Shugaban Apple Tim Cook na shan suka kan albashin dala miliyan 99

Asalin hoton, Getty Images
An bukaci masu hannun jari a kamfanin da su kada kuri'ar kin amincewa da albashin dala miliyan 99 (£73m) da aka yanka wa shugaban kamfanin na Apple TIm Cook a shekarar da ta wuce.
Hukumar da ke kula da harkokin hannun jari (ISS) ta ce tana da damuwa sosai a kan yawan albashin da aka sanya wa shugaban wanda aka kara daga dala miliyan 14.8 a shekarar bara ta 2021.
Ana biyan Mista Cook, ne wanda arzikinsa jumulla ya kai sama da fam biliyan daya, wannan kudi ta hanyar hannun jari da albashi da kuma daukar dawainiyarsa ta wasu hanyoyin.
BBC ta tuntubi kamfanin na Apple domin jin martaninsa.
A wata wasika da hukumar ta ISS ta aika wa masu hannun jari, ta ce akwai damuwa sosai a kan tsari da kuma girman albashin, inda kusan rabin albashin ba shi da alaka da kwazon ko aikin shugaban.
Mista Cook, mai shekara 61, wanda yake yawan magana a fili a kan damuwarsa kan 'yancin dan-Adam, a 2015 ya ce zai bayar da dukiyarsa gaba daya kafin ya mutu.
Hukumar kula da harkokin hannun jarin ta ce albashin Mista Cook, ya ninka albashin yawancin ma'aikatan kamfanin na Apple sau 1,447.
Albashin ya hada da dala $630,600 ta masu tsaron lafiyarsa da dala $712,500 ta amfani da jirgin sama na musamman. Hukumar ta ISS ta ce wadannan kudade sun zarta na wasu kamfanoni sosai, a shekarar da ta gabata.
A shekarar da ta wuce bayanan hukumar kula da hannun jari ta Amurka ta nuna cewa Mista Cook ya bayar da tallafin kusan fam miliyan 7.4 na hannun jarin kamfanin na Apple, mallakinsa ga wata kungiyar agaji, wadda ba a bayyana sunanta ba.
Kamfanin Apple, wanda ke yin iPhone da iPad da MacBook ya kasance na farko da darajar hannun jarinsa ta kai dala tiriliyan 3 a watan Janairu kafin darajar ta yo kasa zuwa yadda take a yanzu dala tiriliyan 2.8.
Kamfanin yana sa ran gudanar da taron shekara-shekarar na masu hannun jarinsa a makon farko na watan Maris. Sai dai kuma kuri'ar masu hannun jari shawara ce kawai, hukumar gudanarwar kamfanince ke da ta cewa a kan albashi.
Korafi na ƙaruwa
Kamfanoni a Amurka da Birtaniya na fuskantar tsananin korafi da adawa a kan yawan albashi da alawus na shugabanninsu.
Kamfanin General Electric da IBM da kuma Starbucks sun kasa samun kuri'a mai rinjaye ta masu hannun jarinsu wajen bayar da goyon bayan yawan albashin da ake ba wa shugabanninsu a 2021.
Kamfanonin mai na Amurka ExxonMobil da Chevron sun gamu da boren masu hannun jari daga masu rajin kare muhalli a shekarar da ta wuce.
Na biyu a yawan hannun jarin kamfanin Exxon, wato Blackrock, sun ninka kuri'arsu biyu ta nuna kin amincewa da yawan albashin da ake son biyan manyan shugabanninsu a nahiyar Amurka ta kudu da Amurka ta Arewa a farkon 2021, idan aka kwatanta da 2020.
A Birtaniya sama da ninki biyu na kamfanonin da ke kasuwar hannun jarin kasar 100, FTSE, sun fuskanci bore ba kamar a shekara ta 2020 ba, kan yawan albashin manyan shugabanni, a lokacin da yawancin ma'aikata ke fuskantar karin matsalar kudi a lokacin annobar korona.
Shugaba Joe Biden tare da 'yan majalisar dokokin kasar na jam'iyyar Democrat sun bukaci da a kara yawan harajin da ake karba a hannun manyan attajirai da manyan kamfanoni domin gwamnati ta samu kkarin kudin daukar dawainiyar jama'a.











