Hakainde Hichilema: Mai 'kiwon shanun' da ya zama shugaban kasar Zambia

Hichilema

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tun shekarar 2006 Hichilema yake tsayawa takarar zaɓe yana faɗuwa
    • Marubuci, Daga Kennedy Gondwe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lusaka
  • Lokacin karatu: Minti 4

Batu ne Hakainde Hichilema, wanda sai bayan karo na shida ya yi nasarar zama shugaban Zambia, bayan ya sha kaye sau biyar.

Mista Hichilema ya kayar da babban abokin hamayyarsa, shugaba mai barin-gado Edgar Lungu, da yawan kuri'u sama da miliyan daya.

To amma shin wane ne sabon shugaban? Kuma me ya sa sai bayan shekaru yana jarraba sa'arsa sannan ya yi nasara?

Short presentational grey line

Mista Hichilema, mai shekara 59, ya bayyana kansa a matsayin talaka, mai kiwon shanu, wanda sai ya je ya kai shanun iyayensa kiwo ya dawo sannan ya tafi makaranta a lokacin yana matashi, kafin daga bisani ya zamo daya daga cikin attajiran Zambia.

Yawanci ana yi wa zababben shugaban kuma jagoran jam'iyyar United Party for National Development (UPND)lakabi da HH. An haife shi ne a matsayin talaka kafin ya yi sa'a ya samu tallafin karatu a Jami'ar Zambia, kuma daga bisani ya samu har ya yi digiri na biyu a Jami'ar Birmingham a Burtaniya.

Daga nan kuma ya samu bunkasar arziki a harkar kudade da gidaje da kiwo da harkar lafiya da kuma harkar yawon bude idanu.

Ya yi amfani da irin yadda rayuwarsa ta kasance daga dan talaka ya zama hamshakin attajiri, wajen shawo kan masu zabe.

Ya gaya wa masu zabe cewa suna bukatar dan kasuwar da ya yi nasara a harkokin kasuwancinsa, da zai san yadda zai tafiyar da kasar mai arzikin jan-karfe, wadda ke fama da rashin aikin yi sosai.

Haka kuma ya yi amafani da asalinsa na dan talakawa manoma wajen jan hankalin manoma, yana mai cewa zai iya raya harkar noma a kasar har ta zama mai ciyar da yankin.

Amma ana ganin kokarin Mista Hichilema na jan matasan masu zabe a jika shi ne babban abin da ya kai shi ga nasara.

Sama da rabin masu zabe miliyan bakwai na Zambia 'yan kasa da shekara 35 ne. Kuma kusan duk daya daga cikin biayr ba shi da aikin yi.

Jam'iyya mai mulki Patriotic Front (PF) ta ci zabe a 2011 a bisa alkawarin rage haraji, da samar da karin kudade ga jama'a, da kuma ayyuka.To sai dai dukkanin wadannan alkawura kusan ba su tabbata ba ga yawancin matasa, wannan ya sa miliyoyinsu suka karkata ga Mista Hichilema.

Daya daga cikin hanyoyin da ya bio na shawo kan jama'a ita ce ta shafukan intanet. Wannan ne zabe na farko da Mista Hichilema ya gawada amfani da irin su Facebook da Twitter wajen yakin neman zabe.

A shekarar da ta gabata ya fitar da wani hoton bidiyo mai taken: Labarin kwararru biyu ("The tale of two professionals...",) bidiyon da ke nuna Mista Hichilema a matsayin natsattse dan kasuwa mai kaifin basira, da kuma Mista Lungu a matsayin wanda ya kashe duk kudinsa a mashaya da gidajen rawa. ''Wane ne daga cikin wadannan ya fi?'' Ake tambaya a bidiyon.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

Mr Hichilema yana yawan yin takaici a shafukan sada zumunta kan batutuwan da ke tashe musamman ma ƙwallon ƙafa - wadda hanya ce mafi sauƙi wajen masun masoya da za su goya masa baya a zaɓe.

A wasu lokutan cikin raha ya kan tsokani magoyan Manchester United da Arsenal idan aka ci ƙungiyoyinsu.

Ya kuma taya ƴan wasan Zambiyan murna, waɗanda aka saye su da tsada a ƙungiyoyin Turai da suka haɗa da Patson Daka, wanda kwanan nan ya koma Leicester City, da Fashion Sakala, wanda ya ya koma ƙungiyar Rangers ta Scotland.

Ya kan ma yi tsokaci kan wasannin sada zumunci inda yake nuna sha'awarsa kan sana'ar tasu

Mr Hichilema na yawan amfani da wasu kalmomi a shafukan sada zumunta kamar su "bally", wata kalma ta girmamawa wajen kiran wani a matsayin uba.

An yi ta amfani da maudu'ai kamar irin su #BallyWillFixIt a ƙoƙarin yin yaren da mutane ke so a kasuwanni da mashayu, ba kawai sai ƴan kasuwa ba.

Hakan kuma ya yi aiki.

Dubban magoya bayan Mr Hichilema sun kwararo kan titunan Lusaka bayan nasarar da ya samu, suna sowa suna cewa "mu je zuwa dai Bally."

Bayanan bidiyo, Mutane sun bazama kan titi don murnar nasarar cin zaben Hakainde Hichilema'

Mr Hichilema ya nuna jajircewa a lamurran siyasarsa. Duk da faduwa zabe da ya yi sau biyar, yana yawan tuna wa mutane cewa sau 15 aka kama shi tun sanda ya fara siyasa.

A shekarar 2016, an tuhume shi da laifin cin amanar ƙasa kan zargin ƙin bai wa tawagar shugaban ƙasa hanya. Ya shafe wata huɗu a gidan yari mai cike da tsaro kafin daga baya a soke tuhumar.

A jawabinsa na murna, zaɓɓɓen shugaban ƙasar Hichilema ya gayyaci abokan hamayyarsa don su zo a haɗa kai a zauna lafiya.

"Kar ku damu, ba abin da zai faru, ba za a muzguna muku ko fesa muku hayaƙi mai sa hawaye ba," a cewar Hichilema, wanda aka sha kai masa hari a abin da ya kira ƙoƙarin rufe bakinsa da tsoratarsa da shi a matsayinsa na shugaban ƴan hamayya.

Bayan da ya samu mulkin, ba makawa Mr Hichilema zai yi murna. Sai dai yana buƙatar fara aiki da gaggawa don daidaita al'amura a ƙasar da ke fuskantar matsaloli da dama.

Baya ga matsalar rashin aikin yi da ta dabaibaye ƙasar, tsadar rayuwa ma kullum ƙara ƙamari take yi.

A karon farko tun shekarar 1998, Zambiya ta faɗa cikin matsin tattalin arziki a bara a yayin da annobar cutar korona ta yaɗu a faɗin ƙasar.

Batun kuɗaɗen da ƙasashen waje ke bin ƙasar bashi kuwa, an ƙiyasta cewa ya fi dala biliyan 12.

Hakan na nufin gwamnati tana amfani da a ƙalla kashi 30 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta kan biyan kuɗin ruwa, a cewar wani kamfani S&P.

A bara, Zambiya ta gaza biyan kuɗin ruwanta, abin da ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta gaza biyan bashi a lokacin annobar cutar korona. Sannan ta fuskantar matsaloli wajen biyan sauran basussuka.

Farin jinin Mr Hichilema zai ragu idan har bai fara warware wasu daga cikin matsalolin nan da gaggawa ba.