ta kai hari Ukraine
Bayan da sojojin Rasha suka tsallaka kan iyaka zuwa cikin Ukraine, mazauna manya da kananan biranen kasar sun rika neman mafaka a wasu wurare, inda wasunsu kuma ke barin biranen zuwa yankunan karkara.
Ga wasu hotunan abubuwan da ke faruwa yayin da 'yan kasar Ukraine suka farka da labarin kutsawar da Rasha ta yi cikin kasar.
Jami'an gwamnatin Ukraine na cewa dakarun kasar Rasha sun fara kutsawa cikin kasarsu ne a Kharkiv, wani gari mai nisan kilomita 36 daga kan iyakar kasashen biyu.
Wannan hoton na nuna cunkoson motoci a Kyiv, babban birnin kasar Ukraine yayin da mazauna birnin ke ficewa bayan da aka kunna jiniyar da ke cewa Rasha ta kai wa kasar hari.
Faɗa mana labarinku: Idan ku 'yan Najeriya ne da ke zaune a Ukraine, a wane hali kuke ciki yanzu?
Kimanin sa'a biyu da ta gabata ne Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya sanar da cewa sojojin kasarsa za su dauki abin da ya kira "matakan soji" kan Ukraine. Mazauna Kyiv, babban birnin kasar sun rika tururuwa zuwa tashoshin jiragen kasa na karkashin kasa domin neman mafaka. Wasunsu kuma sun shiga motoci inda suke barin birnin.
Mahaifin wani yaro yana kwantar wa dansa hankali yayin da matarsa da daya dan nasa ke jira, a yayin da suka isa tashar jirgin kasa ta karkashin kasa domin neman mafaka.
Wasu 'yan sandan Ukraine yayin da suke duba barnar da wani rokan da aka fada kusa da wani gida a birnin Kyiv.
An ga mazauna birnin Kyiv na sumbatar juna, yayin da wasunsu ke yin ban kwana da juna. Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce babu kanshin gaskiya cewa dakarunsa za su kai hare-hare a wuraren da fararen hula ke zama.
Wasu mazauna birnin Kyiv yayin da suka isa cikin tashar jirgin kasa ta karkashin kasa da sanyin safiyar Alhamis domin neman mafaka daga hare-haren da suke fargabar Rasha za ta kai cikin birnin.