Mayaƙan ISWAP sun harba makamai cikin Maiduguri na Jihar Borno

Harin ISWAP a Maiduguri

Asalin hoton, Goni Gudusu

Bayanan hoto, Ana zargin mayaƙan sun harba makamin ne daga wajen birnin

Wani makamin roka da mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka harba ya lalata gidaje a Maiduguri babban birnin Jihar Borno ranar Asabar.

Makamin ya faɗa Unguwar Gida 1000 da farar safiyar Asabar, inda ya yi kaca-kaca da gida biyu da kuma taɓa wasu.

Ana zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne ko kuma ISWAP suka harba makamin daga wajen birnin.

Wani ɗan jarida a Maiduguri ya shaida wa BBC Hausa cewa babu wanda ya jikkata, yana mai tabbatar da cewa mayaƙan ba su shiga birnin ba.

Harin ISWAP a Maiduguri

Asalin hoton, Goni Gudusu

Kazalika, wani makamin roka ya faɗo a yankin Ngomari da ke daf da filin jirgin sama na Maiduguri.

"Babu wanda ya ji rauni sai wani yaro da aka ce bulo ya faɗo masa amma ba wani ciwo ya ji ba sosai," in ji ɗan jaridar.

Mazauna Maiduguri ba su fara zirga-zirga ba sai bayan ƙarfe 10:00 na safe kasancewar ana gudanar da tsaftar muhalli ta ƙarshen wata.

Wasu hotuna da bidiyo sun nuna yadda makamin ya lalata gidaje da dama.

Maiduguri ya kasance cikin zaman lafiya na tsawon watanni tun bayan harin roka da mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi suka kai a watan Fabarairun 2021, inda suka kashe mutum 10.