Yadda ɓarayi da 'yan Boko Haram suka raba hankalin sojojin Najeriya

Asalin hoton, @HQNIGERIANARMY - TWITTER
- Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
Najeriya ta shafe shekaru tana fama da matsalar tsaro a sassan ƙasar tun da daga rikicin Boko Haram a arewa maso gabashi da kuma ƴan fashin daji masu satar mutane da shanu a arewa maso yammaci.
Tun kafin hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ɗaya daga cikin manyan alƙawura uku da ya yi shi ne na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa musamman a arewa maso gabashin ƙasar.
Jim kaɗan bayan hawan shi kan kargar mulki, an ɗan samu sassauci a jihohin arewa maso gabas inda rundunar sojin ƙasar ta ƙwato wuraren da 'yan Boko Haram ke da iko da su.
Har ma ta kai ga wani lokaci da sojojin suka yi iƙirarin cewa sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Dajin Sambisa - Ɗaya daga cikin manyan maɓoyar 'yan Boko Haram a Najeriya.
Amma da tafiya ta yi tafiya, sai hannun agogo ya fara komawa baya dangane da tsaro, inda 'yan ƙungiyar suka fara kai harin sari ka noƙe, tare da kai hare-hare a gefen tituna da dai sauransu.
Hankalin sojojin Najeriya ya rabu
Yayin da sojojin sama da na ƙasa da wasu dakarun haɗin gwiwa ke ƙoƙarin ƙarasa fatattakar ɓurɓushin 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, sai aka fara samun matsalar tsaro a jihar Zamfara inda aka yi ta ba-ta-kashi tsakanin ƴan bindiga da jami'an tsaro.
Ga kuma rikicin ƙabilanci da na makiyaya da manoma a jihar Benue inda hankalin sojoji ya sake karkata a can.
Ba a gama wannan rikici na Zamafara da Benue ba matsalar garkuwa da mutane a arewa maso yammacin ƙasar ta ƙara ƙamari inda masu garkuwa da mutane suka ci gaba da cin karensu babu babbaka a hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar Birnin Gwari a Kaduna da Kudancin Kaduna da dai sauran wurare na arewa maso yammacin ƙasar.
Ana cikin haka kuma sai jihar Katsina ta ɗauka inda can ma 'yan bindiga da ɓarayin shanu suka addabi sassan jihar wanda yanzu haka ana ci gaba da samun irin wannan matsala a jihar nan da can.
Ta irin waɗannan rikice-rikicen ne ya sa aka raba hankalin sojojin ƙasar musamman na sama da na ƙasa inda ake ta kafa rundunonin haɗin gwiwa da ke aiki a dazuka daban-daban na ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Arewa Maso Gabas
A arewa maso gabashin Najeriya, akwai Rundunonin Operation Lafiya Dole da kuma Operation Hail Storm waɗanda suke yaƙi musamman da 'yan ƙungiyar Boko Haram da kuma na ISWAP.
Operation Lafiya Dole runduna ce ta sojin ƙasa da ke faɗa da Boko Haram inda kuma take samun taimako daga rundunar Operation Hail Storm da ke kai hare-hare ta sama.
Arewa Maso Yamma
A arewa maso yammacin Najeriya, akwai Rundunonin Operation Hadarin Daji da kuma Operation Sahel Sanity waɗanda suka mayar da hankali musamman wurin yaƙi da 'yan bindiga daɗi da masu garkuwa da mutane da kuma ɓarayin shanu.
Arewa Ta Tsakiya
A arewa ta tsakiya, akwai rundunonin Operation Safe Haven da kuma Operation Thunder Strike da Operation Whirl Stroke da ke ƙoƙarin fatattakar 'yan bindiga da ɓarayi a yankin.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shin kwaliyya tana biyan kuɗin sabulu?
Watanni kaɗan bayan da Shugaba Buhari ya hau kan karagar mulki a 2015, mutanen ƙasar musamman na arewa maso gabashi suka fara shewa da nuna jin daɗinsu sakamakon ganin alamun kwaliyya ta fara biyan kuɗin sabulu, ganin cewa an ɗauki tsawon lokaci babu tashin bama-bamai, da kuma shingaye kan hanya da aka cire.
An kuma daina samun tashin bama-bamai a jihohin Kaduna da Kano da Filato da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar.
Wannan dalili ne ya sa wasu 'yan ƙasar ke ganin kamar shugaban ya kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.
Amma shekaru kaɗan bayan hakan, wasu 'yan ƙasar da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka fara kiran gwara jiya da yau, sakamakon yadda matsalar tsaron ke ƙara ƙamari a faɗin ƙasar.
A kwanakin baya, ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayar da rahoton cewa an kashe kimanin mutum 1,126 a jihohin arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.
A kwanakin baya ma sai da wani uban ƙasa a jihar Katsina ya shaida wa BBC cewa 'yan bindiga sun mayar da mata 600 zawarawa a yankin Batsari da kuma mayar da yara sama da 2,000 marayu.
Wasu na ganin irin yawan rundunonin da aka kafa a arewacin ƙasar, ya kamata a ce an kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.
Ita ma ƙungiyar Human Rights Watch a 2018 ta fitar da wani rahoto kan cewa akalla mutum 1,200 aka kashe a arewa maso gabashin Najeriya tare da raba kusan mutum 200,000 da muhallansu a 2018 kaɗai.
Jaridar Vanguard a Najeriya a 2018 ta ruwaito cewa sama da mutum 3,000 aka kashe a jihar Zamfara tun daga 2011 tare da garkuwa da sama da mutum 500.
Itama ƙungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin Najeriya cikin shekaru 10, kamar yadda ta fitar a wani rahotonta a watan Mayun bana.











