Shirin bai wa mata damar auren miji fiye da ɗaya a Afirka Ta Kudu ya jawo ce-ce-ku-ce

A wedding cake with figures of a bride and three grooms

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Pumza Fihlani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg

Wani shiri da gwamnatin Afrika ta Kudu ta fito da shi na ba mace damar auren namiji fiye da ɗaya ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Sai dai hakan bai zowa da Farfesa Collins Machoko da mamaki ba, wanda ƙwararren malami ne a wannan fanni.

Ya shaida wa BBC cewa al'ummar Afrika ba su shirya wa daidaito ba. ''Ba mu san yadda za mu riƙa tafiyar da mata ba.'' in ji shi.

Afrika ta Kudu na daga cikin ƙasashe duniya da ke amfani da kundin tsarin mulki da ya ba al'umma damar zabar abin da ransu ya ke so.

Misali tana daga cikin ƙasashen da suka yadda da auren jinsi da kuma auren mace fiye da ɗaya ga mazaje.

Musa Mseleku ɗan kasuwa ne da ke auren mata huɗu, kuma bai yadda da mace ta auri namiji fiye da ɗaya ba.

A cewarsa ''hakan zai rusa al'adar Afrika. Ya matsayin ƴa'ƴan da aka haifa zai zama? Ta yaya za su san asalinsu?''

''Wato ana so a ce mace ta zama matsayin miji kenan za ta mallaki maza biyu. To kenan macen ce za ta biya sadakin mazajen da za ta aura?''

''Sannan mazan za su rika amfani da sunanta tun da ita ta ke aurensu?'' kamar yadda Musa ya tambaya.

Auren sirri

A binciken da Farfesa Machoko ya yi a ƙasarsa ta haihuwa wato Zimbabwe mai makwabtaka kan auren namiji fiye da ɗaya ya jiyo ra'ayin duka ɓangarorin biyu.

Malamin ya tattauna da mata 20 da maza 40 da kowace mace daga 20 din ta auri guda biyu, inda suka bayyana masa cewa suna gudanar da zamansu cikin sirri la'akari da cewa al'ada ba ta yadda da shi ba.

A cewar Mr Machoko ''masu auren namiji fiye da ɗaya na yin komai ne a cikin sirri saboda tsoron al'ummar da suke zaune da su, kamar dai waɗanda ke aikata miyagun ayyuka na ƙungiyoyin asiri.''

''Kuma ma idan har wani ya tunkare su da maganar wanda ba su yadda da shi ba su kan ƙaryata cewa sun aikata hakan saboda tsoron za a tsangwame su cikin al'umma.

Mai gudanar da shirin talabijin Musa Msekelu a tsakiya zagaye da matansa huɗu wanda shima ya aminta cewa irin wannan aure ba ɗabi'ar ƴan Afrika ba ce

Asalin hoton, Musa Mseleku

Bayanan hoto, Mai gudanar da shirin talabijin Musa Msekelu a tsakiya zagaye da matansa huɗu wanda shi ma ya aminta cewa irin wannan aure ba ɗabi'ar ƴan Afrika ba ce

Ma'auratan da Farfesa Machoko ya tattauna da su ba zaune suke wuri ɗaya ba, amma sun yadda da auren kuma sun fahimci junansu.

''Akwai daga cikin matan da ta shaida min cewa ta fara sha'awar namiji fiye da ɗaya ne tun tana da shekaru 12, bayan da ta fahimci cewa sarauniyar ƙudan zuma tana auren maza da yawa, kuma abin na birge ta.

Bayan da ta balaga sai ta fara saduwa tare da duka samarinta kuma duka sun san juna.

''Hudu daga cikin mazaje tara da ta ke aure na daga cikin samarinta na farko,''in ji Mr Machoko.

A tsarin auren namiji fiye da ɗaya mata ne ke nuna sha'awar kulla auratayya ta hanyar neman mazajen don a ɗaura musu aure.

Idan mazan sun so za su iya biyan kuɗin auren, ko kuma su taimaka wa zamantakewar amma bai zama dole ba.

Kuma mace na da damar sakin ɗaya daga cikin mazajen idan har ta fahimci cewa zai kawo wa zaman cikas.

Farfesa Machoko ya ce daga hirar da ya yi da wasu mazajen sun faɗa masa cewa ƙaunar da su ke yi wa macen ya sa suka aminta ta yi musu kishiya, saboda ba su shirya su rasa ta ba gaba ɗaya.

Wasu mazan kuma sun bayyana cewa sun fahimci cewa kwata-kwata ba sa gamsar da matan na su wurin kwanciya, akan haka suka aminta da a yi musu kishiya a maimakon su rabu da matan.

Wasu kuma mazajen ba su da ƙwan haihuwa wanda hakan ya ke sa su aminta cewa matar ta ƙara auren wani namiji su zauna tare.

Kuma idan ta haihu za su riƙa ƙaryar cewa ɗansu ne don gudun a tsangwame su cewa ba su haihuwa.

A cewar Farfesa Machoko ba ya da masaniyar cewa auren namiji fiye da ɗaya na gudana a Afrika ta Kudu.

Amma a yanzu mai fafutukar ya buƙaci gwamnati ta halasta irin wannan aure saboda ba mata irin haƙkin da doka ta ba maza a kansu na auren mace fiye da ɗaya.

Charlene May
1px transparent line

Adawa daga malaman addini

Buƙatar hakan na cikin kundin da hukumomi suka kira 'Green Paper', wadda gwamnati ta fitar na buƙatar yin garambawul ga dokokin aure a karon farko tun bayan shekarar 1994.

A cewar Charlene May wata mai fafutuka daga wata ƙungiyar lauyoyi mata a Afrika ta Kudu ba za su sa ido a tauye haƙƙn mata ta ko wace hanya.

A cewarta ''ba za mu yi watsi da sauyin doka don kawai ya ƙalubalanci ra'ayoyin fifita maza a cikin al'umma ba.''

line
line

Sauyin dokar ya kuma shirya ba da ƴanci ga auratayyar Musulmi da Hindu da Yahudawa da kuma Rastafariya ba.

Sai dai duk da wani bangare na al'umma ya aminta cewa mace ta auri namiji fiye da ɗaya, batun saka shi cikin doka ya samu rashin amincewar malamai da ke cikin majalisa.

A cewar Shugaban jam'iyyar adawa ta Christian Democratic Pary Reverand Kenneth Meshoe ''yin hakan zai ruguza al'umma''.

Ya ƙara da cewa ''za a kai lokacin da ɗaya daga cikin mazajen zai zargi matar da cewa ta fi bai wa kishiyarsa lokaci, kuma hakan zai haifar da rikici tsakanin mazajen.''

A na shi ɓangaren ɗan jam'iyyar Musulmi ta Islamic Al-Jamah Party Ganief Hendricks cewa ya yi '' ku yi la'akari da idan an haifi yaro a irin wannan aure dole ne sai an yi gwajin ƙwayoyin halitta don gano mahaifinsa.''

Har wayau wasu masu adawa da shirin sun bayyana cewa ba kawai don kundin tsarin mulki na son daidaito ba zai aminta da wani abu da zai gurɓata al'umma ba.

Masu sukar mace ta auri namiji fiye da ɗaya sun kafa hujjar cewa za a samu matsalar gwaje-gwajen ƙwayoyin halitta don ba a san mahaifin ɗan da a ka haifa ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu sukar mace ta auri namiji fiye da ɗaya sun kafa hujjar cewa za a samu matsalar gwaje-gwajen ƙwayoyin halitta don ba a san mahaifin ɗan da a ka haifa ba

Amma Farfesa Machoko ya ce an taɓa gudanar da irin wannan aure a Kenya da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Najeriya, sannan yanzu haka mata na auren maza da dama a Gabon kuma doka ta aminta da haka.

''Zuwan addinin Kirista da kuma mulkin mallaka ne ya sa matsayin da mata su ke da shi ya dusashe. Ya zama cewa ba matsayi ɗaya su ke da maza ba. Kuma an yi amfani da aure wurin nuna musu bambanci,'' in ji Farfesa Machoko.

Ya ƙara da cewa ''batun mallakar ƴa'ƴan da a ka haifa a irin wannan aure mai sauƙi ne. Magaanr ita ce za su zama mallakar duka waɗanda auren ya shafa.''