Hichem Mechichi: An sauke Firaiministan Tunisia daga mulki saboda zanga-zanga kan cutar korona

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Tunisia, Kais Saied, ya kori Firaiministansa Hichem Mechichi, tare da dakatar da majalisar dokoki bayan zanga-zangar adawa da yadda gwamnati ke nuna halin ko-in-kula game da annobar korona.
Da yake jawabi a wani taron gaggawa na kwamandojin soji, Shugaba Saied ya ce ya dauki matakin ne domin ceto kasar daga rikicin da take neman fadawa.
Ya gabatar da jawabin ne a talabijin din kasar, bayan taron gaggawa na tsaro.
Shugaba Saied ya ce zai rike iko tare da taimakon sabon Firaminista, yana mai cewa ya yi hakan ne domin kwantar da hankali a kasar.
Sai dai matakin nasa bai samu karbuwa ba a wurin 'yan hamayya da suka bayyana hakan a matsayin juyin mulki.
Shugaban Majalisar Dokokin Rached Ghannouchi ya zargi shugaban da juyin mulki a kan juyin juya hali da kuma tsarin mulkin kasar.
Amma jama'a sun barke da murna bayan samun labarin cire Firaiministan a cikin dare, har shi kansa shugaban kasar ya bi taron jama'a da ke burede a babban birnin kasar Tunis.
Dubban jama'a dai daman suna ta zanga-zangar kin jinin gwamantin jam'iyya mai mulki, suna kira da a rushe majalisar dokoki.
Yanzu dai jamian tsaro sun datse majalisar da titunan da ke kai wa ga dandalin zanga-zangar da ta kai ga juyin juya halin kasar ta Tunisia a 2011
'Yan sanda sun rika harba hayaki mai sa hawaye ga masu zanga-zanga, sun kuma kama mutane da yawa, inda ake samun dauki ba dadi a garuruwa da dama.
Masu zanga-zanga sun far wa ofisoshin jam'iyya mai mulki ta Ennahdha suna ta farfasa kayayyaki suka cinna wuta a wata karamar hedikwatarta da ke Touzeur.

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar ta yi tir da harin wanda ta dora alhakinsa a kan wadanda ta kira gungun miyagu da ke neman haddasa tashin hankali da barna.
Shugaba Saied ya lashi takobin daukar mataki da karfin soji a kan duk wata tarzoma.
Yana mai cewa kundin tsarin mulki y aba shi damar dakatar da majalisar dokoki idan kasar na fuskantar wani hadari.
Shugaban majalisar dokokin da aka rushe da ya bayyana matakin a matsayin juyin mulki ya ce, su har yanzu suna dauka majalisar na nan
Kuma magoya bayan jam'iyya mai mulki ta Ennahda da jama'ar Tunisia za su kare juyin juya halin.
Shekara goma da ta wuce juyin juya halin Tunisiyar ya bude kofar kafa dumokuradiyya da kuma haifar da guguwar juyin juya hali a kasashen Larabawa.
Amma kuma fatan da ake da shin a cewa juyin zai samar da ayyukan yi da walwala ya dusashe ba tare da ganin sauyin ba.
Kasar na ta fama da matsalar tattalin arziki da kuma annobar korona mafi tsanani a nahiyar Afirka.
Matakin Firaiminista na cire ministan lafiya a makon da ya gabata bai kwantar da hankalin 'yan kasar ba.











