Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ethiopia: Majalisar Dinki Duniya ta dakatar da bayar da agajin abinci saboda sata
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya dakatar da raba kayan agaji a garuruwa biyu da ke arewacin kasar Habasha bayan 'yan bindiga sun sace kayan.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce barayin da ke yankin da mayakan Tigray ke iko da shi, sun rutsa ma'aikatan agaji biyu da bindiga a garin Kombolcha.
Sun sace kayan abinci masu tarin yawa, ciki har da wadanda aka tanada domin bai wa kananan yara mai gina jiki.
Arewacin Habasha na fuskantar matsananciyar yunwa, sakamakon ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen Tigray.
Bayan shafe shekara guda ana fadan, Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama mutum miliyan tara ne ke tsananin bukatar abinci a kasar.
Mai magana da MDD da ke tafiyar da shirin samar da abinci na majalisar, ya ce ma'aikatansu na fuskantar matsananciyar barazana musamman lokutan da ake sace kayan abincin.
Ya kara da cewa: "Ba za mu amince da irin wannan cin zarafin ga ma'aikatanmu ba. Sun sabawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji abokan huldarmu, mu na bukatar aiki a wuri mai tsaro da mutuntawa."
Ya kara da zargin dakarun gwamnati da bai wa ma'aikatan shirin samar da abincin umarnin, jibge musu manyan motocin abinci dan bukatar kan su.
Wannan ne ya kai ga daukar matakin dakatar da rabon abincin a Kombolcha da kusa da Dessie, manyan garuruwa biyu da ke arewacin yankin Amhara da ke kan babbar hanyar zuwa birnin Addis Ababa.
A baya-bayan nan gwamnatin Habasha ta yi sanarwar karbe iko da garuruwan da ke hannun 'yan tawaye. Sai dai 'yan tawayen Tigray sun ce sojin gwamnatin sun karbe iko da yankunan da sukai watsi da su ne.
A shekarar da ta gabata ne fada ya barke tsakanin dakarun gwamnati da dakarun 'yantar da yankin Tigray na TPLF, wanda suka mamaye kasar shekara da shekaru, yanzu kuma suke iko da yankin na Tigray.
Fira Minista Abiy Ahmed ya aike sojoji yankin Tigray domin murkushe TPLF, bayan zargin su da kai hari sansanin sojin kasar.
Sai dai 'yan tawayen sun mayar da martani ta hanyar kaddamar da hari kan sojojin, da kuma karbe iko da daukacin yankin da kokarin dannawa yankin Amhara da ke makoftaka da su.
Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna tashin hankalin ya haddasa kisan dubban mutane, wasu sama da miliyan biyu sun rasa muhallansu, ya yin da dubbai ke tsananin bukatar abinci.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida a Amirka, Ned Price ya ce matsnancin halin da ake ciki a arewacin Habasha ya munana, ana kuma bukatar daukar matakin gaggawa.
Ya yi kira ga bangarorin da ke yaki da juna su kawo karshen, su kuma bari agaji ya isa ga masu bukata.
Dakatar da kai agaji zai kara munana lamari
Daga Emmanuel Igunza, BBC News, Nairobi
Halin da ake ciki a wannan shekarar, ya kara nuna irin yadda 'yan Habasha ke cikin bukatar taimako, da su kansu ma'aikatan agajin kan barazanar da suke fuskanta.
Tun bayan fara rikicin shekara guda da ta gabata, an kashe ma'aikatan agaji 8, hakan ya sanya kasar cikin mafi hadarin aiki ga ma'aikatan agaji kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Sai kuma wata matsalar ta daban. Wata da watanni, kungiyoyin agaji ke ta rokon gwamnatin Habasha ta ba su damar taimakon wadanda suka makale a yankunan da ake tashin hankali.
Amma kawo yanzu, wani bangare na masu bukatar tallafin ne kadai suka samu hakan a yankin Amhara, da Afar da Tigray. A kowacce rana ana bukatar akalla manyan motocin dakon kaya 100 makare da kayan abinci yankin, amma kalilan ne suke isa duk kuwa da yawan mabukata.
Kungiyoyin agajin na fuskantar matsalar rashin kudi da man fetur, wanda su ke bukata domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Wannan dakatar da kai agajin, zai kara dagula lamura da sanya mutane cikin matsancin hali.
Tuni daman mutum 400,000 ke fama da yunwa da Fari, idan har dakatarwar ta dauki lokaci, hakan na nufin 'yan Habasha za su shiga matsananciyar yunwa da janyo aikin agajin da aka dade ba a gani ba cikin tarihi.