Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ku nemi aikin ɗan sanda a Najeriya
Hukumar 'yan sanda ta Najeriya (NPF) ta sanar da shirin soma daukan ma'aikata na shekara ta 2020, rukunin kurata, don haka tana gayyatar masu sha'awa su aike takardunsu.
Kakakin 'yan sandan, Farank Mba ya shaida cewa 'yan shekara 17 zuwa 25 ne suka cancanci aike takardunsu, kuma su tabbata suna da akalla kiredit biyar, ciki har da Ingilishi da Lissafi a jarabawar kammala sakanadare da ta hada da WASSCE ko NECO ko GCE ko kuma NABTEB.
Ya kuma kara da cewa za a bude gurbin daukar aiki ne na tsawon mako shida daga ranar 14 zuwa 23 ga watan Agusta, 2020, kuma kyauta ne cike takardar neman aikin.
Yadda za a cike aikin dan sanda na shekarar 2020
- Wajibi ne a cike gurbin wannan aikin a shafin intanet
- Dole ne sai kana da adireshin email da lambar shaidar dan kasa (NIN) kafin ka soma cike aikin
- Ka shiga wannan adireshin www.policerecruitment.gov.ng domin cike gurbin aikin
- Idan aka shiga adireshin sai a cike takardar aikin da ke intanet (ka tabbatar ka karanta abin da ka cike sosai kafin ka aike takardar)
- Ka tabbatar ka yi buga bayananka kamar yadda ya fito a kamfuta sannan ka aike shi email dinka kuma kar a manta a kwafa a kuma adana lambar da rajista ya nuna saboda amfanin gaba
- Ba za ka iya amfani da email guda ko lambar NIN a gurbi sama da guda ba
- Idan ka shiga mataki na gaba, za a bukaci ka gabatar da kwafin email din da aka tura maka kafin a shiga matakin daukar aikin.
Mutanen da suka cancanci neman wannan aikin
Wajibi ne duk mai neman wannan aiki ya kasance yana da sha'awar aikin dan sanda sannan ya cike wadanan sharudan;
- Dole ne ka zama dan asalin Najeriya da haihuwa sannan kana da lambar shaidar dan kasa wato (NIN)
- Dole kana da kiredit biyar a jarabawar kammala sakandare wanda bai zarce sau biyu ka zana ta ba na WASSCE ko GCE ko NECO ko NABTEB da credits a Ingilishi da Lissafi
- Dole sai shekarunka sun kai 17 zuwa 25
- Akwai bukatar kasancewa mai cikakken lafiya, da lafiyar kwakwala da kwari kuma dole tsayinka ya kai mita 1.67 ga namiji mace kuma ta kasance ta kai mita 1.64
- Fadin kirji akwai bukatar ya kai santimita 86 (inci 34) ko kafada (ga maza)
- Idan ke mace ce kuma kina son neman aikin, ki tabbata ba ki da ciki a lokacin daukar aikin
- Kuma sai ka tabbata babu badakalar kudi tattare da kai
- Sai ka yi buga takardar da ka cike a intanet, da na wanda ya tsaya maka, kuma a mika takardun a lokacin jarrabawa da tantacewa da kuma cibiyar daukar aikin.
Frank Mba, ya ce za su gayyaci wadanda aka tantace suka cike ka'idojin daukar aikin ta intanet domin tantacen su a cibiyoyin 'yansanda da ke jihohi, ciki har da Abuja daga ranar 24 ga watan Agusta 2020 zuwa 30 ga watan Agustan 2020.
Ga mutanen da basu da damar neman aikin
- Mutumin da bai iya jawabi ba
- Mutumin da ke da matsalar hakora ko haba wanda hakan ya sa cin abinci na masa wahala
- Mai matsala a guiwa
- Mai gwamiyar kafa
- Gwiwa mai lankwasa - gwiwar da ba ta mikewa koda mutum na tsaye
- Mutumin da ke da lalurar hannu
- Wanda ba ya gani sosai
- Rashin wani sashe na jiki.