Tigray: Zarge-zarge da sadaukar da kai a lokacin da rikicin Ethiopia yake bazuwa

    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent, BBC News

Da zarar dare ya yi, za ka ga ma'aikatan sa kai, 'yan siriti na kai wa da komowa a unguwannin da ke birnin Addis Ababa babban birnin Habasha, i da suke tsayar da ababen hawa suna dubawa da duba takardun mota da na shaidar tukin motar.

"Mutane 180 ne ke cikin kwamitin 'yan sintirin da muke da su. Mun yi nasarar kama bata gari da dama tare da mika su ga jami'an tsaro. Mun kuma kama makamai da dama, ciki har da bindiga da ababen," in ji daya daga cikin manyan 'yan sintirin da ke gudanar da aikin.

'Yan sa kan na neman 'yan tawayen Tigray, da masu mara musu baya, karkashin sabuwar dokar ta bacin da gwamnatin Habasha ta sanya a matsayin martani ga tawayen 'yan Tigray.

Masu suka na cewa an kama dubban mutanen da ba su ba, ba su gani ba, sai dai da alama matakin na gwamnati ya samu goyon baya a babban birnin kasar.

"Ku yi sauri, yana kokarin tserewa," in ji wani mutum, jim kadan sai ya fara magana ta wayar salularsa.

Tituna kadan daga wajen, gungun wasu dattijan 'yan sintiri sun taru ana bada horo, su na maci da jiran a bau umarni.

A zahiri hankula a kwance su ke a babban birnin kasar.

Duk da cewa Birtaniya da wasu kasashe, sun yi gargadin matsalar tsaro na kara tabarbarewa, a daidai lokacin da 'yan tawayen Tigray da wasu kungiyoyi na kokarin dannawa, amma ofishin jakadancin Rasha a kasar ya aike da sako na daban a shafukan sada zumunta.

Ta ayyana sanya dokar ta bacin babu wani tasiri da ta yi, hasalima a kullum ta Allah rayuwa na kara tsananta a birnin.

A baya-bayan nan Fira Minstan Habasha, Abiy Ahmed, ya sanar da cewa zai jagoranci sojojin kasar zuwa arewaci domin yakar 'yan tawayen.

Bidiyon da gwamnati ta fitar, ya nuna Abiy sanye da kakin soji, kewaye da sojojin, da ya nuna a yankin Arid ne da ke arewa maso gabashin Addis Ababa.

"A yanzu mun yi nasrar share wurin baki daya," in ji Abiy a cikin bidiyon.

"Karsashin da sojojin mu suke da shi abin sha'awa ne. Za mu ci gaba da hakan har si mun karbo kasarmu daga 'yan tawayen da ke neman durkusar da ita."

Ya kara da cewa, dakarun kasar su na ci gaba da dannawa domin karbe garuruwan da 'yan tawayen Tigray suke iko da su.

Sai dai, tantance wannan ikirari na gwamnati abu ne mai wuyar gaske, a yankin da tashin hankali ya janyo aka katse hanyoyin sadarwa, da sanya dokoki masu tsauri na yada abin da sojoji ke yi a wannan yakin.

Jami'an TPLF - da a baya suka wallafa wasu hotunan da aka dauka ta jirage marasa matuka, sun nuna dubban fursunonin yakin Habasha, da suke ikirarin su na kara dannawa birnin Debre Birhan, da ake yi wa kallon makarfafar gwamnati da ke wajen Addis Ababa.

Amma masu sharhi na gargadin za a iya kasa shawo kan dakarun Tigray, sannan gwamnati ka iya far musu ta kowacce fuska, da hare-hare daga makofciyar kasar wato Eritrea.

Mutane na fadawa mawuyacin hali

Idan aka kauda tunanin bangaren da ya ke yin nara, a bayya ne ta ke karara yakin na kara yaduwa, sannan farar hula na kara shiga mawuyacin hali.

Shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WTF) ya yi kiyasin mutum sama da miliyan 9 ne ke tsananin bukatar abinci.

"Ya yin da yakin ke kara yaduwa har tsallaken arewacin Habasha, mu na kara ganin yadda mutane ke tsananin bukatar taimako musamman na abinci," in ji Claire Neville, jami'ar WFP a Addis.

Ta dora alhakin mummunan halin da ake ciki a kasar kan masu fada da juna, da zargin 'yan tawayen Tigray da kin ba da damar shigar da agaji yankin, da ita kan ta gwamnati da ke kawo cikas da tsaiko kan aikin agajin.

A baya-bayan nan WF, sun yi nasarar shiga da taimakawa dubban mazauna garuruwa biyu da ke Amhara, wanda 'yan tawayen Tigray ne suka taimaka hakan ta samu.

Yaki da masu yi wa kasa zagon-kasa

A Addis, gwamnatin jam'iyyar Prosperity mai mulki, ta ci gaba da shirya bukukuwan godiya ga 'yan kasar da suka sadaukar da rayuwarsu.

"Mu na tsaka da yaki da masu cin amanar kasa, da hadin gwiwar aminansu na kasashen waje," in ji wani kansila mai suna Etisa Deme.

"An kira ni domin na shiga yakin kubutar da kasar mu. Za ka iya kuka idan an kashe dan uwanka, amma ina za ka je idan kasarka ta kubuce ma ka? Dan haka a shirye na ke na sadaukar da rayuwata ga kasarmu. Ba na jin tsoron cewa ba a taba ba mu atisaye ba," a cewar wani matashi mi shekara 20, Babush Sitotaw.

Wata tsohuwa mai kai cike da furfura, Dinkinesh Nigatu, ita ma ta shiga dandazon mutanen.

"Ina kaunar kasata. Ina son zuwa yakin nan, miji na da 'ya'yana sun ce na zauna a gida, na ce inaaa ai sai na shiga yakin karbowa kasarmu 'yanci," in ji ta.

"SDon haka an yi min atisaye kan aikin sintiri na sa kai, mu na yawo a unguwanni ni da mijina da Da na domin gano bata gari. Na shaida musu su fita faggen daga ba sai makiyansmu sun cimmaana a gida ba," haka ta fada a hirar ta da BBC.

Gwamnatin Habasha, ta yi ikirarin da gangan kasashen yammacin duniya ke tunzura 'yan kasar ta hanayr labaran da ke tunzura duniya da yadda suke kallon yakin.

Yawancin 'yan kasar sun fusata, inda suka fantsama shafukan sada zumunta tare da nuna rashin amincewa da katsa landan din, da cewa lokacin mulkin mallaka ya wuce, da cewa 'yan Tigray na kara kambama matsalar.

A duk lokacin da BBC ta so tattaunawa da gwamnatin Habasha zarge-zargen da ake mata, gwamnatin na kin amincewa da hakan.

Sai dai kowa ya san ana sukar gwamnatin kan durkusar da kafafen yada labaran kasar, yadda ba a bada ainahin rahoton halin da ake ciki .

Fira Minsta Abiy Ahmed da ya lahe kyautar Nobel ta zaman lafiya gabannin wannan yamutsi, ya yi nasarar ne sakamakon sakin fursunonin siyasa da 'yan jarida da sasanta rashin jituwar da ke tsakanin Habasha da makofciyarta Eritrea.

Sai dai a baya-bayan nan ana sukar sa kan halin da ake ganin ya jefa kasar a ciki.

A bangare guda kuma, BBC ta nanata za ta ci gaba da zakulo bayanai sahihai, ba tare da nuna bangaranci ko fifiko ga wani bangare ba.