Kamaru ta gayyaci 'yan wasa 29 kan karawa da Tunisia

Asalin hoton, Getty Images
Sabon kocin tawagar kwallon kafar Kamaru, Toni Conceicao ya bayyana 'yan wasa 29 da za su buga masa wasan sada zumunta da Tunisia.
Cikin wadanda aka bayyana har da sabbin 'yan wasa Ignatius Ganago da Harold Moukoudi da ake sa ran za su buga fafatawar da za a yi ranar 12 ga watan Oktoba.
Ganago, mai shekara 20, yana taka rawar gani a Nice mai buga gasar Faransa, inda ya ci kwallo a wasa bakwai da ya yi mata.
Shi kuwa Moukoudi, mai shekara 21, yana buga wa Saint-Etienne tamaula, wadda ya yi wa wasa shida a gasar Ligue 1.
Kocin ya bayyana 'yan wasa hudu da za su yi jiran kar-ta-kwana da ya hada da Paul Georges Ntep da Salli Edgar da Felix Eboa Eboa da kuma Jean Charles Castelletto.
Conceicao ya maye gurbin Clarence Seedof, wadda aka sallama, bayan da Kamaru ta kasa taka rawar gani a gasar kofin duniya da aka yi a Masar.
'Yan wasan da Kamaru ta gayyata wasan sada zumunta:
Masu tsaron raga: Andre Onana (Ajax Amsterdam, Netherlands), Fabrice Ondoa (KV Oostende, Belgium), Simon Omossola Medjo (Coton Sport, Cameroon)
Masu tsaron baya: Fai Collins (Standard Liege, Belgium), Jerome Onguene (Red Bull Salzburg, Austria), Michael Ngadeu Ngadjui (Gent, Belgium), Harold Moukoudi (Saint-Etienne, France), Allan Nyom (Getafe,Spain), Gaetan Bong (Brighton Albion, England), Ambroise Oyongo Bitolo (Montpellier, France), Joyskim Dawa Tchakonte (Mariupol, Ukraine)
Masu buga tsakiya: Andre Zambo Anguissa (Villareal, Spain), Pierre Kunde Malong (Mainz, Germany), Georges Mandjeck (Slavia Prague, Czech Republic), Jeando Fuchs (Maccabi Haifa, Israel), Arnaud Djoum (Al-Raed, Saudi Arabia), Wilfrid Kaptoum (Betis, Spain), Christian Dingome (Reims, France)
Masu wasan gaba: Ignatius Ganago (Nice, France), Stephane Bahoken (Angers, France), Eric Maxim Choupo-Moting (Paris Saint Germain, France), Christian Bassogog (Henan Jianye, China), Jean-Pierre Nsame (Young Boys, Switzerland), Karl Toko Ekambi (Villareal, Spain), Brice Moumi Ngamaleu (Young Boys, Switzerland)
Masu jiran kar-ta-kwana: Paul Georges Ntep (Kayserispor, Turkey), Edgar Salli (ACS Sepsi, Romania), Jean Charles Castelletto (Brest, France), Felix Eboa Eboa (Guingamp, France)











