Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yakin Ethiopia ya cika shekara ɗaya: Yadda za a kawo karshen wahalar da 'yan kasar ke ciki
- Marubuci, Daga Catherine Byaruhanga & Yemane Nagish
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News & BBC Tigrinya
Ƴan tawayen Tigray a halin yanzu suna yin nasara a yaƙin da ya ɓarke shekara guda da ta gabata a arewacin Habasha wato Ethiophia.
Firaminista Abiy Ahmed wanda suka raba gari da jam'iyya mai mulki ta Tigray kan manufofinsa na siyasa, ya ayyana dokar ta-ɓaci a faɗin ƙasar - yanzu fargaba da rashin tabbas ne ke mulkin ƙasar.
Yayin da ƴan tawaye ke matsawa kusa da babban birnin ƙasar, gwamnati ta buƙaci mazauna Addis Ababa su haɗa kai su kare unguwanninsu.
Mayaƙa daga Tigray, ƙarƙashin jagorancin Tigray People's Liberation Front (TPLF), sun shiga biranen Dessie da Kombolcha a ƙarshen makon da ya wuce.
Suna yankin Amhara wanda ke maƙwabtaka da Tigray kuma suke da nisan kusan kilomita 400 daga babban birnin.
Ana tunanin yaƙin ƙwato Dessie na ɗaya daga cikin faɗa mafi muni yayin da ake ganin birnin a matsayin mashigar Addis Ababa ta kudanci, da kuma iyakarta da Djibouti a gabashi.
Wani mutum da ya yi aiki a babban asibitin Dessie kafin a ƙwace garin ya ce birnin ya sauya sosai a watannin da suka gabata yayin da yaƙi ke ci gaba a yankin.
Ya ce kar a bayyana sunansa, ya shaida wa BBC cewa an yi wa Dessie laƙabi da "babban birnin so" saboda yadda yake da ƙabilu da al'adu daban-daban kuma cibiyar kasuwanci.
Amma a ƴan watannin da suka gabata, dubban mutane sun yi tururuwa a cikin garin suna tsere wa ƴan tawaye.
"Zuwa da dawowa daga aiki, ƙananan yara za su yi ta riƙe ƙafar wandona suna roƙona kuɗin sayen burodi."
Shi da abokan aikinsa sama da 10 sun daina zuwa asibitin lokacin da suka ga sojojin gwamnati suna barin gari.
Ana kama ƴan Tigray
Ga ƴan Tigray a babban birnin, ƙwace Dessie da ƴan tawayen suka yi ya ruruta wutar rikicin ƙabilanci a birnin.
Wani lauya ɗan Tigray da ke zaune a Addis Ababa ya ce yanzu birnin ba kamar yadda aka san shi ba ne. Ƴan sanda na kama ƴan Tigray a samamen da suke kai wa gidaje da shaguna da kuma lokacin da ake duba motoci a kan tituna, a cewarta.
"Idan kai ɗan Tigray ne ba ka da kataɓus. Kama ka za a yi. za a kama ka saboda ƙabilanci," a cewar wani mazauni.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a Addis Ababa ya ce ana kama mutanen ne idan aka tabbatar suna aikata laifuka. Ya tabbatar da cewa mafi yawan waɗanda aka kama ƴan Tigray ne amma ya ce ana kama wasu ƙabilun ma.
Ƴan tawayen sun ce suna ƙoƙarin shiga garin ne don tursasa wa gwamnati ta kawo ƙarshen shingayen da ta sa a yankin arewacin Tigray, inda ake bukatar agaji kuma aka yanke wutar lantarki da ayyukan banki.
Tun a watan Mayu, Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta yi gargaɗin cewa mutum 400,000 na daf da fuskantar yunwa.
Bayan da TPLF ta kori rundunar soji daga Mekelle, babban birnin Tigray a watan Yuni, ƙungiyoyin agaji sun ce an kafa shingayen tare hanya a titunan da ke shiga yankin yayin da ƙarancin man fetur da kuɗi suka sa kai agaji ga mutane sama da miliyan biyar ya ƙara wahala.
Iyaye sun kaɗu
Matsalolin buƙatar agaji a Tigray sun yi tsanani - kamar yadda ake gani a bidiyo daga asibitin Ayder Referral Hospital na Mekelle inda kukan Eden Gebretsadiq - wata ƴar shekara ɗaya da aka sa wa robar cin abinci - ke keta farfajiyar asibitin.
"Da farko, ba mu san ƙarancin abinci ke haifar da shi ba. Yanzu sun shaida min cewa tana fama da tamowa," a cewar mahaifiyarta da ta ɗimauta.
"Maigidana yana da aikin yi a baya - yayin da ni nake kula da yara a gida. Muna kula da iyalinmu lafiya lau. Suna samun abinci mai inganci sosai kuma suna sa tufafi mai kyau."
A wani gado da Mabrhit Giday ke kwance, gaɓoɓinta sun yi matuƙar ramewa yayin da mahaifinta Gidey Meresa ya ɗan kishingiɗe ta don ta ci ayaba.
Ya ce sun yi tafiyar sama da kilomita 100 kafin su iso asibiti daga ƙauyensu na Kola Tembien, wanda ya fuskanci tsananin yaƙi lokacin da dakarun gwamnati suke Tigray.
Mazauna da dama sun tsere zuwa cikin tsaunuka. Lokacin da suka koma bayan da sojoji da ƙawayensu suka fice, sun iske an ƙona masu gidajensu kuma an sace masu dabbobi.
"Duka wannan ya faru kuma mun yi haƙuri. Sai 'yata ta fara rashin lafiya, a baya kuma lafiyarta ƙalau," a cewarsa. Likitoci sun shaida masa cewa ƴarsa mai shekara 11 na da ciwon zuciya, babu mamaki saboda rashin isasshen abinci.
An rufe layukan waya da na intanet kuma wannan na nufin ba a iya buga waya kuma ba a iya magana da mutane a yankin. An hana BBC da sauran gidajen yaɗa labarai shiga yankin.
Barazana
A wata ziyara zuwa Habasha kwanan nan, shugaban ƙungiyar agaji ta Red Cross Peter Maurer bai iya shiga yankunan da ake rikici ba.
Amurka da MDD da Kungiyar Kasashen Afrika na ta kira a tattauna.
Barazanar kakaba takunkumi da kuma sanarwar da Amurka ta yi na cewa za ta cire Habasha daga wata yarjejeniyar kasuwanci mai muhimmanci sun gaza kawo sauyi a rikicin.
William Davison, babban mai sharhi a ƙungiyar International Crisis Group, na ganin zai yi kyau gwamnati ta sassauta don a iya dawo da ayyukan agaji Tigray.