Tsaro a Abuja: Sace-sacen mutane na ƙamari a babban birnin Najeriya

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Muhammadu Buhari

Rahotanni daga Abuja, babban birnin Najeriya na cewa an sake yin awon gaba da mutum huɗu a yankin Gwagwalada, ciki har da wani tsohon jami'in tsaro, sa'o'i bayan 'yan sanda sun sanar da kama wasu da ake zargi masu satar mutane ne a birnin.

Lamarin dai ya auku ne cikin ƙarshen mako inda wasu 'ƴan bindiga ɗauke da makamai suka auka ƙauyen Tungar Maje tare da sace mutum huɗu.

Ana fargabar babban birnin na Najeriya, tamkar jihohin da ke maƙwabtaka da shi, yana daɗa tsunduma cikin halin taɓarɓarewar tsaro.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC yadda wasu ƴan bindiga suka auka gidan tsohon jami'in tsaro inda ya ce ƴan bidigar "suna harbi da ƙarfi da yaji suka buɗe Islamiyya, akwai Islamiyya akwai masallaci, suka koma inda (gate) yake suka fasa suka samu shiga gidan,"

A cewarsa, ƴan bindigar sun kutsa cikin gidan makwabcin tsohon jami'in tsaron suka yi awon gaba da shi. Ya ce a halin yanzu, mutum huɗu na hannun ƴan bindigar.

Ya bayyana cewa duk da sanar da ƴn sanda halin da ake ciki, an samu tsaiko wajen isar su wajen da lamarin ya faru.

Ko a makon jiya ma, an yi awon gaba da wani ɗan jarida da wasu mutum biyu a yankin Kubwa sai dai sun shaƙi iskar ƴanci ranar Lahadi.

Ga sautin rahoton wakilin BBC Zahraddeen Lawal kan batun:

Bayanan sautiRahoton Zahraddeen Lawal