Babagana Umara Zulum: Yadda mayaƙan IS suka kai wa tawagar gwamnan Borno hari

Bayanan bidiyo, Babagana Zulum ya yi kira ga sojoji su zage damtse

Wasu mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyar IS sun kashe jami'an tsaro goma sha biyar a wani kwanton bauna da suka yi wa tawagar gwamnan jihar Borno.

Daga cikin wadanda suka rasa ransu a wannan hari akwai 'yan sanda takwas da sojoji uku da kuma 'yan kungiyar 'yan sintiri da ke tallafawa dakarun gwamnati wato Civilian JTF hudu.

Gwamnan jihar ta Borno, Babagana Umara Zulum, da tawagarsa na kan hanyarsu ne ta zuwa garin Baga a lokacin da aka kai musu harin.

Wani dan banga da ya nemi a sakaye sunansa ya shaidawa BBC cewa ya ga gawar mutum 14 a asibitin da ke garin Monguno.

Akwai dai mutanen da suka samu raunuka daga cikin tawagar gwamnan yayin da kuma maharan suka kwace ababen hawa da dama.

Wannan lamari dai ya faru ne a yayin da jami'an gwamnatin ta Borno ke ziyara a yankin da abin ya faru domin kammala shirye-shiryen mayar da 'yan ainihin garin na Baga matsugunnansu bayan sun shafe shekara da shekaru ba sa garin saboda rikicin Boko Haram.

Wannan layi ne

Ba wannan ne farau ba

Boko Haram

Ba wannan ne karon farko da aka taba kai wa tawagar gwamna Zulum hari ba - ko a kwanakin baya ma an kai masa makamancin wannan hari, abin da ya sa har gwamnan ya ce ana yi wa bangaren tsaro zagon kasa.

Gwamna Zulum ya shaida wa BBC cewa: "Akwai buƙatar Shugaba Muhammadu Buhari ya san cewa zagon ƙasa ake yi wa kokarin gwamnati na wanzar da zaman lafiya a yankin da ya shafe sama da shekara goma yana fama da ta'addancin."

Harin na wannan lokaci da aka kai wa ayarin gwamnan ya sanya shakku a zukatan mutane a kan makomar 'yan gudun hijrar da ake son mayar da su garuruwansu na asali.

An dai shafe shekara fiye da 10 ana fama da hare-haren Boko Haram, kuma matsalar har ta kai ga yin naso zuwa wasu kasashe da ke makotaka da Najeriya kamar Kamaru da Chadi.

Rikicin na Boko Haram a yammacin Afirka, ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da dubu talatin tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu musammamma a kasashen yankin tafkin Chadi.

Wannan layi ne