Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Yan kasar Kenya sun kai karar sojojin Birtaniya kan gobara a gandun daji
- Marubuci, Daga Emmanuel Onyango
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lolldaiga conservancy
Wata mota ta buge Linus Murangiri inda ya mutu a yayin da yake ruguguwar kai daukin kashe gobara a gandun dajin kasar Kenya, wurin da ya karbi bakuncin shirin atisayen sojojin Birtaniya.
Duk da yada labaran da aka yi ta yi game da gobarar a watan Mayu, ba a kula da batun mutuwarsa ba.
Ko da yake ba a fito an nuna kai-tsaye cewa sojojin Birtaniya ne sanadiyyar mutuwar Mista Murangi ba, yanzu mai dakinsa ta shaida wa BBC cewa tana bukatar a gaggauta bincike kan yadda mijinta ya mutu da kuma musabbabin gobarar, kana a sanar da jama'a sakamakon binciken.
Gobarar, wacce aka dora alhakinta a kan atisayen sojojin, ta lalata kusan kadada 12,000 na filin a gandun dajin Lolldaiga mai zaman kansa a tsakiyar kasar Kenya, inda namun daji irinsu giwaye, da kuraye, da dila, da zakuna, da bauna da kuma nau'in jakin dawa na Grevy ke rayuwa.
An zargi wani sojan Birtaniya da rubutawa a shafinsa na Snapchat cewa: "Watanni biyu a Kenya, kuma kwanaki takwas suka rage mana. Abu ya yi kyau, mun haddasa gobara, da kashe giwa, kuma ban ji dadin game da haka ba amma idan ka shiga gari ka ga mutane da jela, to kai ma ka ciri zangarniya ka dasa.''
Ba a sanar da musabbabin abkuwar gobarar a hukumance ba, amma kuma batun yana gaban shari'ar da ta shafi muhalli wacce kungiyoyin masu yin matsin lamba game da doka, da kuma mazauna yankin kusan 1,000 suka gabatar.
Mazauna yankin sun ce girman barnar da gobarar dajin ta haddasa ba zai misaltu ba - sun bayyana cewa ta shafe akalla kwanaki hudu tana ci yayin da hayaki mai kauri ya turnuke sararin samaniya, wanda ya sa ba zai yiwu mutum ya motsa zuwa nan da can ba.
Sun ce hayakin na kaurin gashin nama, duk da cewa Hukumar Raya Gandun Dajin kasar Kenya ta musanta ikirarin cewa giwaye biyar da karamin dansu sun hallaka.
Wasu dattawa sun ce sun samu matsalar konewar idanu, a yayin da wani mai wa'azi a yankin Duncan Kariuki, mai shekaru 43, ya ce sai da aka kwantar da dansa mai shekara daya a asibiti saboda ya shaki hayaki.
Mai magana da yawun Ofishin Huddar Jakadancin Birtaniya ya ce sojojin sun gudanar da binciken cikin gida kan musabbabin tashin gobarar amma kuma saboda wannan ya zama batu ne da ke gaban kotu, bai dace ya kara yin wata magana ba.
Gandun dajin Lolldaiga - mai kusan kadada 49,000 na da tuddan dazukan da kuma ke kewaye da manyan duwatsu a kasar Kenya - wani bangare ne na kwarin Laikipia, inda Turawan Birtaniya suka kwace dubban daruruwan kadada a lokacin mulkin mallaka, wanda ya haddasa rikice-rikice kan filaye wanda har yanzu ke ci gaba da faruwa.
Nisan kilomita 70 ko (mil 45) ne daga gandun dajin Lewa , inda Yarima William ya nemi izinin auren Kate Middleton cikin watan Nuwambar shekarar 2010.
Kilomita kadan daga kudanci kuma akwai sabon barikin sojoji na Nyati, ginin da ya lashe fam miliyan saba'in, da kuma ake kira Cibiyar Horar da Sojojin Birtaniya na kasar Kenya (Batuk), wanda ke karbar bakuncin dakarun Birtaniya a ko wace shekara don gudanar da gagarumin atisaye a gandun dajin Lolldaiga, wanda ke samar da muhalli da kuma yanayi mai tsanani da ya dace da ayyukan horon soji.
An shafe shekaru goma ana amfani da wurin, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Akwai kuma atisayen hadin gwuiwa tare da sojojin kasar Kenya.
Amma kuma taimako daga yankin na raguwa - akalla daga cikin mazauna yankin da ke kusa da suka tattauna da BBC. Sun bayyana cewa sun saba ta jin karar bindigogi, da ababen fashewa da kuma na jiragen sama da ke yawo kasa-kasa a kusa da gidajensu tun daga safe har dare.
Mutane 994 da suka rattaba hannu a kan takardar karar na da koke-koke da dama:
• An karya dokar 'yancinsu na samun tsaftatacce da lafiyayyen muhalli.
• An kaucewa bin tsarin kariya na atisayen soji - da suka hada da yin watsi da tsarin amfani da kuma kulawa da alkinta muhalli, da kare lafiyar mazauna yankin da ke kusa - an karya doka.
• Namun dajin da ke tsere wa makaman da ake harbawa a gandun dajin na abka wa gidajensu kana suna lalata musu amfanin gona.
• Suna bukatar sojojin Birtaniya da kuma masu kula da gandun dajin su dauki alhakin biyan diyyar irin barnar da hakan ta haifar wa da yankin.
Al'ummar yankin sun yi aniyar amfani da sakamakon rahoton barnar da suka gabatar don kara jaddada bukatunsu.
"Rayuwa kusa da sansanonin horarwar akwai matukar wahala, musamman saboda namun dajin da ke lalata mana amfanin gona suna kai hari a kan 'yayanmu masu zuwa mamakaranta.
Adadin namun dajin da ke gararanba a cikin kauyuka sun karu matuka saboda gobarar gandun dajin,'' in ji Mista Kariuki, daya daga cikin masu kai karar.
Macharia Mwangi na Cibiyar Gyara Halinka da Daukar Matakan Rigakafi ta Afirka (ACCPA), da ke cikin wadanda suka gabatar da karar, y ace hich is also part of the lawsuit, ya ce ba ya adawa da zaman sojojin Birtaniya a kasar ta Kenya, kuma ba yana so a dakatar da horon ba ne baki daya.
"Abin da muke adawa a kai shi ne cigaba da lalata mana muhalli da zamanmu da dabbobinmu, na kusan mutane 5,000."
A cikin watan Yuni, lauyoyin sojjojin Birtaniya sun bukaci koton muhallin da ta yi watsi da karar, tare da ikirarin cewa kotunan Kenya ba su da hurumi a kan wannan batu.
Nan gaba a cikin wannan watan ne kotun za ta yanke hukunci a kan bukatar.
Har yanzu Karen Gatwiri ba ta rattaba hannu kan takardar koken ba, amma tana ta fadi-tashi tun bayan mutuwar mijinta a lokacin gobarar.
BBC ta gano ta ita da 'yayanta maza biyu, masu shekaru hudu da kuma biyu a wani karamin gari mai nisan tafiyar tukin sa'a daya daga gandun dajin.
Suna zaune a wasu dakunan katako uku na haya wanda aka zayage cikinsu da tamfol don kariya daga sanyi. Da mayar da daya daga cikin dakunan zuwa kantin sayar da kayan amfanin yau da kullum na gida, amma babu ciniki sosai.
Ba su yi ban-kwana da mijinta ba, ta ce, kuma babu wani abu da ta ji daga mahukunta da masu gandun dajin game da mutuwar mijinta.
Abokan aikin mijinta sun shaida mata cewa mijinta ya mutu ne bayan da ya fado daga mota inda wata motar da bi a kansa.
Bayanai daga dakin ajiyar gawawwaki a yankin sun nuna cewa ya mutu ne nan take sakamakon raunin da ya samu a kai.
A karon farko hukumar gandun dajin ta yi bayani game da mutuwar, amma ta ce ba a amince ta sanar a bainar jama'a ba, kamar yadda ke faruwa ga kamfanoni masu zaman kansu.
"Ban ji dadi ba da ba a kula da batun mutuwarsa ba saboda ina da duka takardu (na mutuwarsa da na amince binnewa) don nuna cewa ya mutu. Ba su mutunta ni ba a matsayina na uwar 'ya'yansa kan rashin bayyana min yadda ya mutu,'' Miss Gatwiri ta ce, cikin rawar murya.
"Ina son a san gaskiya - ya kamata a gudanar da bincike, kuma a yi mini adalci ni da 'ya'yana. Saboda gaskiyar ita ce, ya mutu a ma'aikatar gandun dajin kuma a (lokacin gobarar)."
Ofishin Huddar Jakadancin Birtaniya a birnin Nairobi ya shaida wa BBC cewa "muna bakin cikin samun labarin mutuwar daya daga cikin ma'aikatan hukumar gandun dajin Lolldaiga" kana cewa hukumar na tuntubar iyalan'", tare da yin duk wasu tsare-tsaren da suka dace.
Linus ma'aikacin hukumar ne mai nagarta, kuma muna taya iyalansa alhini, in ji babban jami'an hukumar Harry Hanegraaf a wata sanarwa.
Amma kuma, Misis Gatwiri ta ce har yanzu ba ta samu wani kudi daga hukumar gandun dajin ba.
"Ba ma iya samun abinci kamar yadda muka saba, ba na iya biya wa babban dana kudin makaranta, ba na iya biyan kudin haya - dole sai ina rokon 'yan uwana. Idan da Linus na raye da ba zan rika wahala irin wannan ba."