Nigeria Jubilee Fellows Programme: Abin da ya kamata ku sani kan sabon shirin sama wa matasa aiki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shirin taimaka wa matasa wajen samun ayyukan yi da fito da fikirarsu da tsare-tsaren ci gaba.

Shirin, wanda a Turance ake kira 'Nigeria Jubilee Fellows Programme'. an soma rijistarsa ne a ranar Litinin, 6 ga watan Satumbar 2021.

A lokacin kaddamar da shirin, Shugaba Buhari ya ce wannan tsari zai rika taimaka wa matasa dubu 20 da suka kammala jami'a a gurabe daban-daban a kowacce shekara.

Me shirin ya kunsa?

An kaddamar da shirin ne a ranar 31 ga watan Agustan 2021. Shirin zai taimaka wa matasa samun aikin yi na hadin-gwiwa tsakanin gwamnatin Najeriya da Hukumar Raya Kasashe Ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP.

Annobar korona ta taka rawa wajen sake haifar da tsaiko da dakile damar matasa wajen samun aikin yi, don haka ana gani wannan shirin zai cike gibin da ya kara taggayara tattalin arzikin matasa.

Shirin zai ke haɗa ko sada matasan da suka gama karatu masu fiƙira ko basira da ayyukan da suka dace da kwarewarsu, da nuna musu hanyoyi ko ingantaccen horo. Hakan ba shi da nasaba da mutum da ke da kwarewar aiki.

Shirin ba zai yi la'akari ko zaɓi tsakanin waɗanda za su iya shiga tsarin ko kayyade ko bukatar wasu bayanai masu zurfi ko kwarewa ba kafin samun dama.

Sannan wani abu da shirin ke ba da dama shi ne yana zaƙulo mutane daga fannoni daban-daban ba tare da nuna fifiko kan wani karatu ko kwarewar mutum ko abin da ya karanta ba.

Shirin zai ratsa ko ina domin na 'yan Najeriya ne baki daya - daga arewa zuwa kudu da gabas da yammaci - da tabbatar da cewa kowanne matashi ya samu gurbi wajen gwada sa'arsa.

________________________________________

Su waye za su iya shiga shirin?

Matashin da ya kammala digiri daga shekara ta 2017 ke da damar shiga shirin, don haka dole ba a son mutumin da ya haura 30.

Kuma dole mutum ya kasance ya kammala aikin yi wa kasa hidima wato NYSC, kuma ba ya wani aikin.

Ana son mutum ya kasance mai sha'awar ci gaba da bijiro da tsare-tsare da kwarewa wajen mutunta lokaci da ilimin iya karatu a kowanne mataki.

Kungiyoyi da kamfanoni na iya shiga shirin, domin tayin jagoranci ko koyar da matasan da ke cikin shirin. Sai dai ana bukatar kamfanonin su kasance masu rajista da gwamnati.

________________________________________

Ya shiga shirin zai kasance?

Fitar da waɗanan ka'idoji da tsare-tsare ana ganin zai samawa matasa damar taka muhimmiyar rawa wajen haɓɓakar kamfanoni gwamnati da masu zaman kansu, yayin taimakawa wajen ci gaban Najeriya.

Masu ra'ayin shiga shirin za su aike da wasiƙar bayyana sha'awar shiga tsarin, da zayyana taimakon da za su bayar wajen taimakawa shirin ta hanyar karɓan wadanda za su samu horarwa.

Sannan komai zai kasance a intanet ne, kana daga cike bayanai da tsarin yada komai zai kasance, akwai kuma kamfani mai zaman kansa da za a bai wa damar aikin tantacewar.

Wadanda suka yi nasarar tsallake tantacewar za a musu wasu gwaje-gwaje da jarrabawa kafin a kai ga matakin karshe.

Sannan a karshe za a tsara yada aikin zai kasance ko horarwa tsakanin matashin da ya yi nasara da idan zai yi aiki.

________________________________________

A ranar 20 ga watan Oktoba 2021 za a kawo karshen rajista ga matasa masu sha'awar shiga shirin don a dama da su.