Boeing zai sasanta da iyalan fasinjojin da suka mutu da ya yi hatsari

Asalin hoton, Reuters
Kamfanin kera jirgin sama na Boeing, ya amince da sasantawa da iyalan fasinjoji 157 da suka mutu sakamakon hadarin da jirgin samfurin 737 Max ya yi a kasar Habasha a shekarar 2019.
Wata kotu a birnin Chicago na Amurka, ta ce kamfanin ya kuma dauki alhakin abin da ya haddasa hadarin da ya janyo asarar rayuka. Su kuma iyalan fasinjojin ba za su bukaci a dauki matakin ladabtar da kamfanin jirgin saman ba.
Lauyoyin fasinjojin, sun ce duk da haka alhakin abin ya rataya a wuyan Boeing, inda suka yi maraba da yarjejeniyar da cewa gagarumar nasara ce ga wadanda suke karewa.
Jim kadan bayan wannan labarin, hannayen jarin Boeing sun fadi da kashi daya cikin 100. Wannan yarjejeniya ta bude hanya ga iyalan fasinjojin da ke kasashen Habasha da Kenya damar karbar kudaden diyya da taimakon kotun Amurka.
Maimakon su tsaya can kasashensu ba tare da sun san abin da ke faruwa ba, kuma ta yiwu su sha bakar wuya kafin a ba su diyyar ko ma a ba su dan kudin da bai taka kara ya karya ba.
Mark Pegram wanda dan Birtaniya ne da danshi Sam ke cikin wadanda suka mutu, ya shaida wa BBC cewa abu mai muhimmanci a gare su shi ne, kamfanin Boeing ya amince da aikata ba daidai ba, ba tare da ya karkatar da hankali kan dora laifin ga kamfanin jirgin saman Ethiopian Airlines ko matuka jirgin ba... daman abin da suke bukata shi ne kamfanin ya amsa laifinsa.
Ita ma mahaifiyar Sam, Debbie ta shaida wa BBC cewa: "Abin da muke bukata shi ne samun kudin diyyar, domin kafa wata gidauniya da za mu sanya mata sunan Sam. Abin da muke son yi da kudin kenan, kuma na tabbatar da Sam yana raye zai yi farin ciki da hakan."
A lokacin da hatsarin ya faru, kasuwar jiragen kamfanin Boeing samfurin 737 Maxt na samun tagomashi, amma bayan hatsari na biyu da jirgin ya sake yi cikin 'yan watanni, wanda ya faru da jirgin Ethiopian Airlines daga Addis Ababa, da kuma na Lion Air wanda ya fada tekun da ke kusa da Indonesia - sakamakon daukewar sadarwa , ake ta samun jiragen kamfanin da matsaloli abin da ya janyo aka fara kaurace musu.
An jingine jiragen na sama da watanni 20, yayin da a bangare guda ake gudanar da bincike a kai. Daga bisani an amince ya koma bakin aiki bayan gano matsalolin da ke haddasa hadarin da kuma hanyar magancewa ciki har da sake bai wa ma'aikata da matuka jirgin horo.











