Tunga Maje: Unguwar da ake yawan sace mutane a Abuja

FCT Minister

Asalin hoton, Getty Images

A baya-bayan nan unguwar Tunga Maje na daga cikin wuraren da ƴan bindiga masu satar mutane don neman kuɗin fansa ke yawan addaba a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Lamari na baya-bayan nan ya faru ne a ranar Alhamis da dare, inda wasu 'ƴan bindiga suka dirar wa wani otel a unguwar suka sace wasu baƙi da kuma mamallakin otel ɗin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai otel ɗin da wasu baƙin shida suna wata ganawa ce a ciki lokacin da ƴan bindigar suka dirar wa wurin.

Wannan ne karo na shida da ƴan bindiga suka kai hari Tunga Maje a cikin wata shida in ji wasu mazauna yankin.

Daga cikin wasu hare-haren na baya-bayan nan, ƴan bindiga sun sace mutum 12 a watan Satumban 2020 a Tunga Maje.

Sannan a watan Fabarairun 2021, masu satar mutane sun kai hari kuma cikin waɗanda suka sace har da wani jami'in hukumar shige da fice ta Najeriya.

To ko ina ne Tunga Maje, kuma me ya sa ƴan bindiga suka addabi yankin? BBC ta yi duba kan lamarin.

Wata mazuniyar garin da ba ta so a ambaci sunanta, ta shaida wa BBC Hausa cewa garin yana da ɗumbin albarka da daɗin zama ta yadda ya cika da mutane sosai daga ƙabilun Najeriya daba-daban.

"Wataƙila wannan na daga cikin dalilin da ya sa yake jan hankalin ƴan bindiga," a cewarta.

Ta ƙara da cewa: "Kin ga ko makonni da suka gabata ma ƴan bindiga sun zo sun sace wasu mata uku har da wani jariri ɗan wata uku a garin nan, kuma ba su sake su ba sai da aka biya kuɗin fansa naira miliyan huɗu ga kowane mutum ɗaya.

"Gaskiya sace-sacen mutanen da ake yi a nan yana ƙaruwa sosai, wani lokacin idan ya zo da ƙarar kwana har sai su harbi mutum a rasa rai," ta ƙara da cewa.

Wannan layi ne

Wasu labaran masu alaƙa

Wannan layi ne

Mazauna garin uku da BBC ta zanta da su sun bayyana yadda yanayin garin yake:

  • Babban gari ne da ya haɗa mutane daban-daban daga ƴan kasuwa zuwa ma'aikatan gwamnati da manoma har ma da manyan mutane ƴan siyasa
  • Mazauna garin sun fi yin kasuwanci da noma
  • Garin na kan babbar hanyar Zuba zuwa Gwagwalada ne idan aka gangara daga kan titi kaɗan
  • Akwai makarantun gwamnati da na kudi, ciki har da sakandare ta kwana, kuma kwalejin ilimi ta Zuba ma daf da garin take
  • Ma'aikatan gwamnati da ke aiki a cikin Abuja na son zama a garin saboda sauƙin gidajen haya, inda nisan tafiyar minti 10 ne zuwa 15 a mota
  • Akwai kuma sauƙin samun filayen gwamnati masu takardu
  • Akwai ƙaramin ofishin ƴan sanda a wajen amma babban ofishin nasu na Zuba
  • Tunga Maje na kusa da babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe na Abuja
  • Akwai barikin sojoji daga ɗaya tsallaken garin Tunga Maje
  • Ba shi da nisa da cikin garin Abuja, kuma akwai hanyar mota mai kyau ta zuwa gari
  • Akwai ƙabilu ƴan asalin yankin da suka haɗa da Gbayi da Kporo da Bassa da kuma Gbede
  • Sannan akwai sauran ƙabilun Najeriya da ke zama kamar Hausawa da Ibira da Igala da Ibo da Yarbawa da Nufawa da sauransu
Wannan layi ne

'Muna buƙatar tsaro'

Mutanen yankin sun shaida wa BBC cewa a yanzu ba su da wani buri da ya wuce su ga an samar musu da tsaro sosai don kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Matar da ta buƙaci a ɓoye sunanta ta ce a yanzu haka mutane sai ƙaura suke yi daga garin suna komawa unguwannin cikin Abuja irin su Kubwa, yayin da wasu kuma ke komawa Suleja ko Gwagwalada.

"Don Allah gwamnati ta agaje mu, wannan masifa da ke tunkaro mu sai an tallafa mana kafin mutanen nan su gama durƙusar da mu," in ji ta.

Sai dai rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta sha yin alwashin cewa tana ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro a birnin da kewayensa.

Wannan layi ne