An kama wasu mata da ƙwayar maganin bacci 296,000 za su kai Gombe daga Anambra

Mata masu safarar kwaya

Asalin hoton, NDLEA

Bayanan hoto, An kama su ne da ƙwayoyin Diazepam, mai sa bacci da hana jin zogi, da maganin mura na Exol-5 dubu 296

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wasu mata biyu ɗauke da ƙwayoyin magani Diazepam da Exol-5 har 296,000.

An kama matan ne a jihar Benue da ke yankin tsakiyar Najeriya suna ƙoƙarin fasa ƙaurin magungunan zuwa jihar Gombe a arewa maso gabashi daga jihar Anambra a kudu maso gabashin ƙasar.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a dazu ta bayyana sunan daya daga cikinsu da Chioma Afam wadda ta saka hijabi kuma ta sauya suna don kaucewa binciken jami'an tsaro.

Sanarwar wadda daraktan watsa labarai na hukumar Femi Baba Femi ya fitar ta ce an kama Chioma Afam wadda ta sanya hijabi kuma take amfani da suna Amina ne a Makurdi babban birnin jihar Benue tare abokiyar burminta mai suna Peace Chidinma Calleb.

An kama su ne da jumillar ƙwayoyin Diazepam, mai sa bacci da hana jin zogi, da maganin mura na Exol-5 dubu 296, lokacin da suke kan fasa ƙwabrinsu daga Anaca zuwa Gombe.

Sanarwar ta ci gaba da cewa jami'an hukumar ne suka kama motar da suke tafiya a ciki a wani wurin bincike da tantace motocin da matafiyan da ke shiga birnin na Makurdi.

Mata masu safarar kwaya

Asalin hoton, NDLEA

Bayanan hoto, An kama Chioma Afam wadda ta sanya hijabi kuma take amfani da suna Amina ne a Makurdi babban birnin jihar Benue

Yayin binciken ne aka gano Kilogram 43 na kwayar Diazepam da kuma kilo 33 na Extol 5 maƙare a cikin jakunkunan nan aka fi sani da gari-ya-yi-zafi ko Ghana Must Go.

Shugaban hukumar NDLEA Buba Marwa ya yaba wa ƙoƙarin jami'an da suka yi wannan kamen.

Amma ya ce akwai buƙatar su ƙara ƙaimi domin duk kilogram daya na ƙwaya da suka kama na nufin sun rage kilogram daya daga cikin ƙwayoyin da ake saida wa a kan tituna da kuma unguwanni.

Yankin arewacin Najeriya shi ne wurin da aka fi tu'ammali da miyagun kwayoyi a kasar a bisa alkalumman hukuma.

Amma wasu mazaunansa sun jima suna zargin cewa daga wasu yankunan kasar ake shigo musu da su.

Bayanan bidiyo, Bidoiyo: Mun kama kilo miliyan biyu na wayoyi tun fara aikina - Buba Marwa