Maganin tsarin iyali na maza: Wadanne hanyoyi suka dace a yi amfani da su?

Asalin hoton, SIMON MAINA
Akwai hanyoyi da dama da maza za su iya bi domin kare kai daga samun jaririn da ba a shirya haihuwar sa ba.
Bari mu fara da hanyoyi uku da kuka fi sani;
Kwaroron roba na maza
Amfani da kwaroron roba sananniyar hanya ce da maza ke amfani da shi domin kare kai daga yin cikin da ba a shirya ma sa ba.
Ana ganin kwaroron roba na ba da kariya daga daukar ciki da kashi 98 cikin 100, kuma ita ce kadai hanya daya tilo da ake ganin na bayar da kariya daga kamuwa da cutukkan da ake dauka ta jima'i.
Domin tabbatar da an yi amfani da su ta hanyar da ta dace, dole a duba lokacin da za su lalace, da tabbatar da cewa ba ta da wata illa misali budewar ainahin ledar da kwaroron ke ciki.
Sannan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bada shawarar sayan kwaroron roba daga kamfanonin da suke da ke kima, da kuma wadanda asusun Majalisar Dinkin Duniya ya san da su.
Duk da amfaninsu, dalilan da ake bayar wa na kin amfani da kwaroron roba ya danganta ne daga tsadarsu ko rashin samun gamsuwa a lokacin jima'i da sauransu.
Rashin gamsuwa yayin jima'i, ko Azalu
Sassaukar hanya ce amma kuma ba ta da tabbas, saboda kashi 27 cikin 100 na maza wannan lokacin na kubuce musu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana.
Wannan hanya ita ce ta saurin yin Inzali gabannin lokaci domin kaucewa yin ciki.
Hukumar lafiya ta Birtaniya NHS, ba ta aminta da wannan hanya a matsayin ta tsarin iyali ko takaita haihuwa ko kaucewa yin ciki ba.
Dalili kuwa shi ne, ruwan maniyyi ka iya fita gabannin lokacin gansuwa yayin jima'in, wanda kankani ne daman ke shiga mahaifa tare da zama Da.
Sai dai duk da haka, Moussa Diabaté kwararre a fannin lafiyar kwayayen haihuwa a Senegal, ya bayyana cewa matakin amfani da kwaroron roba, da janye azzakari gabannin fitar maniyyi na da tabbas, domin hanya ce da aka dade ana amfani da ita a kasar, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.
Sai dai ga Dakta Mobile Kampanga, kwararren likitan maza a Congo, ya ce ba wannan ce hanyar da ya ke bai wa abokan huldarsa shawarar amfani da ita.
''Hakikanin gaskiya, tsohuwar hanyar da ake amfani da ita ba ta aiki, sakamakon yawancin mazan da suka yi amfani da ita sun bada bayanai mabambanta.
Wasu daga ciki sun ce ba za su kara amfani da ita ba, yayin da wasu suka ce sam ba za su gwada yin hakan ba.
Ma'aurata, ko abokan rayuwa ka iya sake yin jima'i a karo na biyu, kuma ta yiwu wani daga cikin maniyyin namijin ya makale, sai a lokacin saduwa zai shiga mahaifar mace daga nan kuma ciki ya shiga.
Aikin Tiyata ga maza
Wannan wata hanya ce ta yin tiyata da ta hada yanke hanyar da maniyyi ke bi wajen fita, tare da toshe wajen.
Yawanci idan za a yi wa irin wannan tiyatar ana yi wa mutum allurar da ke kafe wani bangare na jiki, ma'ana mutum zai kasance idonsa a bude amma ba zai taba jin zafi ko sanin abin da ke faruwa, kuma aikin na daukar tsawon mintina 15 kacal.
Kamar yadda shafin hukumar lafiya ta Birtaniya NHS ta tabbatar, ta amfani da hanyar tiyata kwalliya na biyan kudin sabulu da kusan kashi 99.
Ana kallon wannan hanya da dawwamammiya, ko da yake ana iya komawa a sake mayar da komai yadda yake idan bukatar hakan ta taso.
Sai dai abin lura a nan shi ne ba a cika amfani da wannan hanyar ba a nahiyar Afirka, kamar yadda Dakta Kampanga ya bayyana cewa yawancin maza ba su yadda da wannan aikin tiyata ba.
Ya kara da cewa cikin shekaru 27 da ya dauka yana aiki a matsayin likitan fida da ya shafi mafitsarar maza, sau 10 kacal ya taba yin aikin tiyatar.
''Maza kalilan ne ke yadda da hakan,'' kamar yadda ya shaidawa shashen Afirka na BBC.
"Yawanci na fakewa da mahangar addini domin kaucewa aikin, yayin da wasu ke kaucewa hadarin aikin. Don haka ne suke tilastawa mata shan maganin tsarin iyali, domin su kubuta daga waccan tiyatar.''

Asalin hoton, SONNY TUMBELAKA
Shin me maza ke cewa kan batun?
BBC ta tattauna da maza a birane daban-daban na Afirka kamar Kwatano, da Kinshasa da Dakar, kan yadda suke kallon maganin tsarin iyali.
Ga abin da uku daga ciki suka bayyana, amma mun boye sunayensu saboda ba su kariya.
''Ba na amfani da duk wani nau'in tsarin iyali, kamar yadda muka aminta ni da matata, ba ta damu da shi ba kwata-kwata… Na san hanyar da na ke bi don kaucewa hakan, na san lokacin da ya kamata mu yi Jima'I, da lokacin da zan yi Inzali.
"Ina da 'ya'ya da yawa, da ba ma zan iya kirga yawansu ba, amma na riga na zabi tsarin da ya kwanta min a rai, ba yanzu ne zan dauki mataki ba. Idan matata ta dauki ciki, shi kenan haka Allah ya tsara.''
''Tun da na yi aure na daina amfani da kwaroron roba. Matata ta san yadda za ta kirga kwanakin da mahaifarta ke budewa da shirin daukar ciki, don haka muna kaucewa yin jima'I a wadannan ranakun.
A duk lokacin da muka san akwai hadarin daukar ciki, muna daukar mataki kamar yadda jami'an lafiya ke bayyanawa, wato za mu iya amfani da tsarin yin azalu, matukar ba mu yi hakan ba za ta iya daukar ciki.''
''Tiyatar tsarin iyali... Tiyatar tsarin iyali.. kai daga jin sunan kadai ya isa bata min rai, sam bai dace ba. Ina da Da mai shekara 1, don haka ina amfani da kwaroron roba a duk lokacin da zan sadu da matata, domin kare ta daga daukar wani cikin, saboda ban amince da sauran hanyoyin tsarin iyali ba.''
Wadanne hanyoyi ake amfani da su na tsarin iyali a Afrika?
A iya cewa baki daya a nahiyar Afirka, maza ba sa amfani da hanyoyin tsarin iyali ko dai na shan kwayar magani ko amfani da kwaroron roba, sai tsiraru daga ciki ne ke bin hanyoyin da jami'an lafiya suka bada shawara domin kaucewa yin cikin da ba a shirya ma sa ba.
Misali, Nazari na baya-bayan da asibitin Fartick da ke Senegal ya gano sama da kashi biyu na mazan kasar na amfani da tsarin iyali. Yayin da sama da kashi biyar ke amfani da tsarin Azalu domin takaita haihuwa, sai kuma sama da kashi bakwai da ke amfani da kwaroron roba.
Ana ganin hanyoyin kare kai daga daukar ciki, ya dogara ne baki daya akan Mata, ko dai shan kwayar magani, ko sanya zaren da ke toshe bakin mahaifa, domin hana daukar ciki da kidayar lokacin jinin al'ada, ko yin allura, ko maganin gargajiya da sauransu.
Dakta Madina Ndoye, kwararriyar likitar mata a asibin Grand-Yoff a birnin Dakar na kasar Senegal, ta ce yawancin bayanin da maza ke yi yana da alaka da addini da al'ada kan batun tsarin iyali, domin haka ne suke fakewa, tare da nade hannu sai dai mata ne kadai suke yin tsain iyali.
Wani mutum mai suna Bolozi Kalombo mazaunin birnin Kinshasa ya shaida mana cewa ya haramtawa matarsa shan maganin hana daukar ciki.
''Saboda ina son ganin mata na yin abu da gaske ba kulumboto ba, sannan jikinsu na sauyawa idan suna amfani da magani ko allura da sauran hanyoyin tsarin iyali.
Wannan dalilin ne ya sanya ni da matata ba mu amfani da duk wani nau'in tsarin iyali, saboda ni mabiyin addinin Kirista ne kuma littafin mu mai tsarki ya fayyace muna abu mai kyau da maras kyau.''

Ita kuwa Dakta Ndeye Khady Babou ta ce dorawa mata alhakin tsarin iyali ya samo asali ne tun iyaye da kakanni, kuma hakan za a yi ta tafiya kan wannan tsarin.
Ta kara da cewa idan har ana son a karfafa maza su yi amfani da hanyoyin tsarin iyali, to dole sai an sauyawa al'umma yadda suke kallon lamarin.
''Idan mutane suka fara Magana kan hakan, masu fafutuka suka ci gaba da daga murya, watakila hakan ya janyo hankalin hukumomi su dauki matakin da ya dace, na tsayar da kan al'umma musamman maza muhimmancin yin tsarin iyali, da sanin ba wai mata kadai ya shafa ba har da mazan.''
Likitar ta yi bayanin cewa dadewa ko yawan amfani da magungunan tsarin iyali ga mata yana da illa da ke janyo wa mata babbar matsala.
Sannan kamfanonin da ke yin magunguna a kasashe kamar Amurka da Faransa sun sha gurfana gaban kuliya saboda matsalar da wasu daga cikin matan da suka sha maganin tsarin iyali na kamfaninsu ya samar.
Shin yaya addinai ke kallon maganin tsarin iyali?
Babban malamin darikar katolika, Father Alfred Wally Sarr, jagoran gidauniyar Parish da ke Kounoune a Senegal, ya bayyana cewa a fannin katolika an amince da tsarin iyali ta hanyar duba dumin jikin dan adam, da lokacin shayarwa, da yin azalu matukar ma'aurata sun aminta da hakan.
Ya kara da cewa, Cocin katolika ba ta amince da duk wani abu da ya kaucewa koyarwar addinin kirista ba.
''Don me namiji zai sha maganin tsarin iyali? Jin dadin duniya ya ta'allaka ne ga aure da haihuwa. Coci na bai wa ma'aurata kwarin gwiwar yin tsarin iyalin da bai sabawa addini ko al'ada ba, '' in ji Abbé Alfred.
Sai dai Imam Ahmadou Makhtar Kanté, ya ce addinin musulunci ya amince da tsarin iyali idan dukkan bangarorin biyu sun aminta da hakan.
Sai dai wasu na ganin cewa, idan aka zo batun yin tiyata ko dandaka addinin musulunci bai aminta da hakan ba.
Imam ya kara da cewa; ''babu wanda yake da ikon sauya yadda wani bangare na jikin dan adam yake yin aiki da sunan tsarin iyali.
"Dole mu maida hankali kan hanyoyin da ba su haramta ba kuma aka amince da su, domin samun ingantaccen sakamako, hanyar da ba za ta cutar da kowa ba. Amma bisa dalilai na kiwon lafiya, addinin musulunci ya amince da yin aikin tiyata.

Ana ci gaba da bincike kan maganin tsarin iyali na maza
Ana ci gaba da gwaji da nazari kan hanyoyi da dama na tsarin iyali a sassa daban-daban na duniya. Wato amfani da kwayar magani ko sauyin jiki na Homourns(CHM)
Sama da shekaru 50 kenan da masana kimiyya suka dukufa suna nazari, sai di har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, kuma babu ko guda daya da aka fitar kasuwa.
Masana kimiyyar sun yi gwajin maganin tsarin iyali kan maza 100, sakamakon yana nuna ana da kyakkyawar fata, kamar yadda Farfesa Stephanie Page ta jami'ar Washington daya daga cikin marubutan nazarin da aka wallafa a shafin intanet na Endocrine Society ta bayyana.
Wani nazari da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi a shekarun 1990 zuwa 1996, ya nuna tasirin da allurar CHM ta mako-mako mai adadin mili giran 200 ga maza za ta yi gare su.
Me ya sa ake jiran tsammani kan maganin tsarin iyali na maza?
Wani bincike da China ta guda har sau biyu, a shekarun 2003 zuwa 2009, ya yi bayani kan ingancin yi wa maza tsarin iyali ta hanyar allura daya cikin watanni hudu.
Dakta Mobile Kampanga, ya shaida mana cewa likitoci ba sa bayar da shawarar yin allurar saboda illarta da ta ke yi a sauyin halittar dan adam, da rashin tabbas ga wanda aka yi wa.
Wata hanya da maza ke amfani da ita wajen kayyade iyali ita ce ta hanyar sanya matsattsen duros, na akalla sao'i 15 a kowacce rana na tsahon watanni uku, da nufin dumama maniyyin yadda ba zai yi tasirin fitar da kwan haihuwa ba.
Wannan tsari ya nuna tasiri kan mazaje 51 da akai gwaji akan su, daya daga ciki ne kadai aka samu kuskure ciki ya shiga, shi ma din bai yi amfani da tsarin yadda ya dace ba, kamar yadda kungiyar likitocin fidar mafitsara na kasar Faransa suka bayyana.
Yin allura mai nau'in mai
Wata kungiya mai zaman kan ta a Amirka, Parsemus Foundation ta dade tana nazari akan allurar da ake yi wa 'ya'yan gwailo, wadda a hankali cikin shekaru take yin tasirin toshe hanyar da maniyyi ke fita.
Hanya ce mai sauki kuma marar hadari da za a iya sake yin wata allurar domin narkar da toshewar, kamar yadda kungiyar likitocin fidar mafitsara na kasar Faransa suka bayyana.
Kawo yanzu an yi gwajin allurar kan Birrai da zomaye, kuma alamu sun nuna tasirinta, amma sai har yanzun ba a samu cikakken sakamako kan sake yin allurar da kuma narkar da toshewar hanyar da miniyyin ke fita ba.
Maganin da ake shaka
Tun shekarar 2016 masu bincike a Birtaniya suka dukufa domin nazari, kan maganin tsarin iyali na shaka, da zi yi tasirin rage karfin maniyyi.
Wannan aikin wasu kwararru biyu ne na jami'ar Wolverhampton, Farfesa John Howl da Dakta Sarah Jones.
Sun yi aikin hadin gwiwa da jami'ar Aveiro, ta Portugal, a wani bangare na binciken shekaru uku da aka warewa Yuro 194,000 domin aiwatar da shi, domin gano illar da maganin shakar ka iya yi wa kwayoyin halittar dan adam, da yadda za su kayyade maniyyin da namiji ke fitarwa.











