Yadda na daina shan ƙwaya har na kafa ƙungiyar yaki da ita

Bayanan bidiyo, Bidiyonn matashin da ya daina shan kwaya har na kafa kungiyar yaki da ita

Latsa lasifikar da ke sama don kallon bidiyon:

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar Yaki da shan Kwaya da kuma safararta. Taken ranar na bana shi ne ''Ilimi mai inganci don samun kula mai kyau,'' wato "Better Knowledge for Better Care."

An kirkiri taken na bana ne don inganta fahimtar yadda matsalar kwaya take a duniya da kuma neman hadin kai kan yadda za a yi yaki da hakan don magance illolinta ga lafiya da kuma tsaro.

A kan haka ne BBC Hausa ta tattauna da wani matashi a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya wanda ya tuba daga shan kwayar ya kuma zama mai yaki da ita.