Boko Haram: Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutum 110 aka kashe a Zabarmari

Asalin hoton, @GovBorno
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kimanin mutum 110 aka kashe a harin da ake tunanin ƴan Boko Haram ne suka kai wa manoma kusa da garin Maiduguri a ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa, mai kula da ayyukan jin-ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniyar Edward Kallon ya ce manoma ne aka kashe a harin da ya kira mummunan tashin hankali.
Sai dai sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar bayan jana'izar mutanen da aka kashe ta ce mutum 43 aka kashe a harin.
Bayan kisan, gwamnan jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya yi kira ga matasa su shiga aikin ƴan banga ko sa-kai domin yaƙi da ta'addanci.
Babagana Zulum ya yi wannan kiran ne yayin ziyarar jaje a yankin Zabarmari da aka kai harin.
Zulum ya jagoranci jana'izar manoman da aka kashe
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno shi ya jagoranci jana'izar mutanen da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Zabarmari da ke Ƙaramar Hukumar Mafa a jihar.
Zulum ya je garin ne da safiyar Lahadi, inda mazauna yankin suka faɗa masa cewa har yanzu ba a gama tantance yawan waɗanda aka kashe ba da kuma waɗanda suka ɓata, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin jihar.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce akwai mata guda 10 da ba a san inda suke ba, waɗanda ke aiki a wata gonar shinkafa da ke garin na Koshebe.
Mutum 16 daga cikin waɗanda aka kashe 'yan gudun hijira ne, in ji Amnesty.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da kisan a cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar.
Ranar da lamarin ya faru
A ranar Asabar ne aka samu rahotannin da ke cewa wasu da ake tunanin mayaƙan Boko Haram ne sun shiga gonaki kuma suka kashe fiye da mutum 40.
Lamarin ya faru ne a yankin Koshebe na Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mafa ta Borno, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar wa da BBC.
Sun ce maharan sun abka wa manoman ne yayin da suke girbin shinkafa. Kuma bayanai sun ce an ɗaure manoman ne sannan aka yi masu yankan rago.
Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa sai da aka tara mutanen wuri guda sannan aka rinƙa yanka su har mutum 43.
"Bayan sun yanka mutanen akwai mutum 13 da suka aiko domin su sanar da abin da aka aikata, bayan kisan sun yi kone-kone da sunan wai mazauna ƙauyen na manafurtar su.
Wanda abin ya shafa har da baƙi da ke zuwa daga wasu jihohi domin su gudanar da ayyukansu a ƙauye."
Mutumin ya ce: "Akwai wasu mutane da kuma ba a gani ba bayan harin, har da wadanda suka shiga garin daga Zamfara da Kebbi da Sokoto,"
Ana dai cikin yanayi na juyayi da makoki sakamakon ƙazamin kisan da ɓarnatar da dukiyoyi da aka yi".
Neman ɗauki

Injiniya Satomi Ahmed da ke wakiltar mazabar Jere a jihar ta Borno, ya shaida wa BBC cewa akwai mutum 66 da ba a gani ba, sannan gawawwaki 43 aka kai musu.
Ya ce an shafe wata 5 zuwa 6 ba a ga irin wannan hari ba, saboda tsaron da ake samu na sojoji.
Injiniya Satomi ya bayyana takaicinsa tare da koken a kawo masu ɗauki saboda mummunan yanayin da garin ya shiga.
Babu dai wata ƙungiyar da ta fito ta ɗau alhaƙin harin, ammam kowa yasan cewa mayakan Boko Haram ne ke aikata irin wannan migayun kisan a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Ko a watan daya gabata sai da mayaƙan Boko Haram din suka kashe manoma 22 a wannan jihar.

Me gwamnati ke cewa?
Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa da wannan hari inda da ya ce akwai rashin tunani a ciki.
Wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a madadin shugaban na cewa, Buhari ya yi alla-wadai da harin, sannan ya bukaci a ɗau duk matakan da suka dace domin ci gaba da kare ƙasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Mayaƙan Boko Haram da mayaƙan ISWAP, na ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya duk da iƙirarin hukumomi da jami'an tsaro na karya lagonsu.

Abin da ƴan Najeriya ke cewa
'Ƴan Najeriya dai na ci gaba da bayyana takacinsu kan taɓarɓarewar tsaro da yadda ƴan ƙasa ke cikin fargaba da rashin sanin makomarsu duba da yanayin da tsaron ke ciki.
Mutane da dama a shafukan sada zumunta kamar Twitter na alla-wadai da kamun ludayin gwamnati kan yadda ake ci gaba da samun kisan gilla a ƙasar.
Akwai kuma wanda ke bayyana ƙarara cewa akwai gazawar manyan hafsoshin tsaro.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
@Famous_Anfield ya ce: " Zancen gaskiya manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun gaza kuma ya kamata a sauya su. Ba tare da fargaba ko cigaba da basu dama ba, idan suka cigaba da riƙe tsaron kasar nan mutanen na cigaba da mutuwa, to babu batun yaki da matsalar tsaro. A kore su domin kare arewa #SecureNorth #ZabarmariMassacre
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
@aminuyaro_ ya ce: Gwamnatin Buhari ta gaza musamman a fannin tsaro da tattalin arziki. An yiwa manoma 43 yankan rago a Borno yau. Yaushe wadannan kashe-kashe za su kawo karshe? Idan ba za ka iya kare rayukan ƴan kasa ba ka yi murabus. Mun gaji #ZabarmariMassacre
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4