Sheikh Ahmad Gumi: Dalilin da ya sa malamin ya gina wa Fulani makiyaya makaranta

Fitaccen malamin addinin musulunci na Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya faɗi dalilan da suka ya gina makaranta da asibiti da kuma wajen koyar da sana`a ga al`ummar Fulani makiyaya da ke yankunan karkara a jihar Kaduna.

Malamin ya shaida wa BBC cewa ya gina Cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio ne a garin Kagarko, a kusa da gandun dajin Kohoto da ke jihar ta Kaduna domin ilmantar da makiyaya.

A cewar Malamin ilimantar da makiyaya da samar musu da abubuwan more rayuwa ita ce hanyar da ta fi dacewa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya.

Ɗa'awar da malamin ya ƙaddamar ta shiga dazuzzukan da ƴan bindiga ke yin mafaka yana yi musu wa'azi da kira gare su su ajiye makamansu ta haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda wani ɓangare na ƙasar ke sukar matakinsa a matsayin nuna goyon baya ga munanan ayyukan da suke aikatawa.

Ya sha cin karo da hukumomi da kuma wasu ƴan ƙasar kan batun matsalar makiyaya da ake zargi suna fashi da satar mutane domin kuɗin fansa.

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ƙarancin ilimi na daga cikin matsalolin da ke ƙara ta'azzara matsalar tsaro a yankin arewacin Najeriya.

Wannan na daga cikin dalilin da malamin ya bayyana kan ƙaddamar da wani gangami na fita yankunan jihar Kaduna da ma wasu jihohin domin ilimantar da mazaunansu da kuma yi musu wa'azi.

Ya ya gano matsalolin makiyayan ne ta hanyar mu'amular da ya yi da su lokacin da yake shiga daji domin yi masu wa'azi.

Manufar gina makarantar

Sheikh Gumi ya fada wa BBC cewa babban abin da ya ja ra'ayin shi har ya yanke shawarar buɗe irin wannan makaranta shi ne girman matsalar da jahilci ya haifar a Najeriya.

A cewarsa matsawar za a samar da ilimi da sauran ababen more rayuwa a tsakanin al'umma, za a shawo kan matsalar rikici da sauran matsalolin tsaro.

"Yawanci idan ka ga irin al'amarin da ke damunmu a ƙasar nan to za ka ga yana da nasaba da jahilci. Kuma shi wanda yake buƙatar ya samu ilimi, matuƙar akwai makaranta ya san iyalins hi na zuwa to ba zai so ya kawo tashin hankalin da zai ɓata karatunsu ba."

Ya ce yana ganin makarantar za ta taimaka ga samar wa al'umma zaman lafiya a Najeriya.

Girman makarantar?

Makarantar a cewar Sheikh Gumi ta ƙunshi azuzuwa guda shida, da za a riƙa bayar da ilimi dai-dai da na makarantun firamare da sakandare.

Kuma an gina manyan ƙakuna da za a rika koyar da sana'o'i na mata da maza.

"Za a riƙa koya wa mata yadda ake dinke-dinke da yin sabulu da sauransu, inda su kuma maza za a koya musu yadda ake walda da kafinta da dai sauran sana'o'i da suke bukata." In ji Gumi.

Baya ga makaranta, malamin ya fada wa BBC cewa ya gina wa makiyayan asibiti da za ta taimaka musu wurin samun lafiya musamman mata masu juna biyu da Sheikh Gumi ya ce suna shan wahala a daji - "musamman masu nakuɗa da ake ɗauko wa kan mashin ana tsalle ana neman asibiti tsawon kilomita mai yawa."

"To idan suna da wurare irin wadannan, za su samu sauki wurin haihuwa.

Sheikh Ahmad Gumi ya ce tuni sun shirya da kungiyar malamai fulani wandanda sune za su taimaka su rike makarantar.

Malamin ya ce akwai buƙatar mashawartan gwamnati kan tsaro su shiga dazuka su fahimci irin matsalolin da fulani makiyaya ke fuskanta, don ɓullo da hanyoyin samar musu da abubuwan more rayuwa wanda hakan zai taimaka wurin magance matsalar tsaro.