Tedros Adhanom Ghebreyesus: Gwamnatin Habasha ta bukaci WHO ta binciki shugabanta

Gwamnatin Habasha ta bukaci Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bincike daraktanta kuma dan kasar ta Habasha, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, a kan abin da ta kira ''bayanan da ka iya cutarwa, da sam ba su dace ba'' kan rikicin da kasar ke ciki.
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce ''yana yin katsalandan kan harkokin cikin gida na kasar Habasha, ciki har da tsoma baki kan alakar kasar da Eritrea.''
Gwamnatin ta kuma kara da gargadin Dakta Tedros ka iya yin barazana ga amincin WHO.
A makon nan ne, Dakta Tedros ya bayyana halin da ake ciki a yankin Tigray da yaki ya daidaita, da ba shi da maraba da wuta, tare da zargin gwamnatida kin bari akai magunguna yankin.
A bangare guda kuma gwamnatin ta zargi 'yan tawayen Tigray da suke fada da juna, da toshe hanyar da kayan agaji zai shiga yankin.
Dukkan bangarorin biyu dai sun zargi juna da ko dai kai munanan hare-hare da suka shafi farar hula, ko yin makarkashiya wajen kai agaji da dubban farar hula da ke tsananin bukatar taimako.
A baya-bayan nan gwamnati ta zargi Dakta Tedros da goyon bayan 'yan tawayen Tigray a lokacin yakin basasar da ya barke shekara guda da ta wuce a kasar ta Habasha, amma ya musanta zargin.
Dakta Tedros dai ya fito ne daga yankin Na Tigray, kuma ya taba rike mukamin ministan lafiya da gwamnatin da ta wuce, wadda jam'iyyar TPLF ta jagoranta.
A shekarar da ta gabata ne fada ya barke tsakanin sojojin Habasha da 'yan tawayen Tigray, daga lokacin kawo yanzu dubban mutane ne suka mutu wasu dubban suka rasa muhallansu, yayin da wasu kuma sukai gudun hijira zuwa kasashe makwabta kamar Sudan da sauransu.










