Hotunan yadda gadar da ta hada jihohin Filato da Taraba ta rufta

Wasu hotuna na yadda gadar da ta hada jihohin Filato da Taraba da ke tsakiyar Najeriya ta rufta.

Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya na cewa wata babbar gada da ta hade jihar da makwabciyarta jihar Taraba ta ruguje sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Gadar wacce ke tsakanin yankunan Wase da Langtang da ke jihar ta Filato ta kasance wata babbar mahada tsakanin jihohin Filato da Taraba a tsakiyar kasar, inda a kullum dumbin mutane ke zirga-zirga ta tattalin arziki da zamantakewa.

Lamarin ya sanya harkoki sun tsaya cak.

Gwamnan jihar ta Filato Simon Lalong wanda ya ziyarci gadar da ta karye, ya jajanta wa al'umomin yankin kana ya yi alkawarin kai musu dauki.

Gwamnan wanda ya kai ziyarar a ranar Talata, ya ce ko da yake wannan hanyar ta gwmanatin tarayya ce, to amma gwamnatin jihar za ta yi bakin kokarinta don ganin an dauki matakin sake gina ta.

Ya shaida wa jama'ar yankin da kuma sarakunan gargajiya a yayin ziyarar, cewa a mataki na wucin gadi, yanzu hukumomin jihar za su samar da jiragen ruwa ko kwale-kwale da za su taimaka wajen tsallaka wa da matafiya tsakanin jihohin biyu.

Mista Lalong ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta sanar da gwamnatin tarayya domin kai dauki na gyara gadar da ma hanyar baki daya.