Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taraba: Yadda malaman makaranta a jihar ke rayuwa wata shida ba albashi
Malaman makarantun firamare da ma'aikatan kananan hukumomi a jihar Taraba na ci gaba da koka wa kan rashin biyan albashi na tsawon watanni shida.
Wannan na zuwa ne a yayin da ake kara samun tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi biyo bayan karuwar farashin dala a Najeriya.
Ma'aikatan na cewa sai sun sha baƙar wuya suke iya riƙe kansu a halin da suke ciki, sakamakon rashin biyansu haƙƙokinsu.
Daya daga cikin dubban wadannan ma'aikatan ya ce sai an yi kamar za a magance musu wannan matsala, amma sai hannun agogo ya koma baya.
"Yanzu ta kai idan ka je karbar bashi a matsayinka na malamin makaranta ma sai a hana ka idan aka gane cewa kai malami ne, domin an san cewa ba za ka iya ba, don ba ka da abun biya," in ji shi.
Ita ma wata malama da BBC ta zanta da ita ta ce a halin da suke ciki suna nan suna ta kuka da 'ya'yansu don ba su da hatta abincin da za su ba su.
A cewarta ''Yanzu ko neman aure malami ya je yi baya samun mai aurarsa, sai dai ya nemi bazawara, domin sai ta rika ganin me zai ci me zai ba ta''.
Batun jinkiri wajen biyan albashi ga ma'ikata a wasu jihohin Najeriya dai ba sabon abu bane, to amma tsawon lokaci da kuma watanni da ake kwashewa ba tare da biyan ba ya sha ban-ban daga wata jihar zuwa wata.
Su ma ma'aikatan kananan hukumomin jihar na cikin irin wannan yanayi, don watanni bakwai kenan suna aiki ba tare da iya rarrabe farko da karshen watanni ba.
Wannan hali da ma'aikatan ke shiga dai ya sa wasunsu sun fara yanke kauna da samun ingantacciyar rayuwa ta hanyar aikin da sukeyi.
Alhaji Abubakar Bawa shi ne mai bai wa gwamnan jihar Taraba shawara kan harkokin siyasa, kuma ya shaida wa BBC cewa ''Ba shakka ana biyansu hakkokinsu, amma ba zan iya ce maka ga inda aka tsaya ko watan da aka tsaya ba, amma ana ci gaba da biya''.
A halin yanzu dai malaman makarantun firamaren na zaman jiran gwamnatin jihar domin biyan su albashin watanni shida idan aka hada da na watan biyun shekarar 2016 da ba'a biya su ba, yayin da su kuwa ma'aikatan kananan hukumomi ke bin gwamnatin albashin watanni 7.