Tsofaffin matan da masu gadi suka yi wa fyade a gona a Kenya sun fadi halin da suka shiga

    • Marubuci, Daga Vivienne Nunis
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa correspondent, Nairobi

Wasu mata biyu wadanda suka ce masu gadi sun yi musu fyade a gonar Kakuzi da ke kasar Kenya sun bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Sun yi zargin ne a daidai lokacin da kamfanin da ke da gonar ya ce zai shigar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasar kara a kotu kan abin da ya kira zarge-zargen karya da suka yi masa game da cin zarafi.

Masu suka sun ce kamfanin da ke kula da Kakuzi zai shigar da karar ce da zummar sake samun kwantaragin da wani babban shago na Birtaniya ya daina ba ta saboda zarge-zargen cin zarafin mata.

Kamfanin ya shaida wa BBC cewa dole a gudanar da bincike kan sabbin zarge-zargen kuma ba zai amince da masu aikata ba daidai ba.

Mudhikwa Musau, mai shekara 88, tanazaune a wani kauye da ba shi da nisa daga da gonar ta Kakuzi da ke tsakiyar Kenya.

Ta ce a shekarar 2009 masu gadin gonar sun yi mata fyade da karfin tsiya. Da take jawabi da harshensu na Kamba, ta bayyana yadda ta yi zargi an yi mata fyaden.

"Ya kama ni kamar haka kuma ya kama ni a nan. An zagaya da ni. Ya tashi tsaye ya tsaya a kaina. Ya taka muyana. Ya rike muyana sanna ya juya si. Ya rufe mini baki a yayin da nake ihu."

Mudhikwa Musau ta ce ya je wurin 'yan sanda ta kai kara kan abin da aka yi mata, sai dai ba ta sake jin an ce komai a kan batun ba.

Da suke mayar da martani kan batun, masu gonar Kakuzi sun fito da wasu takardun kotu da ke nuna cewa an hukunta daya daga cikin ma'aikatansu kan lamarin amma an wanke shi daga zargin yi mata fyade.

Kazalika ita ma Marium Wanja mai shekara sittin da biyar ta bayyana yadda aka yi mata fyade a gonar. Ta ce ta haifi 'ya'ya biyu sakamakon lalata da masu gadin gonar Kakuzi suka yi da ita a shekarun 1990.

"Masu gadin gonar Kakuzi sun yi mini fyade kuma hakan ya sa aurena ya mutu," a cewarta.

"Karo na biyu da aka yi mini fyade, [mijina] ya ce: 'Yanzu na gaji. Na bar ki ki koma wurin masu gadin Kakuzi. Je ki zauna tare da masu gadin.'"

Cikin fuye da shekaru 30, mutanen yankin sun yi zarge-zarge da dama a kan masu gadin Kakuzi. Zarge-zargen sun hada da fyade, cin zarafi da kuma kisa.

A shekarar da ta wuce manyan kantunan sayar da kaya na Birtaniya sun yanke shawarar daukar mataki. Tesco, Sainsbury's da kuma Lidl sun daina sayen amfanin gonar Kakuzi, sannan suka soke sayen dukkan kayan da suka yi odar saya.

Mata masu gadi

Zarge-zargen take hakkin dan adam din sun ja hankalin manyan kantunan sayar da kayan abinci na Birtaniya ne lokacin da wata kungiyar lauyoyi ta kasar mai suna Leigh Day ta shigar da kara a wata Babbar Kotun Birtaniya a madadin 'yan Kenya 79.

Cikin wadanda suka wakilta har da iyayen wani matashi da ake zargi da satar fiya. An yi zargin cewa masu gadin Kakuzi sun lakada masa duka har sai da ya mutu.

David Ndambuki, wani tsohon ma'aikacin gonar da ya yi fafutikar ganin an kyautata tsarin aiki a kamfanin ya ce tuntuni ya kamata a bi doka yana mai cewa: "A ra'ayina tuntuni ya kamata a tsare mutumin da ya aikata laifin sanna a gurfanar da shi a gaban kotu."

Kamfanin Camellia da ke Birtaniya wanda ya mallaki Kakuzi ya warware matsalar wanna kara a watan Fabrairu, inda ya amince ya biya £4.6m ($6.5m), ba tare da amsa laifi a kan zarge-zargen ba.

Kakuzi ya yi alkawarin samar da wata hanya ta dadadawa mutanen kauyukan, wadda ta hada da gina musu hanyoyi da daukar mata masu gadi aiki.

Kazalika kamfanin ya bai wa wani kamfani mai zaman kansa aiki kan sanya ido game da kare hakkin dan adam a gonar.

Kamfanin mai zaman kansa, mai suna Ibis, ya shaida wa BBC cewa a halin yanzu yana tattara bayanai kan gonar da halin da ma'aikatan ke ciki.

Sai dai a yayin da Kakuzi ke daukar matakin inganta tsare-tsarensa na kare hakkin wadanda ake zargi da ci wa zarafi, a gefe guda kuma yana shirin gurfanar da hukumar kare hakkin dan adam ta Kenya Human Rights Commission da kuma wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Ndula Resource Centre.

Kakuzi ya ce kungiyoyin biyu sun zarge shi da laifin cin zarafi a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a lokacin da aka cimma matsaya a Birtaniya.

Da yake amsa tambayoyin BBC kan dalilan da suka sanya Kakuzi ya yanke shawarar gurfanar da kungiyoyina gaban kotunan Kenya bayan uwar kamfanin ta Birtaniya ta sawo kan batun, sai ya ce: "Muna neman kotu ta bayar da umarnin fito da shaidu a kan batun sannan a hukunta wadanda suke da hannu a kan lamarin."

Manyan kantunan Birtaniya

Haka kuma da yake mayar da martani kan zargin da tsofaffin matan biyu da suka yi hira da BBC suka yi, Kakuzi ya kara da cewa: "Wadannan manyan zarge-zarge ne kuma kamar ko wadanne zarge-zarge, dole mu dauke su da muhimmancin da ya dace. Dole a gabatar da shaidu ga hukumomin da ke gudanar da bincike na Kenya.

"Tabbas Kakuzi zai bayar da hadin kai kan wanna batu - ba ma amincewa da masu aikata laifuka a kamfaninmu ko kuma al'ummarmu."

Kakuzi, wandake noma gyade da danginta da tuffa da timba da kuma kiwon dabbobi tare da fiya, ya ce yana sa san nan ba da jimawa ba kamfanonin Turai za su ci gaba da sayen kaya daga wurinsa.

A yayin da manyan kantunan Birtaniya suka ce ba su koma sayen kaya daga gonar ta Kakuzi, Tesco, Sainsbury's da Lidl sun shaida wa BBC cewa suna sanya ido kan kamfanin da ke tafiyar da gonar domin ganin ko za su inganta tsarinsu.

Mary Kambo daga kungiyar kare hakkin dan adam ta Kenya Human Rights Commission ta ce, "Muna kira ga 'yan kasuwar Birtaniya... ba ma so su yi aikin gaggawa amma muna so su yi amfani da damar su a matsayin kasuwa."

Da take bayani kan karar da Kakuzi zai kai su, ta ce: "[A fili] take cewa suna son sake jan hankalin kasuwannin Birtaniya, amma ba na tsammanin wannan ce hanyar da ta dace."