Zamantakewa: Me ya sa ake tsangwamar matan da suka samu jinkirin aure?
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 20 din, shirin ya yi duba ne kan yadda irin kallon da al'umma ke yi wa macen da ta samu jinkirin aure.
Yaushe za ki yi aure? Kin ki aure kina ta boko har sai kin ga karshen biro ko?
Wance ai ta kama kasa tana jam babbar mota da albashi mai tsoka yaushe za ta so aure.
Wadannan su ne ire-iren kalaman da za a ji mutane na furtawa a kan mata da suka samu jinkirin aure a cikin al'ummarmu.
Shekara ashirin da suka gabata a lokacin ina karatun digiri a jami'a kuma ban yi aure ba, sai wata kawata mai aure ta nemi mu je gidan wata kawar tamu ita ma mai aure don kai mata ziyara.
Bayan an gaggaisa, budar bakin wacce muka je gidan nata sai ce min ta yi, wai ke Halima Umar yaushe za ki yi aure ne? Ko kuwa sai an ga karshen boko?
Sai suka sa dariya dukkansu.
Wannan magana ta soki zuciyata sosai, don ita ba ta san irin abubuwan da suka yi min dabaibayi har aka kai wannan lokacin ban yi auren ba.
Sannan ba ta san na fita son ni ma na ga ina cikin inuwar auren ba, amma don rashin adalci sai ta yanke min hukunci kai tsaye.
Wannan matsin lamba shi ne miliyoyin mata suke fuskanta har yanzu a zamantakewar al'ummarmu.
Wata marbuciya kuma malamar makaranta Amina Hassan Abdussalam ta ce matan da suka isa aure kuma lokacinsu bai yi ba na shiga halim tasku daban-daban
"Ana yawan tsangwamarsu da dora musu laifin da yawanci ba su isa su tabbatar da shi ba sai lolacin yin sa ya yi.
"Wani lokacin ma tsangwamar kan fara ne daga gida wajen iyaye da 'yan uwa har zuwa sauran al'umma.
"Hakan kan jefa dumbin mata cikin tsananin damuwa wato depression."
Mutane da dama kan dauka tsabar kwadayi da joran mai kudi ko wasu dogayen burika na daban ko kuma yawan bin maza irin wadannan mata ke yi shi ya sa ba sa auruwa da wuri.
Amma a gaskiya kudin goron da ake musu ba daidai ba ne sam, don a wani bincike da na gabatar ta hanyar jin ra'ayoyin mata da dama kan batun, kusan duk na lura su ma sun matsu da su yi auren don samun nutsuwa.
Don wata za a ga ta haura shekaru 30 wata ma ta kai 40 har ma fiye amma lokacin aure bai yi ba.
Tabbas na san ba a rasa tsirarun 'yan mata masu dogon buri kan aure, amma mafi yawan mata kowacce so take ta ga ta shiga daga ciki ita ma, amma wasu matsaloli da cakwakiya da suke ciki ke jawo musu tsaiko.
Wani babban malamin Musulunci Sheikh Dr Abdullah Gadon Kaya ya ce matan da suka dade ba su yi aure ba sun kasu kashi hudu.
"Akwai wacce kawai lokacin ne bai yi ba duk da cewa ta mallaki abubuwan nagarta sosai.
"Akwai wacce namijin aljani ke aurarta shi ya sa sai a ga ko maneman ba ta da su.
"Sannan akwai 'yan tsirari da suke saka dogaye burika a ransu da zummar sai sun samu cikar buri kafin su yi auren.
To Malam dai bai bar mu haka ba sai da ya jawo hankalin al'umma kan irin adalcin da ya kamata su dinga yi wa matan da suka samu jinkirin aure.
"To a nan wajen al'umma sai ku dinga musu adalci, ku daina yanke musu hukunci kan abin da ba ku san silarsa ba.
"Wadanda rashin lafiya kuma ta hana su auren sai mu taya su da addu'a."
"Sannan masu dogayen burikan nan sai su ma a yi musu addu'argane gaskiya."
Sannan su ma wadanda Allah Ya dora musu jinkirin auren ke ma malam ya ba ki shawarwari na inganta zamantakewarki yadda ko da al'umma za ta miki kage Allah Yana kallon ayyukanki.
"Na farko shi ne Hajiya ki kame kanki kar ki ba da kofar da za a dinga miki wani kallo na mai dogon buri ko wacce ta ki aure don som holewa."












