ISWAP: An kashe mutum biyar a harin rokoki a Maiduguri

Zulum

Wasu mayaƙa da ake kyautata zaaton mayaƙayan ISWAP sun tashi bama-bamai a wurare da dama a Maiduguri inda suka kashe aƙalla mutum biyar.

Lamarin na faruwa a yayin shugaban kasar Muhammadu Buhari ya isa birnin domin ziyarar aiki.

Wasu bayanai sun nuna cewa kusan bama-bamai tara aka harba a Bulumkutu da Ngomari da kuma Ayafe da ke kusa da filin jirgin saman birnin.

Rahotanni sun ce harin ya rusa da mutum hudu a Ayafe da ke kusa da filin jirgin sama a Maiduguri. Wani harin da shafi Ajilari kusa da Ngomari ya kashe wata mace ɗaya.

Wani mazaunin birnin, Adamu Aliyu Ngulde, ya shaida wa BBC cewa rokokin da aka harba sun lalata wasu gidaje da ke kusa da filin jirgin sama.

A cewarsa "mutum hudu sun rasu biyu kuma suna samun kulawar likitoci a asibiti" yana mai cewa al'ummar unguwar sun fada halin alhini "a yayin da ake murnar ziyarar da shugaban kasa zai kawo."

Wani mazaunin birnin, Mustafa Bukar, ya shaida mana cewa rokar da aka harba ta ruguza gidansa, inda ta jikkata matarsa da 'yarsa sannan ta "kashe ragunana guda bakwai".

Hukumomi a jihar ta Borno sun tabbatar wa BBC Hausa aukuwar lamarin sai dai ba su yi karin bayani kan ta'adin da bama-baman suka yi ba kawo yanzu.

Masana tsaro sun ce an harba rokokin ne daga tazarar kilomita 10 kuma an yi niyyar kai harin ne filin jirgin sama kafin ziyarar shugaba Buhari.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce an baza jami'an tsaro da jirage masu sintiri domin taimakawa sojojin da ke ƙasa don daƙile duk wata barazana ta kai hari.

A farkon watan nan an taba kai harin rokoki a Maiduguri, ko da yake ba a samu hasarar rayuka ba, amma harin ya lalata gidaje da motoci.