Tsohon malamin makaranta ya zama sabon shugaban Tunisia

Presidential candidate Kais Saied speaks during a news conference after the announcement of the results in the first round of Tunisia"s presidential election in Tunis, Tunisia September 17, 2019.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mista Kais Saied ya ce matarsa ba za ta rike mukami na siyasa ba idan ya zama shugaban kasa

Alkaluman da aka tattara zuwa yanzu sun tabbatar cewa tsohon malamin makaranta Kais Saied ne ya lashe zaben shugaban kasa a Tunisia.

Alkaluman na cewa tsohon malamin shari'ar mai shekara 61, ya sami kashi 76 cikin 100 na kuri'un da aka kada, duk da cewa ba a wallafa sakamakon karshe ba.

Amma hukumar zaben kasar Tunisia ta ce wadanda suka kada kuri'a sun zarce kashi 50 cikin 100 na wadanda suka yi rijista.

Mista Saied ya kara ne da wani dan kasuwa mai kafofin watsa labarai mai suna Nabil Karoui mai shekara 56 da haihuwa.

Amma Mista Karoui na tsare a gidan kurkuku ne a yayin da ake yakin neman zabe, saboda hukumomin kasar sun kama shi da tuhumar halarta kudaden haram da kin biyan haraji.

Nabil Karoui greets his supporters after being released from Mornaguia prison near the capital Tunis on 9 October

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Abokin hamayyar zababben shugaban kasar shi ne Nabil Karoui

Ya musanta tuhumar da ake ma sa, kuma jami'an kasar sun ce yana iya daukaka kara, inda ana ganin zai ce ba a yi masa adalci a lokacin yakin neman zaben ba.

Amma magoya bayan Mista Saied sun bazama bisa titunan birnin Tunis bayan da suka sami labarin nasarar da dan takarar nasu ya samu.

Mista Saied ya gode wa magoya bayansa a wajen wani gangami da suka shirya.

Tunisian presidential candidate Kais Saied and his wife Ichraf Chebil react after exit poll results were announced in Tunis, October 13, 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kais Saied da matarsa Ichraf Chebil
line

Wane ne Kais Saied?

An lakaba wa Mista Saied sunan "the Robot", wato mutum-mutumi saboda yadda ya ke tsare a gida.

Ya gudanar da yakin neman zabensa kan yaki da cin hanci da rashawa, da dawo da martabar kasar, kuma abin mamaki shi ne bai yi wasu tallace-tallace na zo a gani ba.

Yana cikin mabobin kwamitin kwararru da ya taimaka wajen samar da sabon tsarin mulkin Tunisia na 2014, kuma ya rika bayyana a talabijin yana yin sharhi kan batutuwan siyasa.

Wani abin sha'awa shi ne ya sanar da dakatar da yakin neman zabensa saboda tsare abokin takararsa a kurkuku da hukumomin Tunisia suka yi a yayin da zaben ke saura mako guda a gudanar da shi.