Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: Mene ne ya ke jan hankalin matasan Najeriya neman aiki a Turai?
Ana ci gaba da samun matasa 'yan Najeriya da ke tururuwar barin kasar zuwa Turai domin samun rayuwa mai kyau kamar yadda suke cewa.
A baya matasan da ba su da wata kwarewar rayuwa aka fi gani suna wannan tafiya mai cike da hadari, ta hanyar bin sahara ko jiragen kwale-kwale da suke ratsa teku.
Duk da cewa ana samun labaran mutuwar mutane da yawa saboda wahalar da ke tattare da wannan tafiya, kama daga nitsewa a ruwa da kuma wadanda ake yi wa kwace da wadanda ake kashewa, hakan ba ya kashe gwiwar masu burin wannan tafiya.
To amma a yau labarin ya wuce wannan babi, domin kuwa kwararru ne ke fita zuwa kasashen Turai domin samun rayuwa mai kyau a cewar mafiya yawansu.
Wannan kuwa na zuwa ne daidai lokacin da Burtaniya ta dauki likitoci 353 aiki a cikin kwana 100 kacal, wato daga ranar 10 ga watan Yuli 2021 zuwa 20 ga watan Satumbar 2021.
Ko da yake idan za mu kalli lamarin a tsawon shekara guda zamu ga adadin wadanda aka dauka aikin sun zarce yadda ake zato.
Shafin ƙungiyar manyan likitocin a Burtaniya ya nuna cewa likitoci 862 da suka samu cikakken horo Burtaniya ta dauka aiki daga ranar 24 ga watan Yuli 2020 zuwa 21 ga watan Satumbar 2021.
Bayan wadannan mutane da suke tafiya Burtaniya, akwai wadanda aka rinka rawaito cewa suna ta fafutukar samun aiki a Saudiyya kuma suma duka likitoci ne.
Rashin tsaro
Hadiza Sulaiman Datti wata kwararriyar likita ce da ke aiki a Burtaniya ta shaida wa BBC cewa akwai abubuwa da dama da ke da alaka da tafiyar kwararrun likitoci kasashen ketare musamman irin su Burtaniya.
"Rashin kayan aiki da za a rinka aikin ceto rayukan mutane na daga cikin abubuwan da suke kashe wa likitoci gwiwa a Najeriya, wani lokacin ana samun rashin jituwa tsakaninsu da gwamnatoci da kuma rashin biyan albashin da ya kamata.
"Tsangwama da suke yawan samu a lokutan da suke karbar horo, bugu da kari mafi damuwa shi ne rashin tsaro da ake fuskanta a yanzu," in ji likitar.
Likitar ta b ada misali da wasu likitoci da aka sace a Zaria da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya wadanda ta ce su na kan aikinsu aka dauke su saboda rashin tsaro.
Abin bai tsaya ba kan iya likitoci, har wadanda suka samu kwarewa a wasu fannonin rayuwa na guduwa zuwa kasashen da aka fi bukatarsu a kan lokaci.
Neman kyakyawar rayuwa
BBC ta tattauna da wani mazaunin Canada wanda ya karanci harkokin gudanar da kasuwanci (Business Admin) ya ce babu dalilin da zai sa ya zauna a Najeriya ya yi aiki idan aka dubi alfanun da ake samu a kasashe irin su Canada.
"Na samu aiki da wani kamfanin kwamfuta ne a Canada bayan kammala karatuna a Masar, gaskiya tun farko ba ni da kwarin gwiwar samun abin da nake so a Najeriya shi yasa ma ko ta kan kasar ban bi ba.
"Akwai alfanun kala uku da ake samu idan aka yi aiki a kasashen ketare, na farko tabbaci, kana da tabbas akan aikinka da kake yi.
"Na biyu kyakyawar albashi, wanda zai isheka da tafiyar da al'amuran iyalanka, a Najeriya babu wani aikin da za ka yi a gwamnatance kana samun irin albashina," in ji mazaunin Canada.
Ana samun rayuwa mai kyau a kasashen Turai in ji shi, ko da yake ba kawai 'yan Najeriya ba ne kadai ke tafiya Turai domin wannan aikin ba, in kana wajen za ka rinka ganin mutane iri-iri daga kasashe daban-daban.
Rashin kyawun yanayi
Wata malama a Jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Aisha Kuliya Gwarzo ta gabatar da wata maƙala kan irin wannan maudu'i a makon jiya lokacin da ake yaye sabbin likitoci a Jihar Kano.
Ta shaida wa BBC cewa dole wadannan likitoci su rinka barin kasashe masu tasowa, saboda yanayin da ake aiki a cikinsa cike yake da ƙunci.
"Rashin kayan aiki na daga cikin manyan abubuwan da suke konawa likitoci da yawa rai, ka karanci abu a littafi amma ba za ka iya dabbaka shi ba a aikace.
"An kashe tsarin kiwon lafiya a matakin farko, wannan ya sanya mai karamin ciwo kamar malaria ma sai ya tafi asibitin koyarwa wanda kuma ba daidai ba ne, kara aiki ne ga likitoci wadanda ya kamata su duba masu manyan matsaloli.
"A tsarin da WHO ta amince da shi, likita daya marasa lafiya 600 zai duba, amma a yau a Najeriya likita daya marasa lafiya 6,000 ya ke dubawa, ina likita zai sa kan shi. in ji farfesa Aisha.
Ta kara da cewa duka nauyin da ke kan wancan tsarin ya dawo kan manyan asibitoci.
Amma a ganinta da za a iya gyara tsarin da Najeriya ke kai a samar da kayan aiki, da sun daina ficewa daga kasarsu.
"Da za a iya samar da abubuwan da ke jan hankalinsu a Najeriya da ba makawa za su daina fita ko ina, suma suna son kasarsu ta ci gaba da sun tsaya sun bayar da tasu gudunmuwar a kasarsu."