Abubakar Shekau: Sojojin Najeriya na shan caccaka kan shugaban Boko Haram

Gwamna Zulum da Janar Buratai

Asalin hoton, @govborno

Lokacin karatu: Minti 3

Masu amfani da shafin Twitter a Najeriya sun karya kumallonsu na yau da rundunar sojojin Najeriya bayan da ta ce tana neman shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

A ranar Laraba ne rundunar sojin Najeriya ta sake gabatar da jerin sunayen mutum 86 da take zargi ƴan Boko Haram ne da take nema ruwa a jallo.

Daga cikinsu akwai shugaban Boko Haram Abubakar Shekau da kuma Al Barnawi shugaban ɓangaren da suka ɓalle daga Boko Haram.

Babban hafsan sojin kasa Janar Tukur Buratai ne ya gabatar da sunayen tare da gwamnan Borno Babagana Zulum, a wajen bikin ƙaddamar da gwama ƴan sa-kai da ƴan banga cikin rundunonin soji da ke faɗa da Boko Haram wanda aka gudanar a wani sansanin soji da ke ƙaramar hukumar Konduga.

An ruwaito Janar Burutai na cewa bikin na ƙaddamar da farmakin ƙarshe ne na kawo ƙarshen ayyukan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Me ya jawo wa rundunar sojin suka?

Sai dai shafin Twitter a kasar ya wayi gari da maudu'ai irin su Shekau da Nigeria Army da Boko, wadanda ke magana a kan wadannan batutuwa.

Galibin masu amfani da shafin sun soki rundunar sojin Najeriya ne saboda neman da suke yi wa Shekau ruwa a jallo suna masu cewa ta dade tana karyar sun kashe shugaban na Boko Haram.

A cewarsu, ba su ga dalilin da zai sa a rika neman mutumin da aka yi ikirarin kashewa har sau uku ba sai dai idan da ma tun da farko yaudarar mutane rundunar ta rika yi.

Wale Adetona ya yi mamaki da jin labarin neman Shekau yana mai cewa "Ku tsaya. Na yi tsammanin an kashe Shekau."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi kuwa Erons Johnson ya zargi rundunar sojin ta Najeriya da watsa labaran karya ind ya kara da cewa: "Yanzu an tabbatar rundunar sojin Najeriya tana watsa labaran karya da wadanda ke da zummar yaudarar mutane. Sau da dama suna cewa an kashe Shekau, yanzu kuma sun ce yana cikin wadanda ake nema ruwa a jallo. Mene ne labarin karya. Wannan ko kuma wanda aka ce an kashe shi?"

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wasu ma abin dariya suka mayar da lamarin inda Nwafresh ta ce "duk da yawan dauke wutar lantarkin da ake yi a kasar nan, na rantse Shekau ya mutu fiye da yadda batirin wayata ke mutuwa."

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Waiwaye kan 'mutuwar' Shekau

Sau hudu rundunar sojin Najeriya tana cewa ta kashe shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ko da yake yakan fito ya karyata hakan.

Daya daga cikin lokutan da rundunar ta yi ikirarin kashe Shekau shi ne ranar 19 ga watan Agustan 2013 inda Rundunar hadin gwiwa ta JTF ta ce Abubakar Shekau ya mutu sakamakon raunukan da ya samu.

A wata sanarwar da ta aika wa manema labarai da sa hannun Laftanar Kanal Sagir Musa ta ce, akwai yiwuwar raunin harbin bindiga ne ya yi ajalin Shekau.

JTF ta ce an raunata Shekau ne a wani artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar ta Boko Haram a dajin Sambisa a ranar 30 ga watan Yuli.

Sanarwar ta kara da cewa an shigar da Shekau wani kauye, Amitchide a Kamaru domin a yi jinyarsa, amma ya mutu tsakanin ranar 25 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta.

A ranar 13 ga watan Agusta ne Abubakar Shekau ya fito a wani bidiyo, inda ya ce kungiyar ce ke da alhakin kai wasu hare-hare da suka hada da na Malam Fatori da Bama da Kuma Baga.

Haka kuma Shekau ya musanta batun kisan shi a wannan bidiyon.

Sauran lokutan da aka ce an kashe Shekau:

Watan Yulin 2009

Watan Satumbar 2014

Watan Agustan 2015