'Babu ci gaban da aka samu a yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya'

Asalin hoton, facebook
Wani jigon ɗan siyasa a arewacin Nijeriya kuma tsohon gwamnan Sokoto, Dr Dalhatu Attahiru Bafarawa ya buƙaci gwamnatin tarayya ta fifita yaƙi da 'yan fashin daji kamar yadda take yi wa annobar korona.
Dr Attahiru Bafarawa ya ce kamata ya yi gwamnati ta kafa kwamiti na musamman da zai sa-ido kan kuɗaɗen da ake kashewa kan harkar tsaro, don yi wa 'yan ƙasa bayani dalla-dalla ta yadda za a tabbatar da tsare gaskiya da kawar da duk wani zargi.
Tsohon gwamnan jihar Sokoton ya shaida wa BBC cewa yaƙin da gwamnati ke yi da ta`addanci ba zai yi nasara ba, sai an samu haɗin kan `yan ƙasa gaba ɗaya.
A cewarsa, "kamata ya yi a sa mutane waɗanda abin ya shafa, za ka ga wani mutum yana nan bai iya rubutawa bai iya karantawa amma idan aka nemi shawara ta ƙauyensu, zai ba da shawarar da za ta fi ta manjo ma."
Ga yadda hirar Attahiru Bafarawan ta kasance da Ibrahim Isa:








