Abd al-Rahman al-Milad: An kama mutumin da ke safarar mutane a Libya

Bayanan bidiyo, Fiye da ƴan ci rani da ƴan gudun hijira 500,000 ne aka ƙiyasata cewa sun maƙale a Libiya

Hukumomi a Tripoli babban birnin Libya sun kama wani mutum da rundunar ƴan sanda ta ƙasa da ƙasa ke nema ruwa a jallo kan safarar mutane.

Gwamnatin Libya da ƙasashen duniya suka yarda da ita ta sanar da tsare Abd al-Rahman al-Milad, wanda aka fi sani da Bija, a ranar Laraba.

A shekarar 2018, Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙaƙaba wa Mista Milad da wasu mutanen biyar takunkumin, kan safarar mutane a ƙasar.

Libya ta zama wata babbar hanyar fitar da ƴan ci rani zuwa Turai a shekarun baya-bayan nan.

Ƙasar ta samu kanta cikin karya doka tun bayan hamɓarar da gwamnatin daɗaɗɗen shugaban ƙasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011, inda mayaƙan sa-kai ƴan adawa suke neman kaɓar mulkin.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce ƴan ci ranin da ke Libya na fusakantar cin zarafi da muzgunawa.

Ofishin jakadancin Libya ya nuna jin daɗi da kama Mista Milad, inda ya bayyana hakan a matsayin "labari mai daɗi da za a magance safarar mutane."

Baya ga nemansa da rundunar ƴan sanda ta ƙasa da ƙasa ke yi, ita ma ƙasar Libya ta ayyana nemansa.

Amma ƙoƙarin kama mutanen da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ke yi yana wahala a Libya, saboda irin ƙarfin ikon da mayaƙan sa-kai ke da shi a ƙasar.

Wane ne Abd al-Rahman al-Milad?

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, Mista Milad ya taɓa zama shugaban masu kula da gaɓar teku na garin Zawiya da ke arewa maso yammacin ƙasar, "inda ake alaƙantawa da rikicin fitar da ƴan ci rani da sauran masu safarar mutane."

Tawagar ƙwararru ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a shekarar 2017 Mista Milad, da wasu masu gadin gaɓar tekun, "suna da hannu a nutsewar da kwale-kwalen ƴan ci rani suka yi ta hanyar amfani da makamai."

Ana zarginsa da buɗe wata cibiyar tsare mutane a Zawiya, inda a can ake cin zarafin ƴan ci rani, kuma shi ne mai shirya yadda za a yi safarar mutanen, a cewar tawagar.

A farkon watan nan ne, Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da wani ƙuduri na bai wa ƙasashen da ke cikin kwamitin damar duba jiragen ruwan da ake zargin ana safarar mutane da su a gaɓar tekun Libiya.

A watan Maris, Ofishin da ke kula da ƙaurar mutane a duniya ya ƙiyasta cewa fiye da mutum 20,000 ne suka mutu yayin da suke tsallake Tekun Bahar Rum a shekarar 2014.