Poland za ta gina katanga kan iyakarta da Belarus saboda ƴan gudun hijira

..

Asalin hoton, Reuters

Ƙasar Poland ta amince ta gina katanga kan iyakarta da Belarus sakamakon yadda ake samun ƙaruwar masu ƙetarawa cikin ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

Ministan harkokin cikin gida na ƙasar, Mariusz Kaminski ya ce za a aika wa majalisar ƙasar wannan kuduri domin tafka muhawara a kai da kuma yanke hukunci a kai.

Kudurin dokar dai ya tanadi gina katanga mai ƙwari da tsawo inda za a kafa mata na'urorin da za su rinƙa sa ido da kula da giftawar duk wani abu.

Tuni dai sama da sojojin Poland 3,000 suka yi aikin gina wata katanga ta wucin gadi da aka yi da wayar ƙarfe mai ƙayoyi a kan iyakar ƙasar.

Tun daga watan Agusta, sama da mutum dubu 16 ne suka yi niyyar tsallaka iyakar ba bisa ƙa'ida ba, idan aka kwatanta da mutum 120 da suka yi ƙoƙarin yin hakan a bara, wanda hakan ke nufin lamarin ya ƙara ƙamari.

Ƙasashen Poland da Lithuania da Latvia da ma Tarayyar Turai ɗungurumgum, duk sun zargi Shugaban Belarus Alexander Lukashenko da bayar da kafa ga ƴan ci rani musamman daga Gabas Ta Tsakiya domin su shiga Tarayyar Turai.

Ministan harkokin cikin gida na Poland Mariusz Kaminski ya bayyana cewa matakan da gwamnatin Alexander Lukashenko ta ɗauka na buƙatar martani mai ƙarfin gaske

Ya kuma bayyana cewa an gina irin wannan katangar a wasu ƙasashe tare da cewa wannan da za a gina za ta zama zakaran gwajin dafi tsakainta da Belarus.

A farkon watan da ya gabata ne Poland ɗin ta saka dokar ta ɓaci a kan iyakarta, inda ta haramta wa ƙungiyoyi masu zaman kansu da ƴan jarida zuwa wurin.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun zargi dakarun gwamnati da ke tsaron iyakar ta Poland da saɓa dokar ƙasa da ƙasa kan ƴan gudun hijira sakamakon yadda suka rinƙa korar ƴan gudun hijirae zuwa cikin Belarus. Dokar dai ta ce dole ne a bai wa mutane damar bin matakan samun mafaka ko da sun shiga ƙasa ba bisa ƙa'ida ba.

Ƴan gudun hijira da dama ne dai suka mutu a kusa da iyakar ƙasar saboda rashin lafiya