Ra'ayi: Me ya sa neman gafarar kisan kiyashin Namibia da Jamus ta yi bai isa ba?

Tsakanin 1904 da 1908 dubban ƴan kabilar Herero da Nama aka kashe

Asalin hoton, National Archive of Namibia

Bayanan hoto, Tsakanin 1904 da 1908 dubban ƴan kabilar Herero da Nama aka kashe

Neman gafarar da aka daɗe ana jiran Jamus ta yi game da kisan gilla a Namibia a ƙarnin da ya gabata ya sake haifar da tambayoyi game da yadda ƙasashen Turai ke fuskantar abin da suka aikata lokacin mulkin mallaka a Afirka, kamar yadda mai sharhi a Namibia Emsie Erastus ya bayyana.

A makon da ya gabata, bayan kammala sasanci da Namibia, ministan harakokin wajen Jamus Heiko Maas ya sanar da cewa ƙasarsa ta yi kisan kiyashi a ƙasar da ta yi wa mulkin mallaka.

Ta kuma yi alƙawalin bayar da tallafin da ya kai sama da dala biliyan ɗaya.

Turawan mulkin mallaka na Jamus sun kashe dubban ƴan ƙabilar Ovaherero da Nama a Namibia tsakanin 1904 da 1908. Wannan ya kai kashi 80 na Harero da sama da kashi 40 na ƴan Nama.

An kuma kwace filaye da dabbobinsu. Wannan wani hukunci ne kan laifin boren da suka yi.

Waɗanda aka kama daga boren Ovaherero an kashe su ko kuma an azabtar da su

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Waɗanda aka kama daga boren Ovaherero an kashe su ko kuma an azabtar da su

Sanarwar da kafofin watsa labarai suka bayar ranar Juma'a an yi taka-tsan-tsan da kaucewa jan hankali don kauce wa duk zuwa ga matakin shari'a.

Wannan na zuwa yayin da rarrabuwar kai ke ƙaruwa tsakanin al'ummar Ovaherero da ke ci gaba da yunƙurin ƙalubalantar Jamus a kotu kan kisan ƙare dangi.

An shirya sakon ne don Jamusawa masu nuna shakku cewa, bisa ga bincike da aka gudanar da dama, ba a tuna kashe-kashen ba ko kuma tarihin ƙasar a matsayin babbar rundunar mulkin mallaka da ta yi mamayar Togo da Namibia da Burundi da Tanzania.

Sanarwar da ba ma'ana

Dangane da amincewa da tarihin mulkin mallaka da ta yi a Namibia, Jamus a kullum ba ta son yin hakan. Wannan duk da bayar da tallafi na ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatocin da suka gabata tun samun ƴancin kan Namibia a 1990.

Wani uzuri mai jan hankali da ministan ci gaban Jamus ya gabatar a shekarar 2004, a kan cikar shekaru 100 da fara kisan kare dangi ya sha suka.

Wani abin tunawa da kisan kiyashin Nambia da aka gina a garin Swakopmund

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani abin tunawa da kisan kiyashin Nambia da aka gina a garin Swakopmund

Kukan da al'ummomin da aka tarwatsa suka yi kan amincewa da kisan gillar ba tare da wata shakka ba, neman gafara, da biyan diyya ya zama abin karfafawa. A sakamakon haka, gwamnatocin biyu ba su da zabi.

Tatattaunar ce ta kai ga amincewa da kisan kiyashin, amma kuma yadda aka sanar ba ma'ana.

Da farko, an fitar da sanarwar cikin gaggawa saboda dalilai na cikin gida da sauran dalilai na siyasa. A kan haka, dukkaninsu haɗi da gwamnatin Namibia sun shiga taraddadi

Wasu masu sharhi na cikin gida sun yi hasashen an zaɓi lokacin ne domin kawar da hankalin jama'a bayan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nemi gafarar Rwanda kan rawar da ta taka a gisan kiyashin ƙasar a 1994.

Na biyu, an ki yarda da sasantawar saboda rashin cimma sharuddan bukatun biyan kuɗin

Kuɗaɗen da Jamus za ta bayar, waɗanda ba su taka kara sun karya ba fiye da yadda wasu suke fata, za a yi amfani da su ne domin gudanar da ayyukan ci gaba.

Wasu sarakunan gargajiya sun bayyana adawa da yarjejeniyar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu sarakunan gargajiya sun bayyana adawa da yarjejeniyar

Har yanzu babu tabbar kan waɗanda za su ci moriyar kuɗaɗen. An ƙulla jarjejeniyar ba tare da wakilcin ƙabilun da aka yi wa kisan kare dangi ba a waurin tattaunawar.

Amma tallafin na ci gaba shi ma yana da matsala.

Jamus ta bayyana cewa tana son shafe laifukan da ta aikata zamanin mulkin mallaka.

Amma kuma kasar tana buƙatar ta yi la'akari da asalin ra'ayin wariyar launin fata na duniya, inda ake sanya shugabannin yammacin duniya a sama na Afirka a kasa.

Tallafi

A zamanin mulkin mallaka, ana ɗaukar ƴan Afirka a matsayin waɗanda ba su da 'asali' waɗanda ba su iya kawo sauyi a tattalin arziki da fasaha, abin da manyan ƙasashe suka fake da shi.

Wannan tunanin ya bayyana yadda ƙasashen yammaci suka ɗauka ƴan Afirka a baya, kuma har yanzu ana samun haka.

Har yanzu ana bayar da tallafi na ci gaba ta hanyar dangantaka. Amma ba ta lalata dangantakar da ta bayar da damar yin kisan gilla ba tun a farko.

line

Mutanen Ovaherero da Nama ba su kadai ba ne a cikin mutanen da neman diyya daga turawan mulkin mallaka.

Ƙabilu da dama da kasashe daban-daban sun nemi diyya a shekarun baya.

Burundi da Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Congo suna buƙatar dala biliyan 43 daga Jamus da Belgium kan abin da suka aikata.

A bara Sarkin Belgium Philippe ya bayyana taikaicinsa kan abin da ƙasarsa ta aikata a Jamhuriyyar Congo, amma kuma ya kaucewa neman gafara.

Duk da yake bayanai na yin nadama da neman gafara sun kasance kusan yau da kullun, amma biyan diyya har yanzu wani baƙon abu ne.

Matakin shari'a, da kuma ikirarin duniya, sun sa Turawan mulkin mallaka jan ƙafa.

Yarjejeniyar ta biyo bayan kokarin da aka shafe shekaru ana sasantawa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yarjejeniyar ta biyo bayan kokarin da aka shafe shekaru ana sasantawa

A Namibia, dangin waɗanda aka kashe an raba su da gidajensu da al'adunsu, wasunsu sun koma Botswana da Afirka ta Kudu, nesa da gidajensu.

Yahudawa kuma sun samu mafaka saboda Holocaust, amma ƙabilun Ovaherero da Nama sun yi ƙoƙarin samun wannan damar

Ba abin mamaki ba ne da sarakunan gargajiya suka yi watsi da sanarwar Jamus, haɗi da waɗanda ake zargi suna goyon bayan ƴan Namibia.

Sarki Manase Zeraeua na Zaraeua da yake magana a madadin kwamitin sarakuna biyar da gwamnati, ya fitar da sanarwa yana yin watsi da tsarin wanda ya gaza cimma buƙatunsu.

Babu tuntuɓa

Given the severity of the genocidal murders perpetrated, the amount offered by the Germans for reconstruction work over a 30-year period has been deemed unacceptable by the chiefs.

Ganin tsananin kisan gillar da aka aikata tsawon shekaru 30, sarakunan sun yi watsi da tayin kuɗin da Jamus ta ce za ta biya.

Kuma suna tambayar yadda Jamus ta yanke shawara kan adadin kuɗin.

A cewar sarakunan, ba a tuntuɓi mutanen Ovaherero da Nama waɗanda matsalar ta shafa, a tattaunawar.

Domin tabbatar da samun nsara, yana da matuƙar amfani a tantance girman illar da mulkin mallaka ya yi ta hanyar sauraren waɗanda abin ya shafa.

Wannan wani darasi ne ga ƙasashen da suka yi mulkin mallaka idan da gaske suke domin sasatawa.