Hakainde Hichilema: Yadda zaben sabon shugaban kasar Zambia ya karfafa gwuiwar 'yan adawar Afirka

Zambian opposition leader Hakainde Hichilema waves at his supporters after being released from prison after treason charge against him were dropped on August 16, 2017 in Lusaka

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Daga Dickens Olewe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Nan gaba a ranar Talata ne ake rantsar da dadadden jagoran adawa na kasar Zambia, Hakainde Hichilema, lamarin da ya karfafa gwuiwar takwarorinsa na sauran kasashen Afirka cewa watarana su ma za su iya shawo kan duk wata matsalar danniyar da ake yi musu a kasashensu, kana su kasance masu rike da mulki.

A tsawon shekarun da ya shafe yana harkar siyasa da ya rika faduwa zabuka da ya yi ta yunkurin tsayawa har sau biyar don zama shugaban kasa, an gallaza wa Mista Hichilema, da shaka masa hayaki mai saka kwalla, har ma da tsare shi kan karya dokar tuki a shekarar 2017 da aka bayyana cewa cin amanar kasa ne bayan da kwambar motocinsa ta ki bai wa tawagar shugaban kasa mai barin gado Edgar Lungu hanyar wucewa.

Amma kuma, a wani abu mai kama da juyin waina ( na irin sa'ar da ya taka) da ba a taba tsammani ba, mutumin da aka taba ayyanawa a matsayin makiyin kasa ne za a rantsar a matsayin shugaban kasar Zambia na bakwai bayan da ya kayar da Mista Lungu a zaben da aka gudanar ranar 12 ga watan Agusta.

"Akwai karfafa gwuiwa matuka," in ji jagoran adawa na kasar Tanzania Tundu Lissu wanda ya tsira daga yunkurin hallaka shi da aka yi a shekarar 2017 bayan harbinsa da aka yi har sau 16 da mutanen da ya yi amanna gwamnati ce ta saka su.

"'Yan kasar Zambia sun nuna mana cewa zai iya kasancewa, duk kuwa da halin da suka yi kokarin saka mu ciki, duk da irin wahalhalun da muka sha, in ji shi.

A bara ne Mista Lissu ya fadi zabe bayan da shugaba John Magufuli ya samu galaba, wanda ya yi zargin an tafka magudi.

Daga bisani ya tsere ya bar kasar bayan da jami'an tsaro suka fara shirin kama shi.

Tanzania Opposition lawmaker Tundu Lissu waves from his wheelchair after giving a press conference surrounded by members of his family and supporters on January 5, 2018 at a hospital in the Kenyan capital, Nairob

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tundu Lissu ya yi jinya a Kenya bayan an yi yunkurin halaka shi a 2017

An kama wasu abokan siyasarsa a jam'iyar Chadema, da suka hada da Freeman Mbowe na kankanen lokaci.

A watan Mayu ne aka tuhumi Mista Mbowe kan aikata laifukan da suka shafi ta'addanci. Magoya bayansa sun bayyana cewa yana fuskantar ''zalunci na siyasa" kan fafutikar da yake yi kan sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Kamar yadda dan adawar siyasar kasar Tanzania Zitto Kabwe ya bayyana, sabon kundin tsarin mulki kadai ne wanda zai bai wa hukumar zaben kasar 'yancin cin gashin kai zai tabbatar da ganin 'yan adawa sun samu dama a zabe mai zuwa.

"Da alamu a kasar Zambia, hukumomin zabe da tafarkin dimokaradiyya sun fi daukar matakai kan abubuwan da suka shafi jama'a fiye da kasashen Afirka da dama.

"Kasancewa sojoji, da 'yan sanda, da jami'an tsaron farin kaya, da hukumar zabe za su fi bai wa abubuwan da jama'a suke so fifiko, sako ne mai karfi aka aikewa da nahiyar Afirka,'' a cewarsa.

'Babu bin gajeriyar hanya wajen cin zabe'

Tasirin wannan sako ya bazu zuwa nisan duniya, musamman kasar Zimbabwe makwabciyar kasar daga bangaren kudu, inda ya haifar da zazzafar takun-saka tsakanin babban dan adawar siyasa Nelson Chamisa, da 'yan jam'iya mai mulki ta Zanu-PF, wacce ke kan mulki tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1980.

"Zimbabwe nan gaba kadan ke ce,'' jagoran 'yan adawa ya wallafa haka a shafinsa na Twitter, lokacin da yake taya Mista Hichilema murna.

Shugaba Emmerson Mnagangwa ya mayar da martani: "Abin da ya faru a Zambia ba zai taba faruwa ba a nan."

Mai magana da yawunsa har ya dan magantu da cewa sojoji ba za su taba barin mulki ya koma hannun 'yan adawa ba.

Jami'an tsarom Zimbabwe sun yi kaurin suna wajen cin zarafin 'yan adawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jami'an tsarom Zimbabwe sun yi kaurin suna wajen cin zarafin 'yan adawa

Amma kuma, mai magana da yawun jam'iyar MDC-Alliance ta Mis Chamisa Fadzayi Mahere, ya shaida wa BBC cewa nasarar da Mista Hichilema ya samu ta nuna cewa za a iya samun nasara a fafutika kan dimokaradiyya, kuma mutane za su iya hada kan su wajen kawar da mulkin danniya''.

Mis Mahere ta kara da cewa "babu batun bin gajeriyar hanya wajen cin zabe".

  • Ta kuma ce ya kamata 'yan jam'iyar adawar kasar Zimbabwe su yi koyi da jam'iyar Mista Hichilema ta United Party for National Development (UPND) ta hanyar:
  • Yi wa sabbin masu kada kuri'a rajista
  • Saka matasa cikin harkokinsu
  • Kare kuri'u daga aikata magudin zabe
  • Da kuma, mafi muhimmanci, mayar da hankali kan manyan matsaloli da mutane suke so a shawo kai - farfado da tattalin arzikin da ya durkushe, da samar da ayyukan yi ga matasa da dama da ke zaman kashe wando, da kuma kawo karshen dabi'ar rashin adalci a gwamnati.

Sako ne wanda Mmusi Maimane, tsohon jagoran 'yan adawa na Afirka ta Kudu kuma abokin Mista Hichilema, shi ma yake kokarin jaddadawa.

Ya kuma yi kira a kan jam'iyar MDC-Alliance, yana mai cewa : "Zimbabwe, an samar da abin koyi."

"Mutanen kasar Zambia sun nuna kin jinin talauci da cin hanci da rashawa. Mutanen Zambia sun nuna kin jinin girman kai da lalaci. Sun zabi makomarsu da ta dace a yi wa aiki tukuru,'' Mista Maimane ya kara a cikin sakonsa.

'Shugabannin kasa bayin kasa ne'

A kasar Kenya, magoya bayan tsohon jagoran siyasa Raila Odinga su ma sun nuna farin cikinsa game da nasarar da Mista Hichilema ya samu, a yayin da dan siyasar mai shekaru 76 ke shirin karbar shugabancin kasar, bayan yunkurin tsayawa karo na biyar a shekarar 2021.

Mista Odinga ya bayyana cewa sakamakon zaben na kasar Zambia "zai ankarar da sauran 'yan kasashen Afirka cewa babu wani abu da zai gagara."

Mista Odinga na shirin halartar taraon rantsarwar tare da jaogororin adawa daga sauran kasashen Afirka, a wata alama da ta nuna cewa Mista Hichilema bai yi niyyar yin watsi da su ba, yanzu da yake zai kama mulki.

Matasan Zambia sun goyi bayan Hakainde Hichilema a zaben da ya gabata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Matasan Zambia sun goyi bayan Hakainde Hichilema a zaben da ya gabata

Sanin yadda wannan zabe ya samu tagomashi a daukacin nahiyar, mai magana da yawun jam'iyar UPND Cornelius Mweetwa ya shaida wa BBC cewa babu wani "asirin boye" game da samun nasarar.

"Wannan nasara ce ga 'yan kasar Zambia. Sun fito kwan su da kwarkwata sun kada mana kuri'u saboda suna bukatar a shawo kan cin hanci da rashawa, da matsalar rashin aikin yi, da kawo karshen tashe-tashen hankula na siyasa da kuma mulkin kama-karya," in ji Mista Mweetwa.

Masu sa ido su ma sun yaba wa Mista Hichilema, mai shekaru 59, kan yadda saka matasa cikin al'amuransa, muhimmiyar mazabar da ya yi wa lakabi da Bally - salon sunan da yake nufi mahaifi - saboda mayar da hankalinsa kan abubuwa da suka danganci hakan.

"Mu ba iyayen gidan mutane ba ne, mu bayinsu ne," Mista Hichilema ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe.

Hakan ya haifar da martani a fadin nahiyar.

Amma kuma, wasu sun yi gargadin cewa sun sha ganin yadda sauran shugabannin suka rika nuna cewa su masu fafutikar 'yancin jama'a ne, amma daga bisani su sauya zuwa masu gallazawa mutane da zarar sun hau kan karagar mulki.

'Yan kasar Zambia da sauran jama'a a fadin Afirka za su zura ido sosai su ga abin da zai faru.

line