Boko Haram: Shekau ya shiga 'tsaka mai wuya'

Asalin hoton, Getty Images
Bisa dukkan alamu kungiyar Boko Haram bangaren Abubakar Shekau na cikin wani irin yanayi mai wuya bisa la'akari da wani sauti da aka wallafa a shafukan zumunta da ke bayyana irin damuwar da kungiyar take ciki.
A sautin, an ji murar Abubakar Shekau yana 'kuka' yana neman Allah ya kare shi daga sojin Najeriya.
BBC ta tuntubi wani masani kan harkokin ta'addanci a Afrika, Audu Bulama Bukarti kan ingancin wannan sautin, inda ya ce hakika wannan muryar shugaban Boko Haram ce Abubakar Shekau, kuma alamu na nuna cewa 'ruwa ya soma kare wa dan kada.'
A cikin sautin wanda ya yi shi a harshen Kanuri, Shekau din ya ce suna cikin mawuyacin hali a cikin wannan watan na Ramadana.
A cewar Audu Bulama Bukarki, bisa dukkan alamu sautin na daga cikin wani bangare na hudubar Abubakar Shekau a ranar Juma'a.
"Wannan ne karon farko a tarihi muka ji Abubakar Shekau yana kuka, a da shi mutum ne mai izgilanci da dariyar keta ga wadanda ya cutar", in ji Bukarti.
Ya kara da cewa "Hakan nuna cewa kungiyar na cikin matsin lamba da kuma damuwa na abin da ke faruwa a yanzu, ina zaton abin da ke faruwa shi ne sabon matakin da rundunar sojin Najeriya ta dauka na kaiwa wannan kungiyar ta shi da kuma daya bangaren hari babu kakkautawa".
'Buratai ya koma Borno'
A cikin 'yan makonnin nan rahotanni sun nuna cewa babban hafsan dakarun Najeriya, Lafnar Janar Tukur Buratai ya tare a jihar Borno domin ganin ya kawo karshen kungiyar Boko Haram.

Asalin hoton, Twitter/@HQNigerianArmy
Rundunar sojin Najeriya a 'yan kwanakin nan kuma ta wallafa bidiyo da hotuna na nasarorin da take ikirarin ta samu a kan kungiyar Boko Haram.
"Dama sojoji suna da'awar suna samun nasarori har ma suna nuna hotuna na nasarorin da suka samu, sannan kuma ita kungiyar Boko Haram a kwanakin nan ta fitar da hotunan wasu mayakanta da ta ce sun yi shahada", in ji Bukarti.
Kawo yanzu hukumomin sojin Najeriya ba su mayar da martani ba a kan wannan sautin muryar Abubakar Shekau.
An shafe fiye da shekaru 10 hukumomi a Najeriya suna yaki da kungiyar Boko Haram - wacce ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da lalata dukiya ta miliyoyin naira.
Rikicin na Boko Haram wanda aka soma a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya fantsama zuwa bakwabtan kasashe kamar su Nijar, Chadi da kuma Kamaru.











