Pandora Papers: An tona asirin wasu manyan shugabanni da attajiran duniya

Asirin wasu shugabanni da attajirai da manyan 'yan siyasa na duniya ya tonu a daya daga cikin manyan bankaɗar sirri da aka taba samu na bayanan arzikinsu.
An bankaɗo bayanan arzikin wasu shugabannin kasashen duniya 35 na da, da na yanzu, da jami'an gwamnatoci fiye da 300 daga kamfanonin da aka sa a takardun Pandora.
Takardun sun shafi bayanan hada-hadar kuɗi na Sarkin Jordan da tsohon Firaiministan Birtaniya Tony Blair da Shugaba Vladimir Putin da Firaimistan Czech Andrej Babis da dai sauransu.
Bayanan sun gano cewa Sarkin Jordan ya boye dukiya mai dumbin yawa da kadarori har na fam miliyan 70 a Birtaniya da Amurka.
Takardun sun kuma nuna yadda tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair da matarsa suka adana fam 312,000 a lokacin da suka sayi ofishinsu na Landan.
Bankadar ita ce ta baya-bayan nan a cikin shekara bakwai da aka yi, bayan na takardun Paradise da Panama da kuma Lux da kuma FinCen.
Bayanan da aka fallasa sun kuma alaƙanta Shugaba Vladimir Putin da wasu kadarori a Monaco, haka kuma sun tabbatar da cewa Firaiministan Czech Andrej Babis- wanda zaɓe ke gabansa a cikin makon nan- bai bayyana wata kadararsa ba, wani kamfanin ƙasar waje da ya yi amfani da shi wajen sayen maka-makan gidaje biyu a kudancin Faransa.
Duncan Hames, wanda darakta ne a ƙungiyar Transperency International da ke yaƙi da cin hanci da rashin adalci a duniya, ya ce wahala kullum a kan talaka dai kawai take ƙarewa.
"Idan ɗan siyasa ya azurta kansa ta hanyar mulki, mutane gama gari maza da mata ne kawai ke wahala kuma waɗanda ƙasarsu ke ci gaba da talaucewa. A wani lokacin ba ma batun ƙin biyan haraji bane. Idan kai ma'aikacin gwamnati ne kuma ka karɓi cin hanci domin ka bayar da kwangila ta gina asibiti ga wani naka, hakan ba abin ci gaba bane ga ƙasarka, kuma ƙasarka za ta wahala ne saboda cin hancin da ka karɓa", in ji Mista Hames.
Shi ma shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ba a bar shi a baya ba domin binciken ya bankado cewa iyalansa sun mallaki kamfanoni da dama a sirrance da ke ƙasashen waje.
Cikin kadarorin da suka mallaka har da hannun jari da kuma takardun lamuni na miliyoyin daloli.
Wannan bincike dai ya kuma gano cewa akwai wasu makusantan Firaiministan Pakistan Imran Khan - ciki har da ministocinsa da iyalansa da suka mallaki kamfanoni na miliyoyin daloli.
Wannan dai ya kasance bincike mafi girma da gamayyar ƴan jarida masu binciken ƙwaƙwafi a duniya suka gudanar inda sama da ƴan jarida 650 sukayi wannan aikin.











