Ecuador: Yadda fursunoni 116 suka mutu a rikicin gidan yari

Several inmates remain on the roofs of the Litoral prison in Guayaquil, Ecuador, 28 September 2021.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu fursunonin sun hau kan rufin gidan yarin lokacin da fadan ya yi ƙamari

Iyalai da dama da ke cikin tashin hankali sun taru a gaban gidan yari a Ecuador inda 'yan sanda ke kokarin shawo kan lamurra bayan wani fada da ya yi sanadin mutuwar a kalla fursunoni 116.

Fadan ya barke ne a ranar Talata, inda fursunoni suka dinga amfani da abubuwan fashewa da makamai wajen fada da junansu.

Iyalai na neman labari kan danginsu, amma da yake wasu mutanen da suka mutu sun rasa wasu bangarorin jikinsu, za a shafe kwanaki kafin a gane mutane da dama.

Rikicin gungun fursunonin shi ne mafi muni a tarihin Ecuador.

Ba a san ainihin abin da ke faruwa a cikin gidan yarin ba. Jami'ai sun ce a ranar Laraba sun samu shawon kan rikicin tare da karbe iko da gidan yarin, amma a ranar ALhamis da safe makwabtan yankin sun ce sun ji karar fashewar abubuwa da harbin bindiga.

Jim kadan bayan nan 'yan sanda suka ce za su sake tura jami'ai 400 don shawo kan lamarin.

Ta yaya rikicin ya fara?

Fadan farkon ya faro ne a ranar Talata lokacin da fursunoni daga wani bangaren gidan yarin suka kutsa ta karkashin wata iyaka don shiga wani bangaren gidan, inda suka far wa wasu fursunonin da suke gaba da su.

'Yan sanda sun samu tseratar da masu dafa abinci shida a sashen da aka yi fadan, inda suka kai su wani amintaccen waje, amma an ji wa ƴan sanda biyu rauni.

Shugaban gidan yarin Ecuador Bolívar Garzón, ya ce ƴan sanda sun ga gawa 24 ranar Talata da suka shiga gidan yarin.

A cewar Mr Garzón, an ci gaba da harbe-harbe a cikin gidan yarin da tsakar daren Talata har zuwa wayewar garin Laraba, kuma da ƴan sanda suka dinga shiga sashen ɗaya bayan ɗaya sun tarar da karin gawarwaki, inda aka gano yawan waɗanda suka mutu ya kai 116.

Ɗumbin iyalai sun yi dafifi a gaban gidan yarin, yayin da jami'an tsaro ke ciki da wajensa.

Wasu daga cikin dangin fursunonin sun ce an aika musu hotuna da bidiyo na abin da ya faru a ciki amma ba a ba su wani bayani a hukumance kan ko ƴan uwansu na daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

Wata jarida El Comercio ta ruwaito cewa wata mace ta gane mijinta a ɗaya daga cikin bidiyon. Ta ce yana daga cikin waɗanda aka yanke wani ɓangare na jikinsu.

Su waye suke fadan?

Gano cewa ƴan sanda biyu ne kawai suka jikkata amma fiye da fursunoni 100 sun mutu ya sa aka yarda cewa fada ne tsakanin fursunonin fiye da ƙoƙarin tserewarsu.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa ta iya yiwuwa an bayar da umarnin tayar da hargitsi ne a gidan yarin daga waje saboda rikicin neman iko tsakanin masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke faruwa a Ecuador.

Jami'an gidan yarin Litora sun tsare fursunonin ne daga wani gungun masu hada-hadar miyagun ƙwayoyi ƴan Ecuador waɗanda aka tabbatar suna da dangantaka da manyan masu safarar miyagun ƙwayoyi na Mexico.

An inmate is seen at a prison in Guayaquil, Ecuador, on September 29, 2021, after a riot occurred.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Akwai ɓangarorin adawa na masu safarar ƙwayoyi da gidan yarin

Amma wata kungiyar masu aikata miyagun laifukan ta Mexico mai suna Jalisco New Generation cartel (CJNG), tana ƙoƙarin haɗa kai da gungun ƴan Ecuador don ƙwace iko da hanyoyin da ake fataucin miyagun ƙwayoyi zuwa yankin Tsakiyar Amurka daga ƴan adawarta na Sinaloa.

Yanayin faɗan da ya farun a cikin gidan yarin rikici ne irin na masu safarar miyagun ƙwayoyi ƴan Mexico, da a mafi yawan lokuta suke kashe ƴan hamayyarsu ta mummunar hanya don sake bai wa mutane tsoro.

Ta yaya lamarin ya yi muni?

Wannan rikicin na baya-bayan nan shi ne amfi muni a tarihin tsarin gidan yarin Ecuador amma an sha samun munanan fito-na-fito a shekarar da ta gabata.

line

Manyan abubuwan da ke jawo rikici a gidan yarin Ecuador:

  • Ecuador ta zama wata ƙasar yada zango ga masu safarar koken daga maƙwabtan ƙasashe irin su Peru da Colombia
  • Miyagun masu safarar koken na Mexico sun faɗaɗa kutsaw cikin Ecuador kuma suna ƙulla ƙawance da gungun ƙungiyoyin Ecuador
  • Cikowar gidan yarin da rashin isassun masu tsaro sun sa yin sintiri a gidajen yarin na yin wahala.

A watan Fabrairu, fursunoni 79 ne suka mutu a wasu faɗace-faɗace da aka yi a gidajen yari huɗu, ɗaya daga cikinsu shi ne na Litoral Penitentiary.

Daya daga cikin matsalolin a cewar shugaban gidan yarin Garzón, shi ne fursunonin suna dauke da makamai.

Ya ce an yi fasa kwaurin makamai da dama cikin gidan yarin kuma ko binciken da da ƴan sanda ke yi kaɗan suke ganowa.

A baya Shugaba Lasso ya zargi karuwar rikicin kan cikowar gidan yarin. A watan Yuli ya ce tsarin gidan yarin Ecuador ya fi ƙarfin yawan mutanen cikinsa da kashi 30 cikin 100.

Akwai lokacin da ya sanar da shirin faɗaɗa abubuwa da sakin fursunonin da suka yi kananan laifuka don rage cunkoson.

Ya kuma ce za a sake samar da kuɗaɗe don sanya kyamarori a gidan yarin.

line