Tsananin Zafi: Mutum kusan 70 sun mutu a yanayi irinsa na farko a Canada

Asalin hoton, Reuters
Gomman mutane sun mutu a Canada a sanadin tsananin zafi da ya addabi yankin arewa maso yamma na kasar.
Ƴan sanda a British Columbia sun ce kusan mutum 70 su ka yi mutuwar fuju'a daga Litinin zuwa yau, cikinsu har da wadanda su ka manyanta.
Sun ce tsananin zafin da ke gasa yankin ya taimaka wajen yawan mace-macen.
Tsananin yanayin zafi a garin Lytton na British Columbia ya kai maki 47.9 a ma'aunin celsius ranar Litinin, daga maki 46.6 a ranar Lahadi.
Kafin makon nan, zafi a fadin Canada bai taba zarce maki 45 a ma'aunin celsius ba.
Jami'in dan sanda Kofur Mike Kalanji na Royal Canadian Mounted Police, wato RCMP, da ke aikinsa a Burnaby da ke wajen birnin Vancouver ya yi kira ga mazauna yankin:
"Ku rika duba halin da makwabtanku ke ciki, da 'yan uwanku da kuma wadanda su ka manyanta."

A Burnaby kawai, ƴan sanda sun ce an kira su zuwa gidajen da mutum 25 su ka yi mutuwar fuju'a, kuma yawancinsu sun manyanta.
A wani karamin gari mai suna Lytton, wata mata mai suna Meghan Fandrich ta sanar da jaridar Globe & Mail cewa fita waje ya kusa zama kasada.
Ma'aikatar kula da yanayi ta Canada, Environment Canada, tana gargadin jama'ar British Columbia da Alberta, da na yankunan Saskatchewan da na arewa maso yammaci da wani yanki na Yukon cewa su kiyaye.
"Canada ce kasa ta biyu cikin yankunan mafi tsananin sanyi a fadin duniya, wadda har dusar kankara mai dumbin yawa ke zuba", inji David Philips, ma'aikaci a Environment Canada.
"Mun saba fuskantar matsanancin sanyi a kai a kai, amma ba kasafai mu ke samun yanayin zafi irin wannan ba", inji shi. "A halin da mu ke ciki, Dubai ma ta fi yanayi mai sanyi-sanyi."

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ta ya ya yanayin zafin ya shafi Amurka?
Tsananin zafin ya shafi wasu biranen Amurka kamar Portland da Seattle, har ta kai ga ya zarce zafin da aka taba samu a tarihin yankunan.
A Portland da ke jihar Oregon zafin ya kai maki 46.1, na Seattle kuwa ya kai 42,2. Tsananin zafin ya kai wanda zai iya narkar da wayoyin lantarki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wani mazaunin birnin Seattle ya sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa birnin ya zama tamkar kana cikin hamada.
"Akasari mu kan sami zafin da bai zarce maki 60 ko 70 na ma'aunin fahrenheit ne - kuma za ka kowa sanye da kananan kaya - amma wannan zafin.. babu abin cewa."











