Rasha ta kaddamar da yaƙi a kan Ukraine

Russian President Vladimir Putin. File photo

Asalin hoton, TASS via Getty Images

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da soma yaƙi da farmakin sojojinsa na musamman a yankin Donbas da ke gabashin Ukraine.

A wani jawabi da ya gabatar kai-tsaye ta kafar talabijin, ya umarci sojojin Ukraine da ke fuskantar 'yan tawayen da Rasha ke goyon baya su mika wuya, su koma gidajensu.

Mista Putin ya ce Rasha ba ta da niyyar mamaye Ukraine, amma ya yi gargadi cewa Moscow za ta mayar da martani mai karfi kan kowanne mutum da ya kalubalanci Rasha.

Gwamnatin Ukraine ta ce "Putin ya kaddamar da cikakken harin mamaye Ukraine".

Bakin hayaki a kusa da shalkwatar tsaron Ukraine a birnin Kyiv

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bakin hayaki a kusa da shalkwatar tsaron Ukraine a birnin Kyiv

A wani sakon da ya wallafa a Tuwita, Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya bayyana cewa: "An kaddamar da hare-hare kan biranen Ukraine da ke zaune lafiya. Wannan yaki ne na son rai. Ukraine za ta kare kanta kuma za ta yi nasara. Dole duniya ta tsayar da Putin. Kuma yanzu ne lokacin yin hakan."

Ukraine da sauran kasashen Yammacin Duniya sun jima da sanar da cewa Rasha na shirin afka wa Ukraine domin mamaya.

Faɗa mana labarinku: Idan ku 'yan Najeriya ne da ke zaune a Ukraine, a wane hali kuke ciki yanzu?

Rahotanni sun nuna cewa ana jiyo karar fashe-fashe a biranen Ukraine da dama da harbe-harbe a kusa da filin jirgin sama na Kyiv.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kasarsa da kawayenta za su mayar da maratani mai zafi kan harin da dakarun Rasha suka kaddamar kan Ukraine.

"Shugaba Putin ya zaɓi hanya mafi muni na kazamin yaƙi da zai salwantar da rayuka da akuba ga rayuwar mutane", a cewar Mista Biden. " Duniya za ta riƙe Rasha kan duk wani alhaki."

A jawabinsa na karshe a kokarin ganin ya kauracewa kai wa a matsayin yaƙi tun kafin sanarwar Mista Putin, shugaban Ukraine Volodymrd Zelensky ya ce Rasha na iya "soma gagarumin yaƙi a Turai" inda ya roƙi 'yan Rasha su nuna adawarsu da faruwar hakan.

Mista Zelensky ya ce Rasha ta aike sojoji kusan 200,000 da dubban motocin yaƙi iyakokin Ukraine.

Rasha ta kaddamar da wannan hari ne kwanaki bayan amincewa da 'yanci gashin kai ga wasu yankunan Ukraine biyu na Donetsk da Luhansk da ke gabashin Ukraine.

Yankunan biyu da suka jima suna fafutikar neman ɓallewa - da ke kuma ke iko da galibin yankin Donbas - sun nemi taimakon sojoji daga baya daga Rashar.

A lokacin sanarwarsa, Mista Putin ya ce sun zabi kaddamar da harin soji ne domin kare wadanan mutanen da aka dane kusan shekara takawas "gwamnatin Kyiv na musu kisan kare dangi".

Mista Putin ya kuma ce Moscow a shirye take ta karya lagon sojojin Ukraine.

An shafe watanni ana fargabar hare-haren Rasha.

Mista Putin ya sha shi ma zargin Amurka da kawayenta da birin da bukatun kasarsa na hana Ukraine zama mamba a kungiyar tsaro ta Nato da ba shi tabbashin tsaron su.

A ranar Laraba, 'yan majalisar Ukraine suka amince a ayyana dokar ta tabbaci a kasar a duk fadin kasar.