Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Boko Haram na riƙe da ikon wasu yankunan jihar Niger'
Gwamnatin jihar Neja da ke arewacin Najeriya ta ce tana fargabar cewa mayakan Boko Haram na riƙe da ikon aƙalla yankuna biyar a kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar.
Ta kuma ce yanzu haka masu tayar da kayar bayan na nan na cin karensu ba babbaka a yankunan, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankunan da dama tsarewa zuwa wasu sassan jihar da maƙwabta.
Sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Matane wanda ya tabbatarwa da BBC da lamarin ya ce yankunan da mayaƙan ke iko sun haɗa da Kurebe da Farina Kuka da Gussau a yankin ƙaramar hukumar Shiroro da kuma Madaka, da Hanawanka a karamar hukumar Rafi na jihar.
Ya ce suna ganin ƴan bindigar da ke yankunan sun fi ƙarfin ƴan fashi daji da ke satar mutane. - "muna da tabbacin cewa ƴan ta'addan Iswap ko Boko Haram ne da suke zaune a waɗannan ƙauyukan."
"Ba cikakkiyar Daula suka kafa ba amma suna cikin ƙauyukan suna shige da fice," in ji shi.
Sai dai ya ce suna ganin kamar akwai hadin kai tsakanin ƴan bindiga masu fashin daji da kuma mayakan Boko Haram ko Iswap.
Ya ce mutane da dama sun tsere daga ƙauyukan da ke yankunan ƙanannan hukumomin na shiroro da Madaka.
A watan Oktoban da ya gabata wasu mazauna sun ce mayaƙan sun mamaye wasu ƙauyukan da ke cikin ƙaramar hukumar Shiroro suna yi wa mutane wa'azi, al'amarin da ya jefa jama'ar yankin cikin fargaba da tashin hankali.
Mazauna yankunan sun ce suna tara mutane suna yi musu wa'azi, suna kuma raba kuɗi a garin Kurebe da Kwaki.
Wannan na zuwa, watanni bayan Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar Boko Haram ta kafa tuta a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu.
Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello wanda ya tabbatar da kasancewar Boko Haram a jihar a watan Afrilu, ya ce mayaƙan sun kafa tuta ne a ƙananan hukumomin Kaure da Shiroro.
A makwannin da suka gabata ne Shugaban ƙaramar hukumar Shiroro Suleiman Chukuba, ya shaida wa Kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ƴan Boko Haram sun mamaye aƙalla ƙauyuka takwas daga cikin 25 na yankin.
Wasu rahotanni sun ce kusan ƙauyuka 500 ne mayaƙan suka mamaye a ƙaramar hukumar Shiroro.
Wasu mazauna yankin da BBC ta zanta da su sun ce ƴan Boko Haram sun ɓulla a makwabtan garuruwa ciki har da Mashekari da Lukafe da Kusaka da Sabon Gida da kuma Kwaki Chukuba. Kuma Mayaƙan har sun fara yi wa mutane hukunci.
Boko Haram sukan shigo gari su tara mutane a waje suna wa'azi da zartar wa mutane hukunci," a cewar wani mazauni yankin.
Ya ƙara da cewa mayaƙan sun samu wurin zama ne bayan janye jami'an tsaro a yankin nasu.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja Alhaji Sani Idris ya fadawa Reuters cewa gwamnatin jihar da kuma jami'an tsaro sun dukufa don dakile bazuwar 'yan Boko Haram din zuwa wasu yankuna.
Tun a watan Agustan 2020 aka fara bayar da rahoton ɓullar Boko Haram a Neja da ke makwabtaka da Abuja babban birnin Najeriya bayan wani bidiyo da ke iƙirarin nuna mayaƙan suna gabatar da saƙon gaisuwar Sallah.
Kusan fiye da shekara 12 jami'an tsaron Najeriya ke yaƙi da Boko Haram. Har yanzu ƙungiyar na ci gaba da zama barazana a Najeriya da ƙasashen da ke kewaye da Tafkin Chadi duk da mutuwar shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau.
A baya-bayan na dubban ƴan Boko Haram 8,000 ne suka miƙa wuya ga hukumomin Najeriya, sai dai bullar mayaƙan masu tayar da ƙayar-baya a jihar Neja da ke kusa da babban birnin Najeriya Abuja, wani al'amari ne da ke sake fito da buƙatar yin hubbasa don kakkeɓe duk wata barazana daga mayaƙan da har yanzu suke addabar yankin arewa maso gabashin Najeriya fiye da tsawon shekara 10.