Gobara ta kashe mutum 38 a gidan yari a Burundi

Asalin hoton, SOS MEDIAS BURUNDI via REUTERS
A ƙalla mutum 36 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata sakamaon wata gobara da ta tashi a gidan yarin Burundi.
Mataimakin shugaban ƙasa Prosper Bazombanza ya shaida wa manema labarai cewa gobarar ta tashi ne a wani gidan yari mai cunkoso a babban birnin ƙasar Gitega, inda a ƙalla mutum 69 suka jikkata.
Hotunan da suka yaɗu a intanet sun nuna yadda ginin gidan ke ci da wuta sannan da tarin gawarwaki, waɗanda aka ce na fursunoni ne.
"Wannan babban bala'i ne," kamar yadda wani fursuna ya shaida wa BBC ta waya.
"Zan iya cewa kusan kashi 90 cikin 100 na ɗakunan kwana sun ƙone ƙurmus."
Wani ɗan jarida a wajen gidan yarin ya shaida wa BBC cewa ma'aikatan jinya daga asibitin Gitega sun shiga gidan yarin don taimaka wa waɗanda lamarin ya rutsa da su, yana mai cewa suna kwashe mamatan da waɗanda suka jikkata.
Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 4 na yammaci agogon ƙasar, wato ƙarfe 2 agogon GMT.
"Mun fara ihu ganin cewa za mu ƙone muna ji muna gani yayin da muka ga wutar na ci ganga-ganga, amma sai ƴan sanda suka ƙi buɗe mana ƙofofin sashen namu, yana mai cewa 'wannan ne umarnin da muka samu'," kamar yadda wani fursuna ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta waya.
"Ban san ta yadda aka yi na tsira ba, amma akwai fursunonin da suka ƙone ƙurmus," ya ƙara da cewa.
Shaidu sun shaida wa AFP cewa a yanzu an shawo kan wutar.
Gidan yarin Gitega na ɗaukar fursunoni 400 ne kawai amma akwai mutum 1,539 a cikinsa a watan da ya gabata, a cewar Ƙungiyar Kiristoci mai adawa da Azabtarwa a Burundi wato (ACAT-Burundi).
Wani saƙon tuwita da ministan harkokin cikin gida na Burundi ya wallafa ya ce matsalar wutar lantarki ne ya jawo tashin gobarar.
A watan Agusta ma an yi wata gobarar a gidan yarin, inda mahukunta suka ɗora alhakin a kan wutar lantarki. Sai dai a wancan lokacin gobarar ba ta jawo asarar rayuka ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X












