Matsalar tsaro: Ƴan Najeriya sun 'ƙosa da mulkin Buhari'

BBC

Asalin hoton, BORNO STATE GOVT

Bayanan hoto, Manoman 43 da aka yiwa jana'iza bayan kisan da Boko Haram suka yi musu ranar Asabar a Kauyen Zabarmarin Borno

Ƴan Najeriya sun fara bayyana suƙewa game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ƙazanta a arewacin ƙasar yayin da ake zaman makokin manoman da aka yi wa yankan rago a jihar Borno.

Babu shakka girman matsalar tsaro na ci gaba da ƙonawa jama'a gyaɗa a tafin hannu, kuma hakan ya sa fushin jama'ar yankin arewacin ƙasar ya fara bayyana ƙarara.

Yanzu haka dai hankulan mafi yawan mutanen yankin a tashe yake, da alamu kuma an kai su bango, dangane da yadda matsalar ta tsaro ke matukar ci masu tuwo a kwarya.

Tun bayan samun labarin kisan da aka yi wa manoman hankulan suka tashi a ciki da wajen ƙasar kan matsanancin yanayin da Najeriya ke tsintar kan ta a kullum.

Har yanzu dai ana neman wasu daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su, yayin da wasu ƴan ƙasar ke ganin ko shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen magance matsalar tsaron ko kuma ya sauka daga mulki.

Kashe mutane a kauye

Akwai manoma da dama da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriyar, wanda yanzu haka kayan amfanin gonarsu na can yashe, sun kasa zuwa su girbe, ballanatana ma su kwaso su, saboda hare-haren 'yan bindiga.

Ɗaya daga cikinsu ya shaida wa BBC cewa sai ka iske ƙauye guda an kashe kowa ko kuma an sace mutane, wasu lokutan ko ka bada kuɗin fansa ba a dawo da mutane.

Ya ce: "Zancen gaskiya gwamnati ta gaza saboda shekaru biyar da ta kwashe babu wani sauƙi kullum matsalar tabarbarewa take.

Sannan akwai buƙatar shugaban ƙasa ya kawar da masu bashi gurguwar shawara, ya sauya fasali indai da gaske yake".

1px transparent line

'Buhari ya gaza'

Wani mai rajin kare haƙƙin bil'Adama, Kwamred Kabiru Dakata, yana ganin lokaci ya yi da shugaban Najeriya zai yi adalci.

Ya ce, "Adalci na farko da muke nema daga wajen shugaba Buhari shi ne ya sauka daga mulki, saboda ta tabbata gaskiya ya gaza ta fuskar tsaro, wanda dama anan ake salon ya taka kyakkyawar rawa."

Kwamared Dakata ya ce: "idan shugaban bai manta ba, ai ya taba bai wa tsohon shugaban ƙasar Jonathan shawarar sauka daga mulki lokacin da shi buhari ya zargi Jonathan da gazawa kan harkar tsaron Najeriya".

Kuma ya kamata ya sauke manyan hafsoshin tsaron ƙasar in dai da gaske ake, saboda shi kansa ya taɓa zarginsu da gazawa, in ji Ƙwamared Dakata.

To amma Hajiya Hawwa El Yakuob, wata mai fafutukar kare haƙƙin talaka, wadda aka fi sani da Maso Talakawa, ta ce matsalar ba ta mutum ɗaya ba ce domin in dai Buharin zai sauka akwai buƙatar ya tafi da duk muƙarrabansa da ya ɗora.

1px transparent line

Fadar gwamnati na ba da hakuri

Sai dai kuma yayin da jama'ar arewacin Najeriyar ke bayyana irin wannan damuwa, Malam Garba Shehu, mai Magana da yawun shugaban na ƙasar, hakuri ya ke bayarwa da jaddada cewa suna sane da komai.

Mai magana a madadin shugaba Buharin ya ce, ba za su dai na nuna baƙin ciki da damuwa ba kan halin da ake ciki da rayukan da ake rasa wa.

Ya ce sun damu kuma hankalinsu a tashe yake, kuma basu raina matsalar da ake fuskanta ba.

Sai dai yace kar a manta da irin gudunmawar da jami'an tsaro da sojoji ke bayarwa saboda ai galibin 'ƴan kasar na cikin tsaro a cewar Garba Shehu.

1px transparent line

Karin haske

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kisan da aka yi wa manoma a Borno shi ne hari mafi muni da aka yiwa farar hula a wannan shekarar a duniya.

A yanzu dai ta bayyana ƙarara, cewa jama'ar arewacin Najeriya sun gaji da yadda matsalar tsaron ta yi wa yankin ƙofar rago, da kuma yadda ake ta yin abin da galibi ake kallo a matsayin tsallen Baɗake ko dukan kura da gwado wajen magance ta.

Yayin da ake wayyo-wayyo a arewa maso gabashin Najeriyar, can a arewa maso yamma su ma hannuwa suka ɗora a ka.

Mutanen garin Ranndagi cikin yankin Birnin Gwarin jihar Kaduna, na cewa suna cikin fargaba, har ma wasu sun fara tunanin barin garin, saboda ƙaruwar hare-haren 'yan fashin daji.

Wani shaida ya faɗa wa BBC cewa ko a ƙarshen makon nan, an kashe mutum uku tare da jikkata wasu.

A wani ɓangaren kuma, gwamnatin jihar ta ce wani ɗauki ba daɗi tsakanin wasu ƙabilu mazauna kudancin Kaduna a ƙarshen makon ya yi sanadin kashe-kashe da ƙona gidaje.

Sannan rahotanni na cewa an shafe daren jiya Lahadi ana ɓarin wuta tsakanin jami'an tsaro da ƴan bindigar da suka tsaren titin Kaduna zuwa Zaria daidai jaji.

Bayanan bidiyo, Bidiyon 'yan matan da 'ke kai' harin kunar bakin wake